Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa maza ke mafarkin saduwa, ko hakan alama ce ta rashin haihuwa?
Akwai jita-jita da yawa da ake yi kan batun fitar maniyyi ga maza a lokacin da suke barci, kuma maza da yawa sun yi imanin cewa jin mutum yana tafiya lokacin barci, alama ce ta rashin haihuwa ko rashin wadataccen maniyyi a wurin maza.
Jin dadin da ke haifar da fitar maniyyi ga maza yayin barci abu ne da aka saba, a cewar masana kiwon lafiya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a daidai lokacin da yara maza suka fara balaga, yawan ƙwayoyin halittan namiji na ƙaruwa, wanda wani lokaci zai kawo tsaiko wurin barci.
Mafarke-mafarken jima'i
Masu bincike a jami'ar Shu Yin ta Hong Kong, sun gudanar da wani bincike mai taken 'Mafarkin Jima'i,' domin ƙoƙarin gano abin da ya sa ake yin sa yayin barci.
Kashi 80 cikin 100 na waɗanda suka shiga binciken sun shaida wa masu binciken cewa yin mafarkin jima'i yayin barci yana sa su fitar da maniyyi. An yi imanin cewa yara suna yawan yin irin waɗannan mafarke-mafarke.
Sun ce suna yin irin wannan mafarki kusan sau tara a shekara.
Hakanan an yi imanin cewa nau'in mafarkin da kuke yi yana da alaƙa da tunanin da kuka fi yi ko ma kuke sha'awa. Amma wannan binciken ya kalubalanci wannan batu.
Bincike ya nuna cewa, duk da cewa jima'i wani muhimmin ɓangare ne na rayuwar ɗan'adam, amma ba a fiya yin mafarki a kansa ba, abin da ke nufin cewa yawan masu yin sa ba shi da yawa.
Masanin ilimin jima'i Dakta Kamaraj ya ce, "jikin namiji a yana samar da maniyyi a ko dayaushe. Idan ba a fitar da maniyyin ta hanyar jima'i ba, za a iya fitar da shi lokacin barci. Wannan tsari ne na halitta."
Dakta Bhupati Jan ya ce, "Kamar yadda mata suke haila, su ma maza ma suna fitar da maniyyi.
Shin wannan zai iya janyo matsalar rashin haihuwa ga maza?
Masu bincike daga kwalejin kiwon lafiya ta Tongji da ke ƙasar China, sun ba da misali da wani binciken da aka wallafa a shafin shafin intanet na ɗakin karatu na likitanci na ƙasar Amurka, wanda ya kwatanta samfurin maniyyi daga maza masu matsalar rashin haihuwa da na maza masu lafiya.
Binciken ya gano cewa kashi 72 cikin 100 na rashin haihuwa tsakanin maza na faruwa ne sakamakon 'rashin ƙarfin maza'. Lamarin na bai wa maza wahala wajen fitar da maniyyi yayin jima'i.
Duk da haka, suna iya yin mafarki kan jima'i yayin barci.
Don wannan binciken, an yi nazarin maniyyin maza 91 da ke fama da matsalar fitar maniyyi ko kuma rashin lafiya.
Binciken ya nuna cewa maniyyin da ake fitar wa lokacin barci ya kai kashi 30.6 fiye da sauran maniyyi da ake fitar wa ta wasu hanyoyi.
Ya gano cewa maza masu fama da rashin ƙarfin maza suna da lafiyayyen maniyyi kuma ana sakinsa yayin barci.
Rahoton ya bayyana cewa ko da yake ba a san lokacin fitar da maniyyi ba yayin barci, an buƙaci mazan da ke cikin binciken da su kwana da kwaroron-roba har na tsawon watanni uku.
Ingancin maniyyin da ake fitar wa lokacin barci ya bambanta. Binciken ya nuna cewa za a iya amfani da maniyyin wajen saka wa mace domin ƙauce wa raɗaɗin ƙarfin maza.
Dakta Kamraj ya ce, "Yara daga shekara 12 zuwa tsoffi kan fuskanci matsalar rashin ƙarfin maza. Babu hujja ta kimiyya da ta ce hakan na janyo rashin haihuwa ko rashin wadataccen maniyyi a wajen maza ba."
"Jiki na samar da sabon maniyyi bayan fitar da wani. Kawowa ko biyan buƙata yayin barci ba ya shafar rashin haihuwa ko yawan maniyyi.
Me ya sa ake mafarki kan jima'i?
Dr. Bhupati Jan ya ce, "Jiki na adana maniyyin da yake samarwa. Maniyyin da ke jiki ke samarwa ya bambanta daga wanna zuwa wancan. Kamar yadda ruwa ke fitowa cikin tankar ruwa idan ta cika, haka maniyyi ke fita."
Dakta Kamaraj ya ce yin mafarkin yin jima'i ba ya nufin cewa mutum yana ɗauke da wata cuta.
Ya ƙara da cewa "an yi bincike kan wannan batu, amma ba a kai ga gano abin da ya sa ake mafarkin jima'i ba."
"Wannan na faruwa ne watakila saboda burin mutum na jima'i ko kuma idan yana jin sha'awa.
"Babu wata hujja da ke nuna cewa waɗannan mafarke-mafarke kan shafi rashin yawan maniyyi ko jima'i yadda ya kamata ba," in ji shi.
Kamaraj ya ce, "Kawowa ba tare da jima'i ko biya wa kai buƙata ba alama ce ta lafiyan jiki."