Ana zaɓen da aka bayyana da naɗi a Cambodia

Firaminista Hun Sen na zaɓe

Asalin hoton, Reuters

A ranar Lahadin nan ake babban zabe a Cambodia, inda ake sa ran Firaminista Hun Sen zai yi nasara.

Kamar dai a shekara biyar da ta gabata, a wannan karon ma an haramta wa babbar jam’iyyar hamayya shiga takara.

Mista Hun Sen, tsohon kwamandan soja na sa ran a samu fitowar masu zabe sosai, yayin da yake shirin mika mulki ga dansa bayan shekara talatin da takwas a kan mulki.

Yayin da Firaminista Hun Sen ke daukar babban zaben a matsayin wani gagarumin cigaba a siyasar kasar ta kudu maso gabashin Asiya, wasu na bayyana zaben a matsayin nadi kawai ba zabe ba, domin babu babbar jam’iyyar hamayya a ciki.

Sauran jam’iyyu goma sha bakwai da aka bari su yi takara, kanana ne da ba za su iya yin wani tasiri ba balle wata barazana ga jam’iyya mai mulki, wato Cambodian People’s Party, ko CPP.

Daman jam’iyya daya tilo da za ta kasance barazana ga mai mulkin ita ce, ta Candlelight, kuma wata biyu baya aka ayyana cewa ba ta cancanci shiga zaben ba, bisa wasu dalilai na abin da kotu da ake ganin na bin ra’ayin gwamnati ta ayyana rashin bin ka’idoji.

Daman an samar da jam’iyyar ta Candlelight ne daga birbishin tsohuwar hadakar ‘yan hamayya ta kasar, CNRP, wadda kotuna suka haramta.

Bayan haramcin an kuma yi wa jagoran hadakar, Kem Sokha daurin-talala a gida, na shekara 27, bisa laifin cin manar kasa.

Kungiyoyin kare hakkin dan’Adam sun bayyana hukuncin a matsayin siyasa.

Kamar a baya ma a wannan karon Firaminista Hun Sen, mai shekara 70 yana takara ne bisa tarihin da ya kafa na na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Cambodia, bayan shekaru na mummunan yaki da juyin-juya-hali, da suka gabaci mulkinsa.

Hun Sen ya kasance daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa a kan mulki a duniya, inda ya kasance firministan tun 1998.

To amma kasancewar kusan rabin yawan masu zaben ‘yan kasa da shekara 35 ne, kadan ne daga cikin ‘yan kasar za su iya tuna wancan lokacin na tashin hankali.

Kuma gagarumin cigaban tattalin arziki da kasar ta samu tun shekarun 1990, ya gamu da rashawa da barnata muhalli da kuma rashin daidaito a tsakanin ‘yan kasar.

Babban dan Firaminista Hun Sen, wanda ake sa ran zai gaje shi bayan zaben shi ne ke jagorantar yakin neman zaben jam’iyyar mai mulki, CPP, da ake sa ran za ta sake cinye duka kujerun majalisar dokokin kasar, ashirin da biyar.

Domin tabbatar da an samu gagarumar fita a zaben, wanda ba a ba jama’a dama ta gaskiya ta zaben jam’iyyar da ta kwanta musu a rai ba, gwamnati ta zartar da wata doka da ta sa duk wani yunkuri na kaurace wa zaben ko bata takardar zaben ya zama babban laifi.