An raba takalmin zinare shida a gasar Euro 2024

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Ƙyaftin din tawagar Ingila, Harry Kane ya ƙarbi ƙyautar takalmin zinare a Euro 2024 tare da ƴan wasa biyar a matakin waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye.

Sauran da suka karɓi ƙyautar sun haɗa da ɗan wasan Sifaniya, Dani Olmo da na Georgia, Georges Mikautadze da na Netherlands, Cody Gakpo da na Slovakia, Ivan Schranz da kuma na Jamus, Jamal Musiala.

Kane da Olmo sun buga wasan karshe ranar Lahadi a birnin Berlin, amma ba wanda ya zura ƙwallo a karawar da Sifaniya ta doke Ingila 2-1.

A baya a kan tantance gwarzo, idan aka duba yawan ƙwallon da ya ci da waɗan da ya bayar aka zura a raga, amma a Euro 2024 Uefa ta ce da yawan cin ƙwallaye za ta yi amfani.

Kane, mai taka leda a Bayern Munich, mai shekara 30 ya ci Denmark da Slovakia da kuma Netherlands a Euro 2024.

Kane shi ne ya lashe ƙyautar takalmin zinare a gasar Bundesliga ta Jamus da ta wuce, wanda ya zura ƙwallo 36.

Tsohon ɗan wasan Tottenham shi ne kan gaba a yawan ci wa tawagar Ingila ƙwallaye a tarihi, kuma shi ne ya lashe ƙyautar a kofin duniya a 2018, wanda ya zura shida a raga.

Ɗan wasan Sifaniya da Manchester City, Rodri, shi ne ya lashe ƙyautar fitatcen ɗan ƙwallo a Euro 2024.

Haka kuma Lamine Yamal na Sifaniya da Barcelona shi ne matashin ɗan wasan gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.