Ko nasarar ƴan hamayya ka iya kawo karshen mulkin shugaba Erdogan?

Magoya bayan shugaba Erdogan

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Erdogan ya lashi takobin gyara kura-kuran da suka janyo jam'iyyarsa ba ta samu nasara a zaɓukan magadan gari da aka yi ba
    • Marubuci, Cagil Kasapoglu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service, Istanbul

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da jam'iyyarsa mai mulki ta AK, sun samu koma baya a zaɓukan kananan hukumomin da aka gudanar a ranar Lahadi.

An gudanar da zaɓen ne yayin da ƙasar ke fuskantar matsalar tattalin arziki.

Jam'iyya mai mulkin ƙasar ta samu gagarumin koma baya a biranen da take da rinjaye, to ko me wannan shan kaye da jam'iyyar ta samu ke nufi ga makomar Erdogan?

Babbar jam'iyyar adawa a ƙasar CHP, ta samu kashi 37.8 cikin 100 a gaba ɗayan kuri'un da aka kaɗa, yayin da jam'iyya mai mulki kuma ta samu kashi 35.5 cikin 100.

Yawancin kwararru na ganin wannan zaɓe a matsayin wani gagarumin koma baya ga Mista Erdogan.

Jam'iyyar CHP, ba wai ta yi nasara a kan jam'iyyar AK mai mulki ba ne a sassan ƙasar kaɗai, ta samu sakamako mafi rinjayen da ba a taɓa samu ba tsawon gomman shekaru.

Ko ya aka yi hakan ta faru?

Matsalar tattalin arziki: Hauhawar farashi da rashin gamsuwa da salon mulki daga al'ummar ƙasar

Matsalar tattalin arzikin da ake fama da shi a Turkiyya shi ne makasudin abin da ya janyo faɗuwar jam'iyya mai mulki.

Ba kamar sauran ƙasashe ba da suka fara fuskantar matsalar tattalin arziki a 2022 bayan da aka fara yaƙin Ukraine, Turkiyya ta fara fuskantar wannan matsala ce tun a 2018.

Matakin hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 65 cikin 100, yayin da darajar kuɗin ƙasar lira kuma ta faɗi da kashi 80 cikin 100.

Ana yawan zargin gwamnatin Turkiyya karkashin jagorancin Mista Erdogan da nuna ko-in-kula ga halin da talakawan ƙasar ke ciki.

Mutane a kasuwa na siyayya

Asalin hoton, Chris McGrath/Getty Image

Bayanan hoto, Halin matsin rayuwa na daga cikin abubuwan da suka janyo jam'iyyar Erdogan ta sha kaye a zaɓukan da aka gudanar
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Jam'iyya mai mulki ta AK, ta makara wajen magance irin matsalar tattalin arzikin da ake fama da shi." in ji H. Bahadir Turk, farfesa ne a sashen kimiyyar siyasa a jami'ar Haci Bayram Veli da ke Ankara.

Ya ce duk da wannan matsala da ake fama da ita a ƙasar, Mista Erdogan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a 2023 haka ma jam'iyyarsa, to amma duk da haka sun gaza shawo kan wannan matsala.

Ya ce "Na yi amanna wannan ne babban kuskuren da jam'iyya mai mulki da kuma Mista Erdogan suka yi."

Batun matsin rayuwa shi ne ya mamaye yaƙin neman zaɓen da aka yi.

"Bai kamata a ce ƙasar nan na fama da talauci ba" bisa la'akari da kasancewarta ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da ke da tarihin tattalin arziki". In ji magajin garin Istanbul, wanda ke neman a sake zaɓarsa, a yanzu an sake zaɓarsa inda zai sake shafe shekaru biyar a kan mulki.

Imamoglu, ɗan takara ne a jam'iyyar CHP, ya zargi Mista Erdogan da hargitsa tattalin arzikin ƙasar.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da Erdogan ya sake samun nasara a karo na uku, ya yi alkawarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

To amma a zaɓukan kananan hukumomi na 2024 da aka yi a ranar Lahadin da ta wuce, kwararru sun ce masu kaɗa kuri'a na son aika wa Mista Erdogan da ma jam'iyya mai mulkin ƙasar sako ne.

"Ba abun mamaki bane masu kaɗa kuri'a su juya wa shugabansu baya a lokaci guda. A zaɓukan kananan hukumoi, ba su zaɓi jam'iyya mai mulki ba. Sako suke son aika wa shugaba ƙasar cewa ba sa jin daɗi ko kuma ba su gamsu da salon mulkin jam'iyyar ba shi ya sa suka ki zaɓarta," in ji Farfesa Evren Balta, na sashen kimiyyar siyasa a jami'ar Ozyegin da ke Istanbul, kamar yadda ta shaida wa BBC.

Kalubalen da ke gaban ƴan hamayya

Ekrem Imamoglu, na gaishe da magoya bayansa supporters during his speech in Istanbul - 01 Apr 2024

Asalin hoton, ERDEM SAHIN / EPA-EFE

Bayanan hoto, Ana ganin Mista Imamoglu a matsayin wanda ya dace da shugaban ƙasar

Babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar ta CHP, ta samu nasara a manyan biranen ƙasar kamar Istanbul da Ankara da Izmir, sannan ta samu nasara a sauran birane kamar Bursa.

