An buƙaci Fifa ta faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta 2030 zuwa ƙasashe 64

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Kudancin Amurka (Conmebol) ta gabatar da buƙata a hukumance na ƙara yawan ƙasashen da za su halarci Gasar Kofin Duniya ta 2030 zuwa ƙasashe 64.
Haɗakar ƙasashen Sifaniya da Morocco da Portugal ne za su karɓi baƙuncin gasar, bayan buɗeta a ƙasashen Argentina da Paraguay da kuma Uruguay.
Gasar Kofin Duniya ta 2026 ce ta farko da ƙasashe 48 za su halarta, to amma Conmebol na son a faɗaɗa gasar a 2030 domin murna cika shekara 100 da fara gasar.
"Hakan zai bai wa ƙasashen duniya damar kallon gasar, don haka ba wanda za a bari a baya dangane da bikin da za a yi na cika shekara 100 da fara gasar,'' a cewar Shugaban Conmebol, Alejandro Dominguez a wani taro da hukumar ta gudanar ranar Alhamis.
"Mun yarda cewa bikin cika shekara 100 na gasar zai zama na ƙasaitacce, saboda ba a taɓa yin irinsa ba'', in ji shi.
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Uruguay, Ignacio Alonso ne ya fara gabatar da buƙatar a lokacin taron Fifa da aka gudanar cikin watan Maris.
Cikin wata sanarwa da hukumar Fifa ta fitar ranar Juma'a, ta ce haƙƙinta ne ta yi nazarin kowace shawara da mambobinsu suka gabatar.
Shugaban hukumar ta Fita, Gianni Infantino ya halarci taron Conmebol na ranar Alhamis, inda kuma ya bayyana cewa Gasar 2030 za ta zama ''gagaruma'' da ba a taɓa gani ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarar 2017, aka ɗauki matakin faɗaɗa ƙasashen da za su halarci gasar 2026 zuwa 48 bayan duka mambobin Fita sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da matakin.
A anar 15 ga watan Mayu mai zuwa ne za a gudanar da taron Fifa na 75, kuma a nan ne za a tattauna buƙatar ta Conmebol.
Idan har aka amince da buƙatar, gasar ta 2030 za ta ƙunshi karawa 128, daga karawa 64 da ake yi tsakanin 1998 zuwa 2022.
Masu sukar matakin dai na cewa faɗaɗa gasar zai rage darajar tsarin da ake bi wajen tantance cancantar shiga gasar, yayin da ƙungiyar kare muhalli ta FFF ta ce shawarar buga gasar a nahiyoyi uku "barazana ce ga muhalli".
Tuni dai afarkon watannan shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Turai, Aleksander Ceferin ya bayyana matakin a matsayin ''mummunar shawara''.
"Wannan shawara ta yiwu ta fi ba ni mamaki fiye da ku, ni ina ganin wannan shawara ce maras kyau a ra'ayima," in ji Ceferin a wani taron manema labarai.
Za dai a fara gasar 2030 a Uruguay - ƙasar da ta fara lashe gasar a 1930, a wani ɓangare na bikin cika shekara 100 da fara gasar.











