Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tinubu na shan suka kan zargin fifita jihar Lagos kan Arewa
Gwamnatin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da shan suka kan zargin fifita jihar Lagos a ayyukan raya kasa, musamman daga wasu 'yan yankin arewacin kasar.
Wannan batun ya janyo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan a kasar tsakanin wasu 'yan arewacin Najeriyar da kuma masu kare gwamnatin ta Tinubu, kan zargin shugaban ya fi bayar da fifiko wajen samar da manyan ayyukan cigaban kasar, yayin da wasu jihohi da yankuna ke fama da matsalolin tsadar rayuwa da tabarbarewar ababen more rayuwa.
'Yan siyasa da masu fafutukar kare hakkin bil'adama daga arewacin kasar na zargin gwamnatin da rashin nuna kulawa ta musanman, kamar yadda gwamnatin ke nuna kulawa da jihar Lagos, maimakon gaba dayan kasar musamman ma arewaci.
Masu sukar na cewa hakan ya ta'azzara matsalar tattalin arziki da kuma zamantakewar al'ummar yankin na arewa.
Suna zargin ne inda suke cewa gwamnatin ta mayar da bangaren na arewa tamkar saniyar-ware, tare da ikirari ya taka rawar gani fiye da sauran bangarorin kasar musamman ma jihar Lagos din, a nasarar da Shugaba Tinubun ya samu a zaben da ya kai ga hawansa mulki a zaben 2023.
Sai dai gwamnatin kasar ta ce duk wasu ayyuka ana gudanar da su ne domin ci gaban al'ummar Najeriyar baki daya, bisa la'akari da yadda kowane aiki zai tabbatar da bunkasar kasar baki daya.
Tun bayan hawan Shugaba Tinubu, gwamnatinsa ta fara gudanar da manyan ayyuka da dama, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce, bisa zargin nuna fifiko ga jihar Lagos.
Masu zargin na kokawa da cewa gwamnatin ta bar arewacin da alkawura kawai, in banda sabinta tsofaffin ayyukan da wasu gwamnatoci suka fara tun a baya.
Suna zargin cewa manyan ayyuka da ake gudanarwa a Lagos duk sababbi ne,
Ayyukan da suka hada da katafariyar hanyar da ta tashi daga gabar Tekun Lagos zuwa Kalaba da babbar gadar ruwa ta Fourth Mainland Bridge da babbar tashar jiragen sama ta kasa da kasa a Lekki.
Alhaji Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu kuma tsohon dan takarar gwamna a jihar Kano, na daga cikin masu zargin gwamnatin shugaban, inda ya ce manyan ayyuka sun taru a jihar da ke yankin kudu maso yammacin kasar kadai.
Ire-irensa sun bayyana cewa jiha kamar Kano, cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya, da kan bayar da gudummawar kusan kashi 15.4 cikin dari na arzikin kasa da ba na bangaren man fetur ba, an bar ta ba tare da wasu manya-manyan ayyukan more rayuwa na gwamnatin tarayya da ya wuce maganar fatar baka da alkawarin sabuntawa ba kawai.
'Yan fafutukar kare hakkin bil'adama kamar su Kwamared Aliyu Charanchi na kungiyar CNG sun yi kira ga al'ummar arewacin da su farka game da yadda ake mayar da shiyyar baya, yana mai jaddada bukatar a raba ayyukan kasa cikin adalci.
Sai dai daya daga cikin masu magana da yawun gwamnatin Shugaba Tinubun, Abdulaziz Abdulaziz, ya kare matakin gwamnatin, inda ya bayyana cewa an tsara ayyukan ne don amfanin al'umma 'yan kasa baki daya, wanda kowanne bangare na kasar zai ci gajiya.
Wannan batu dai shi ne abin da kusan ake ta tafka muhawara a kansa, game da daidaiton hakkin samar da manyan ayyukan gwamnatin tarayya a shiyyoyi shida na kasar.
Yayin da gwamnati ke kare ayyukanta a fadin kasar baki daya, masu suka na cewa jihar Lagos din kadai ba ma sauran jihohi na yankin kudu maso yammaci ko ma sauran yankunan kudanci ba, na cin gajiya fiye da kima, idan aka kwatanta da arewacin kasar.
Ko a baya-bayan nan ma tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dantakarar shugaban kasar na jam'iyyar NNPP, a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ma ya zargi gwamnatin ta Tinubu da mayar da bangaren arewacin kasar saniyar-ware, wajen samar da ayyukan raya kasa, a kan yankin kudanci, musamman ma
Masu sharhi kan harkokin siyasa dai na cewa dole gwamnatin Tinubu ta tashi ta kare kanta bilhakki ko kuma masu hamayya da gwamnatin su kafa hujjarsu kan wadannan korafe-korafe.
Abin jira a gani shi ne ko wadannan korafe-korafen da shiyyar ta arewa ke gabatarwa su ne za su kasance wani mizanin tantance ayyukan gwamnatin Shugaba Tinubu, tare da samar da sauyi mai kyau ga yankunan da abin ya shafa.