Abin da ake nufi da ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda da gwamnati ta yi

Asalin hoton, OTHER
A ƙarshe dai gwamnatin Najeriya ta fito ta ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda makonni bayan wata kotu a ƙasar ta ayyana su.
A wata hira da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da gidan talabijin na Channels, ya bayyana cewa ayyana yan fashin daji da ke addabar yankin arewa maso yamma a matsayin ƴan ta'adda ne kaɗai abin da yan ta'addan za su fahimta.
Jim kaɗan bayan tattaunawar da aka yi da shugaban, ma'aikatar shari'a ta Najeriyar ta fitar da wani daftari na ayyana su a matsayin ƴan ta'addan.
Ko a kwanakin baya da a karon farko kotu ta ayyana su a matsayin ƴan ta'adda, sai da ministan shari'a na Najeriyar Abubakar Malami ya bayyana cewa an tuntuɓi duk masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro kafin ɗaukar matakin, za kuma a hukunta 'yan bindigar ƙarkashin dokokin shari'a na kasar.
Dangane da batun ayyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta'adda, mun tuntuɓi wasu masu sharhi kan alamuran tsaro domin samun ƙarin haske kan bayanan shugaban ƙasar.

Me ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda yake nufi?
Dangane da hakan, BBC ta tuntuɓi Group Captain Saddik Shehu mai ritaya inda ya ce gwamnatin Najeriya ta bi dukan matakan da ya kamata ta bi wajen ayyana su a matsayin ƴan ta'adda.
"A dokar Najeriya ayyana su a matsayin ƴan ta'adda, hakan na nufin sojan Najeriya ko ɗan sandan Najeriya ko wani jami'in tsaro da ya gansu ko ya tababbatar su ne a wuri, ba ma sai sun kawo hari ba, zai iya far musu.
"Ko barci suke yi za a far musu, ko noma suke yi za a far musu matuƙar an tabbatar da cewa su yan ta'adda ne," in ji Group Captain Saddik.
A cewarsa, a baya gwamnatin Najeriya ta ayyana ƴan Boko Haram a matsayin ƴan ta'adda.
Yayin da ƴan IPOB da ƴan ƙungiyar Shi'a kuma aka haramta su, kuma dukansu an san su kuma an san manufarsu, amma a cewarsa su ƴan bindiga ba a san su ba haka kuma ba su da wata ƙungiya ko wani babban shugaba a Najeriya.
"Abin da muke jin tsoro ka da a sa shaida na yare ko addini ya zama da shi ake kwatanta ɗan ta'adda, a duk duniya ana mayar da ƙungiya ce sananniya wadda ta yi suna" in ji shi.
Ya bayyana cewa a ganinsa gwamnatin Najeriya ta gaji da irin ce-ce-ku-cen da ake yi na cewa ta ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda wanda hakan ya ja har ƴan majalisa su ma suka matsa kan sai an ɗauki wannan mataki.

Ko ayyana su a matsayin ƴan ta'adda zai kawo sauyi?
A cewar Barrista Bulama Bukarti mai sharhi kan al'amuran tsaro, ya ce ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda ba zai kawo ƙarshen ta'addanci ba ko sauya wani abu ba, aiwatarwa da aiki ne zai kawo ƙarshen hakan.
Bukarti ya ce idan aka tashi tsaye aka yi yaƙi da su gadan-gadan a cikin wata uku za a iya gamawa da ƴan ta'addan.
Sai dai Group Captain Saddik mai ritaya ya ce yana da shakka kan ko za a samu sauyi duk da an ayyana su a matsayin ƴan ta'adda.
"Tun kafin a yayyana su a matsayin ƴan ta'adda, yaƙin da sojojinmu da ƴan sandanmu ke yi da yan bindiga suna iya bakin ƙoƙarinsu.
"Ban yi tsammanin akwai wani ƙarfi ko wata dabara ko akwai wasu kayan aiki da ake jira sai an ayyana su a matsayin ƴan ta'adda a fito da su domin a yaƙe su ba," in ji shi.

Sabbin matakan da ya kamata gwamnati ta ɗauka
Bayan matakin da gwamnati ta ɗauka a kan ƴan bindiga, ƴan Najeriya da dama za su so ganin sabbin matakan domin yaƙi da ƴan bindiga.
A cewar Group Captain Saddik, yawan sojoji da ƴan sanda da kayan aikin da Najeriya ke da su, fadin Najeriya ya yi musu yawa inda ya ce akwai buƙatar a samu ƙarin jami'an tsaro da kayan aiki.
Shi ma a na shi ɓangaren, Barrista Bulama Bukarti ya bayyana cewa akwai buƙatar jami'an tsaro su samu ƙarin kayan aiki musamman ɓangaren masu leƙen asiri.
A cewarsa, idan ba a tattara bayanai da kyau ba, ba za a iya yaƙarsu ba domin ba a san sirrinsu ba ko kuma za a iya yaƙar waɗanda bai kamata a yaƙa ba.
Ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar gwamnati ta toshe hanyar samun kuɗinsu da abinci da makamai.

Me hakan ke nufi a fannin shari'a?
A baya BBC ta tuntuɓi wani mai sharhi kan harkokin shari'a Barrister Sa'idu Tudun Wada, wanda ƙwararren lauya ne a Kano, inda ya ce ayyana ƴan bindigan a matsayin ƴan ta'addda ba ƙaramar nasara ce ba ga ƴan Najeriya.
"A hukumance, kotu ta samu damar da za ta ayyana duk wanda ta samu da laifin aikata haka ta yanke masa hukuncin kisa, wannan zai tsoratar da su masu aikata laifin.
"Bugu da ƙari shi kansa laifin yanzu da masu aikata shi an faɗaɗa shi, ta hanyar cewa duk wani wanda yake mu'amala ta kusa ko ta nesa ko kuma yake taimaka musu ta hanyar kuɗi, ko karɓar kuɗin ko ɓoye kuɗin, shi ma hukuncin kisa ya hau kansa," in ji Barrister Tudun Wada.
Ya kuma ce a halin gwamnati za ta samu dama wajen tuntuɓar al'ummar duniya wajen neman taimako da kuma haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kawar da wannan matsalar da ta addabi ƙasar.

Matsalar harin ƴan bindiga da satar mutane a Najeriya na neman zame wa al'umma da mahukunta alaƙaƙai, sakamakon ƙunci da asarar rayuka da dukiya da lamarin ke haddasawa. Mahara sun tilasta wa mazauna yankunan karkara ƙaurar dole, suna kona musu gidaje, da hana su noma da sauran sana`o`i.
Tun ana kukan yawaitar satar mutanen a ƙauyuka da biranen wasu jihohi, yanzu mazauna Abuja, babban birnin tarayyar ma, musamman na gefen gari a cikin zullumi suke, duk kuwa da cewa mahukunta na alwashin daukar matakan kariya.












