Agogon da ke hasashen tashin duniya ya ƙara matsawa da daƙiƙa ɗaya

    • Marubuci, Jaroslav Lukiv
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Agogon da ke hasashen tashin duniya ya ƙara matsawa da daƙiƙa ɗaya, inda yanzu ya rage daƙiƙa 89 ko kuma minti ɗaya da sakan 20 kafin tashin duniya - mafi kusa da ya taɓa kaiwa.

Ƙungiyar masu nazari kan harkokin kimiyya ta Bulletin of Atomic Scientist (BAS) - wadda ke saita agogon a duk shekara, ta ce barazanar makaman nukiliya, da kuma fargabar yin amfani da abubuwan cigaba a fannin ilimin halittu ba yadda ya kamata ba, da ƙirƙirarriyar basira, da kuma sauyin yanayi su ne manyan abubuwan da ake dubawa.

Daniel Holz, shugaban kwamitin kimiyya da tsaro na ƙungiyar, ya ce wannan matakin ''gargaɗi ne ga dukkan shugabannin duniya''.

Agogon ya fara aiki ne tun a shekarar 1947, inda ya fara daga mintuna bakwai kafin tashin duniya.

A bara, ba a sauya shi ba daga daƙiƙa 90 da yake.

A cikin sanarwar da ƙungiyar mai zaman kanta da ke Chicago ta fitar, ta ce ''matsar da agogon da muka yi da daƙiƙa ɗaya, tamkar muna aikewa da saƙo mai ƙarfi ne.''

''Saboda duniya ta na ta ƙara kusantar faɗawa halaka, matsawa ko na daƙiƙa ne alamari ne da ya kamata a ɗauka a matsayin alama da ke nuna tsananin haɗari kuma gargadin cewa duk daƙiƙa ɗaya da ya wuce ya na ƙara mana kusanci ga faɗawa bala'i a faɗin duniya.''

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa cigaba da yaƙi a Ukraine- wanda yanzu a ke kusantar shekaru uku bayan mamayar Rasha- '' zai iya rikiɗewa ya koma yaƙin nukiliya a kowane lokaci saboda wani matakin gaggawa ko kuskure ko kuma rashin lissafi.

''Rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya na barazanar tsananta ya zama babban yaƙi ba tare da gargaɗi ko alamu ba,'' in ji sanarwar.

Tawagar masu bincike kan kimiyyar sun kuma ce ''shirin dogon lokaci da duniya ta yi na magance sauyin yanayi ba ya tasiri sosai, ganin cewa akasarin gwamnatoci sun gaza aiwatar da tsarin samar da kuɗaden da ake buƙata domin daƙile ɗumamar yanayi.''

A fannin ilimin halittu, ƙungiyar BAS ta cigaba da cewa, ''cututtukan da ke ɓullowa da waɗanda ke sake dawowa na cigaba da yin barazana ga tattalin arziki, da al'umma da kuma tsaro a faɗin duniya''.

Ƙungiyar ta kuma yi gargaɗin cewa '' jerin wasu sabbin fasahohi sun bunƙasa a bara, a wani yanayi da suka sa duniyar ta ƙara haɗari''.

''An yi amfani da tsarin da ake sanya ƙirƙirariyyar basira cikin samamen da ake yi a Ukraine da gabas ta tsakiya, kuma wasu ƙasashe da dama sun fara yunƙurin sanya ƙirƙirarriyar basirar cikin ayyukan sojojinsu.''

Ƙungiyar ta jaddada cewa dukkanin waɗannan barazanar ''na ƙara tsananta ne saboda wasu dalilai kamar: yaɗa labaran ƙarya, da labaran da ba su da tushe da ke kawo cikas ga tsarin sadarwa kuma ya kuma toshe layin da ke tsakanin gaskiya da ƙarya.

A cewar ƙungiyar BAS, Amurka da China da Rasha na da ƙarfin haɗin gwiwar da za su ruguza ɗan'adam baki ɗaya'', inda ya ƙara da cewa ƙasashen uku ''na da alhakin fitar da duniya daga barazanar halaka''.