Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda attajirai ke shirya wa zuwan ranar tashin duniya, me ya kamata sauran al’umma su yi?
- Marubuci, Zoe Kleinman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editar Fasaha
- Lokacin karatu: Minti 7
An ce Mark Zuckerberg ya fara aikin gina wani katafaren gidan gonarsa - Koolau Ranch, a fili mai fadin eka 1,400 a tsibirin Kauai da ke Hawaii tun a shekarar 2014.
Bayanai sun nuna cewa gida ne da aka tanadar wa hanyar samar da wutar lantarki ta kansa da kuma dimbin kayan abinci da aka tanada domin yanayi na kar-ta-kwana.
Kodayake an hana masu aikin gina gidan yin magana a kan aikin bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya, kamar yadda mujallar Wired ta rubuta.
Haka kuma an gina katanga mai tsawon kafa shida da za ta hana ganin cikin gidan daga wani titi da ke kusa da wajen.
Da aka tambayi Zuckerberg a shekarar da ta wuce ko yana gina wata maboya ce ta karkashin kasa saboda wani bala'i da zai iya zuwa duniya a nan gaba sai ya ce ''a'a''.
Ya kara bayani da cewa gidan na karkashin kasa mai fadin murabba'in kafa 5,000, kamar wani dan karamin daki ne na karkashin kasa kawai.
Duk wadannan kalaman nasa ba su sa an daina rade-radi ba - wanda bugu da kari ya sayi wasu gidaje 11 a unguwar Crescent Park ta garin Palo Alto a jihar California, inda kuma ake ganin ya kara wani gini na karkashin kasa a wajen mai fadin murabba'in kafa 7,000.
Duk da cewa takardun izinin ginin nasa sun nuna cewa za a yi dakuna na karkashin kasa , kamar yadda jaridar New York Times, ta nuna wasu daga cikin makwabtansa sun ce maboya ce ta karkashin kasa.
Akwai kuma jita-jitar da ake ta yadawa cewa wasu manyan attajiran na duniya kamar shi Zuckerberg da suka mallaki kamfanonin fasaha su ma suna ta sayen filaye da za su iya mayar da su maboya ta kasaita ta karkashin kasa, wadda za a kashe dimbin kudi a aikin.
Attajirin da yana daga cikin wadanda suka mallaki shafin LinkedIn, Reid Hoffman, ya yi magana a kan abin da ya kira inshorar kariya daga bala'in tashin duniya, inda ya yi magana kan gina irin wannan maboya ta karkashin kasa a New Zealand.
To a nan za mu iya cewa watakila wadannan hamshakan attajirai masu kamfanonin fasaha, na shirya wa wani yaki ne, ko illolin sauyin yanayi ko kuma wani babban bala'i da suke hangen zai faru wanda mu ba mu sani ba zuwa yanzu?
A 'yan shekarun da suka gabata bunkasar da ake samu ta kirkirarriyar basira wato AI ta zama kari a kan jerin irin bala'o'in da ake fargabar za su iya afka wa duniya - su kawo karshenta.
Masana kimiyya da fasaha da dama na fargaba kan irin cigaba na gaggawa da ake samu a wannan fasaha ta AI.
Ilya Sutskever, babban masanin kimiyya wanda kuma na daga cikin wadanda suka mallaki kamfanin Open AI, an ce yana daya daga cikinsu.
Zuwa tsakiyar shekarar 2023, kamfanin mai cibiya a San Francisco ya samar da ChatGPT - inda a yanzu daruruwan miliyan mutane a duniya suke amfani da manhajarsa (chatbot), wadda ke iya kwaikwayon mutum ta murya ko ta sakon rubutu, kuma sun dage sosai wajen inganta manhajar.
To amma zuwa bazarar shekarar ta 2023, Mr Sutskever ya yi amanna cewa kwararrun masana kwamfuta na dab da samar da abin da suka kira ''AGI'' wato ''Kirkirariyar Basira ta Komai-da-Ruwanka''
Ita wannan fasaha ta AGI, na nufin matakin da na'ura ko kuma kwamfuta ta samu basirar da ta kai daidai da ta dan'Adam kamar yadda aka bayyana a littafin 'yarjarida Karen Hao.
A wani taro da suka yi, Mista Sutskever ya bai wa abokanan harkar tasu ta fasaha shawarar, gina wata maboya ta karkashin kasa, ta manyan masana kimiyyarsu kafin a saki wannan fasaha ta gagara-badau ko kuma komai da ruwanka a duniya in ji Ms Hao.
"Lalle kam za mu gina maboya ta karkashin kasa kafin mu saki AGI [Kirkirariyar Basira ta Komai-da-Ruwanka]'', kamar yadda aka yi ta bayar da rahoton cewa ya fada, kodayake ba a san takamaimai me yake nufi da ''mu'' ba.
Wannan ya kara bayar da haske kan yadda manyan kwararrun masana kimiyya da manyan masu kamfanonin fasaha na duniya ke aiki tukuru wajen kirkiro babbar Kirkirarriyar Basira, inda kuma ta daya bangaren suke nuna damuwa sosai kan abin da wannan fasaha za ta iya yi wata rana.
