Sheikh Gumi na so gwamnati ta ba shi kayan aikin da zai yi wa 'yan fashin daji wa'azi

Bayanan bidiyo, Gumi na so gwamnati ta ba shi kayan aikin da zai yi wa 'yan fashin daji wa'azi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya yi kira ga gwamnati ta ba su kayan aiki domin su shiga daji su yi wa 'yan fashi wa'azi.

Ya yi kiran ne a tattaunawarsa da BBC Hausa.

Ya kara da cewa matakin zai taimaka wajen shawo kan hare-haren da 'yan fashin daji suke kai wa a wasu sassan kasar.

Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Chukwuemeka Anyikwa