A shekarar 1923 ne aka kafa jam'iyyar wadda Mustapha Kemal Ataturk, ya kafata.

Jam'iyyar ta CHP, ta sha zargin jam'iyyun siyasa ciki har da AKP, da ci da addini.

Batun masu tsatsauran ra'ayin addini da kuma 'yan ba ruwanmu da addini ne ya mamaye siyasar Turkiyya tsawon gwamman shekaru.

To amma a shekarun baya-bayan nan jam'iyyar CHP, ta sauya abin da ake gani shi ne ya ɓata nasara.

Magoya bayan Ekrem Imamoglu

Asalin hoton, REUTERS/Umit Bektas

Bayanan hoto, Magoya bayan Mista Imamoglu sun taru a gaban wani gini da ke Istanbul don murna a kan nasarar da ya samu a ranar Lahadi

"Tun shekara ta 2017 bayan yunkurin juyin mulkin 2016 da aka yi a Turkiyya, jam'iyyar CHP, ta sauya salon siyasarta na daidaitawa da masu tsatsauran ra'ayi, abin da ya kawo karshen batun rarrabuwar kawuna kenan." in ji Farfesa Balta.

A Istanbul, ɗaya daga cikin abin da ya sa ɗan takarar CHP, Imamoglu ya samu nasara ko kuma aka sake zaɓarsa shi ne goyon bayan al'ummar Kurdawa, duk da cewa akwai 'yan takarar da ke goyon bayan Kurdawa da ke cikin takardar zaɓen.

Ta ce "A ɓangare guda kuma, akwai ɗan takarar jam'iyyar AK, waɗanda ke kiran Kurdawa a matsayin 'yan ta'adda. Yayin da gefe guda kuma ɗan takarar CHP, Imamoglu na ɗaukar Kurdawa a matsayin 'yan ƙasa. Hakan ya sa suka zaɓi wanda ke son su wato Imamoglu."

Wani dalili da ya sa kuma jam'iyyar hamayya ta samu nasara a wannan zaɓen shi ne irin bayanan da suka rinka yi wa masu kaɗa kuri'a a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Masu suka dai na zargin Mista Erdogan da kankane kafafen yaɗa labaran ƙasar, ma'ana sai abin da ya ke so suke yi.

Ko wannan rashin nasarar ya kawo karshen shugaba Erdogan kenan?

Kodayake masu sharhi sun yi amanna cewa ya yi wuri a fara magana a kan batun faɗuwar Mr Erdogan ko jam'iyyarsa, ko kuma a ce karshen mulkinsa ya zo ba.

Sai a 2028, wa'adin mulkin Mr Erdogan zai zo karshe, kuma komai zai iya canja wa kafin wannan lokaci.

Haci Bayram Veli, ya ce "Yayin da ake cewa jam'iyyar hamayya ta kankane zaɓukan kananan hukumomi da aka yi a 2024, har yanzu Mr Erdogan ya kankane komai a Turkiyya, kama daga siyasar ƙasar da kuma karfin fadɗ a jinsa."

Ya ce "Kada mu manta yawancin masu kaɗa kuri'a har yanzu suna ganin kimarsa da kuma kaunarsa."

A cewar Farfesa Turk, nasarar jam'iyyar AK, ta dogara ne ga zaman lafiyar da ake tsakanin gwamnatin Erdogan mai kwar jini da kuma jam'iyyar.

"To amma ina ganin zaman lafiyar da kwar-jinin na raguwa a hankali bisa la'akai da sakamakon zaɓen da aka yi."

Sake zaɓar magajin garin Istanbul, Ekrem Imamoglu, a yanzu ana ganin shi ne mutumin da ya dace da takarar shugaban ƙasar, kodayake har yanzu bai sanar da aniyarsa a hukumance ba.

Magoya bayan shugaba Erdogan

Asalin hoton, NECATI SAVAS/ EPA-EFE

Bayanan hoto, Magoya bayan Mr Erdogan sun taru a shalkwatar jam'iyyar AK bayan da jam'iyyarsu ta sha kaye a zaɓukan kananan hukumomi

Shekara 20 ɗin da ya shafe yana mulki, karfin siyasa da karfin faɗa a jin shugaba Erdogan ya faɗaɗa har zuwa iyakokin ƙasar ta Turkiyya.

Ya sanya kansa a matsayin mai shiga tsakanin Rasha da Ukraine, inda ake tattaunawa a kan muhimmancin yarjejeniyar fitar da hatsi, hakan kuma ya karawa Turkiyya karfin dangantaka da ƙasashe kamar na Afirka da Asiya.

Duk da ya ke wa'adin mulkin Mr Erdogan bai zo karshe ba, sakamakon waɗannan zaɓukan ya nuna irin babban kalubalen da ke gabansa.