To a takaice da yaushe ne takamaimai idan har za a kirkiro wannan fasaha ta AGI, za ta zo? Kuma akwai wani abu da za ta iya yi da za ta sa mutane karabiti tsoro?
Fasahar za ta zo da wuri
Manyan masu kamfanonin fasaha sun yi ikirarin cewa ba makawa wannan fasaha ta AGI (Kirkirariyar Basira ta Komai-da-Ruwanka) za ta zo.
Shugaban kamfanin OpenAI Sam Altman, ya fada a watan Disamba na 2024 cewa za ta zo da wuri fiye da a lokacin da yawancin mutane a duniya ke tunani.
Sir Demis Hassabis, daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin DeepMind, ya yi hasashen cewa za ta zo cikin shekara biyar zuwa goma mai zuwa, yayin da, a shekarar da ta gabata, mai kamfanin Anthropic, Dario Amodei ya rubuta cewa, za ta iya bayyana a farkon 2026.
wasu daga cikin wadannan masu kamfanonin na fasaha kuwa, sun ki bayyana matsayarsu, inda suke sauya magana kusan a kodayaushe, in ji Dame Wendy Hall, farfesa a fannin kimiyyar kwamfuta a Jami'ar Southampton.
Sai dai malamar jami'ar ta ce, ''masana kimiyya sun ce KirKirarriyar Basira na da ban mamaki'' amma kuma ta ce, '' duk da haka ba ta yadda za ka iya kwatanta ta da basirar dan'Adam.''
A baya-bayan nan littafin Genesis, wanda Eric Schmidt, da Craig Mundy da kuma marigayi Henry Kissinger, suka rubuta a 2024, ya yi bayani kan yuwuwar samun fasahar da za ta zama sha-kundum wajen fitar da matsaya ko yanke hukunci da shugabanci, wadda kuma za mu mika mata komai na gudanarwa gaba daya.
Magana ce ta yaushe za ta bayyana, amma ba maganar, sharadin samuwarta ba, in ji marubutan.
Kowa zai samu kuɗi ba tare da ya yi aiki ba?
Wadanda ke goyon bayan samar da fasahar ta AGI da ta ASI, suna ganin tana da tattare da alfanu da dama.
za ta gano sababbin hanyoyin magance miyagun cutuka, da magance matsalar sauyin yanayi da kirkiro hanyoyin da ba za su kare ba na samun makamashi maras gurbata muhalli a cewarsu.
Elon Musk ya ma ce fasahar za ta iya samar da hanyoyin samun kudade masu yawa a duniya.
Sannan ya ce fasahar za ta yi araha ta yadda kusan kowa zai so ya mallake ta.
''Kowa zai samu hanyoyi mafiya inganci na kula da lafiya, da abinci, da sufuri na gida, da kusan komai. Kowa zai yalwatu,'' in ji shi.
Sai dai kuma akwai fargaba a tattare da fasahar. Ina ga idan ta fada hannun 'yan ta'adda, suna amfani da ita a matsayin makami, ko kuma idan ita fasahar ta ga cewa ai dan'Adam shi ne sanadin matsalolin duniya kuma ta yanke shawarar hallaka mu?
Da yake magana da BBC mutumin da ya kirkiro World Wide Web Tim Berners Lee, ya yi gargadin cewa: "Idan har ta fi ka basira, to dole ne mu, iya taka mata birki.''
"Dole ya kasance za mu iya dakatar da ita gaba daya."
Gwamnatoci na daukar matakan kariya a kan wannan fasaha.
A Amurka inda yawancin kamfanonin wannan fasaha ta kirkirarriyar basira suke , Shugaba Biden ya yi doka a 2023, wadda ta bukaci kamfanoni su nuna wa gwamnati irin matakan da suke dauka na kare lafiya da sakamakon da suka samu na gwajin matakan.
To amma kuma tuni Shugaba Trump ya soke wannan doka, da cewa ta zama tarnaki ga kirkira.
A Birtaniya, shekara biyu da ta gabata aka kafa hukumar tabbatar da kare matsaloli ko haduran da za a iya samu daga fasahar.
Anya barazanar ba soki-burutsu ba ce?
farfesa a bangaren koyar da ilimin amfani da na'ura a Jami'ra Cambridge, Neil Lawrence, shi yana ganin duk wannan surut ne kawai na shirme da ko soki-burutsu kawai ake yi a kan fasahar.
Ya ce, ''maganar fasahar AGI -[Kirkirarriyar Basira ta Komai-da-Ruwanka], shirme ne kawai kamar maganar fasahar AGV [Kirkirarriyar-Basirar Komai-da-Ruwanka].''
Ya ce yana amfani da jirgin sama (Airbus A350) idan zai je Kenya, sannan ya yi amfani da mota idan zai je jami'a, kuma ya taka da kafa idan zai je gidan cin abinci, saboda haka babu mota ko abin hawa da shi kadai zai iya yin wadannan.
Saboda haka shi a wajensa maganar fasahar AGI, shirme ne kawai, abu ne da kawar da hankali.
Masanin ya ce,'' mun bari maganar AGI ta dauke mana hankali, har muna mantawa da hanyoyin da ya muke bukata na inganta rayuwar mutane.''