Bidiyo: Tsohon shugaban Najeriya Abdussalami Abubakar ya koka kan matsalar tsaro
Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja Janar Abdussalami Abubakar mai ritayata ya bayyana takaici kan yadda tsaro ke kara tabarbarewa a kasar.
Janar Abdussalami wanda kuma shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na kasar, ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da editan BBC Hausa Aliyu Tanko, bayan wani taro da aka gudanar a Abuja da nufin nemo hanyar magance matsalolin da kasar ke fusknata ta fuskar tsaro.
Tsohon shugaban ya kuma yi tsokaci kan irin rawar da sojojin kasar ke takawa wajen tabbatar da tsaro a kasar da kuma hare-haren da ake kai wa jami’an tsaro a kudu maso gabashin Najeriya.