Yadda mai ciki ta haihu a hannun ƴanbindiga a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar garin Nahuce da ke jihar Zamfara na cikin alhini bayan wasu gungun ƴan bindiga sun sace mata sama da 20 da ƙananan yara da suke goyo da kuma wasu maza huɗu.
Wani abu da ya fi tayar wa al'ummar hankali shi ne yadda ɗaya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hanyar tafiya da su daji, amma duk da haka maimakon ɓarayin su bari ta koma, ai suka tafi da ita.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan samun sauƙin matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya, inda wasu ke ganin an samu sauƙi, wasu kuma suke ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin da suke daɗe suna fama da matsalar garkuwa da mutane da fashin daji da kashe-kashe, lamarin da ya yi ajalin mutane da dama.
Sai dai hukumomi a ƙasar suna bayyana cewa an fara samun sauƙi, inda suke bayyana irin nasarorin da suka samu wajen yaƙi da rashin tsaro a arewaci da ma ƙasar baki ɗaya.
Satar Nahuche
A daidai lokacin da mutanen jihar Zamfara suka fara ƙirga irin sauƙin da ake samu wajen yaƙi da matsalar tsaro, mutanen garin Nahuche da ke ƙaramar hukumar Bunguɗu ta jihar Zamfara, cewa suka yi wankin hula na neman kai wa dare.
Wannan na zuwa ne bayan satar mutane da aka yi a garin nasu bayan ɗan sauƙin da suka samu, lamarin da suka bayyana da rashin tausayi kasancewar ɓarayin sun tafi da mai ciki, ta haihu a hanya, amma suka tafi da ita.
Wani mazaunin garin ya bayyana wa BBC cewa, "mun shiga cikin tashin hankali na yadda ɓarayin daji suka shigo mana cikin dare, inda suka tafi da mutane ciki har da masu goyo."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ɗaya daga cikin waɗanda suka sace ta haihu a hanya.
"Amma saboda rashin tausayi sai suka tafi da ita daji maimakon su bari ta koma gida," in ji mazaunin gari.
Ya ce sun tafi da mata sama da 20, sai kuma maza huɗu, "amma a cikin matan akwai masu goyo, don haka ba mu ƙirga da goyon ba saboda ba mu san adadinsu ba. Kuma maharan sun kutsa ne cikin dare da misalin ƙarfe ɗaya ba tare kowa ya sani ba, har sai da suka kwashe mutanen."
"Amma daga baya wata mata ta dawo saboda ba ta da lafiya sosai, saboda haka ba su iya tafiya da ita daji ba."
Mazaunin garin sun ce sai bayan sun fita ne kafin suka fara buɗe wuta, wanda ya ankarar da mutane.
Ya ce daga baya sojoji sun kai musu ɗauki, "amma sai daga baya bayan ƴanbindigar sun tafi."
Ya ƙara da cewa sun fara canja salo, domin a cewarsa, "yanzu ba sa zuwa da babura, suna shigowa ne, sai sun kwashe mutane sun fita, kafin sai su hau babura su tafi da su."
Shi ma wani mazaunnin garin ya ƙara da cewa an san dabar ƴanbindiga da suke addabar yankin, inda ya ce ya kamata a fatattake su.
"Akwai wata daba ta Ɗansadiya, wadda ita ce dabar da take addabar mutanen yankinmu a yanzu."
Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ta ce tana ci gaba da tattara bayanai, kuma da zarar ta kammala haɗa komai, za ta fitar da bayanai a hukumance.










