Mutumin da ya ƙirƙiro fitacciyar fistol Glock ya rasu

Gaston Glock, injiniya ɗan ƙasar Austria da ya ƙirƙiro ƙaramar bindigar hannu mai suna Glock, ya rasu yana da shekara 94.

Kamfanin Glock ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa ayyukan mutumin da ya kafa kamfanin lokacin da yake raye "ruhinsa zai ci gaba" da su.

Dakarun tsaro da jami'an tsaro da fararen hula masu mallakar bindiga da ɓata-gari a faɗin duniya, duk suna amfani da makamin.

Bindigar ta ƙara samun shahara ne sanadin harkokin kiɗan fof na Amurka da ganinta a fitattun fina-finan Hollywood ciki har da fim ɗin almarar kimiyya na The Matrix Reloaded.

Duk da shaharar bindigar da ya ƙirƙiro, an bayyana Glock a matsayin biloniyan da bai cika son shiga mutane ba, kuma yakan kwashe mafi yawan lokacinsa a katafaren gidansa da ke gaɓar tafki a ƙasar Austria.

Ba kasafai ake jin ɗuriyarsa ko a labarai ba, ya shiga kanun labarai ne kawai lokacin da aka wallafa wani littafi game da harkokin kasuwancinsa a 2012, bayan sun rabu da matarsa ta farko a 2011 da kuma lokaci da wani abokin kasuwancinsa ya yi ƙoƙarin ganin an kashe shi a ƙarshen shekarun 1990.

A wannan al'amarin, maharin da aka yiwo haya ,wanda ƙwararren ɗan dambe ne, ya buga masa gudumar roba sau bakwai a ka, amma Glock a lokacin yana ɗan shekara 70, ya yi kukan kura, ya hamɓare shi.

"Gaston Glock ya shata wata muhimmiyar alƙibla ga Gungun kamfanonin Glock gaba ɗayan rayuwarsa sannan ya shirya shi don tunkarar gaba," cewar sanarwar kamfanin.

Ta ƙara da cewa shugaban kamfanin ya "kawo gagarumin sauyi kan harkar ƙananan bindigogi a duniya" kuma "ya yi nasarar kafa kamfanin Glock a matsayin jagora a kan harkar sarrafa ƙananan bindigogin hannu".

Glock, wanda aka haifa a 1929, ya karanci fannin injiniyanci a wata kwaleji da ke birnin Vienna. Daga bisani ya kafa harkar kasuwancin sarrafa kayayyaki a wani gari da ke wajen babban birnin Austria.

A farkon shekarun 1980, kamfanin ya shiga harkar samar da kayan aikin sojoji kuma ya karɓi wnai kira daga rundunar sojin Austria da ke neman sabunta bindigoginta na fistol.

Glock ya tsara sannan ya samu lasisin ƙera bindigar hannu maras nauyi wadda za a iya ɗura wa harsashi 18 kuma cikin sauƙi a sake yi mata ɗuri.

Bindigar ta samu ɗaukaka a tsakanin jami'an sojoji da 'yan sanda a faɗin duniya.

Paul Barrett, marubucin littafin: The Rise of America's Gun, ya rubuta cewa makamin ya zama "ƙaramar bindigar tashen zamani a wajen fararen hula: jagaba da ta zama abar misali a cikin tsara".

Mujallar Forbes ta yi ƙiyasin cewa dukiyar Glock ta kai dala biliyan ɗaya da miliyan 100 a shekarar 2021.

Bindigar Glock ta kuma samu shiga har a cikin harkar fina-finai da waƙoƙin zamani na Amurka. "Je, ka samu Glock, ka jefar da wannan 'yar ficiciyar fistol mai yarfen tagulla," jarumi Tommy Lee Jones ya faɗa a wani fim mai suna US Marshals cikin 1998.

Mawaƙan gambara ko raf na Amurka Snoop Dogg da Wu-Tang Clan su ma sun ambaci bindigar a wasu waƙoƙi.

Bindigar ta kuma bayyana a fitattun fina-finan Hollywood ciki har da Terminator 3: Rise of the Machines da The Matrix Reloaded.

A tsawon shekaru, masu fafutukar taƙaita mallakar bindiga sun yi ta sukar lamirin Glock saboda ɗaukaka bindigar da ya yi, wadda ta kasance cikin sauƙi ana iya ɓoye ta kuma za a iya ɗura mata harsasai masu yawa fiye da na makamantan bindigogi irinta.

An kuma yi ta taƙaddama a kanta. Lokacin da sojojin Amurka suka gano shugaban mulkin kama-karyan Iraƙi, Saddam Hussein da bindigar Glock a inda yake ɓoye cikin ƙarƙashin ƙasa a 2003.

A 2018, wani tsohon sojan ƙundumbalar Amurka da ake zargin yana da larurar ƙwaƙwalwa ya kashe mutum 12 a wani kantin shan barasa mai yawan hada-hada a California, cikinsu har da wani ɗan sanda.

Haka kuma, wani kamfanin haɗa bindiga na Amurka ya taɓa shan caccaka saboda ƙera wata bindigar fistol ɗin Glock, da ake iya harhaɗa ta, kuma tana kama da abin wasan yara na robobin Lego.

Glock bai cika mayar da martani ba ga sukar da masu fafutukar taƙaita mallakar bindiga suke yi masa. Kuma ya ƙi bin sahun kamfanonin ƙera makamai da suka sa hannu kan wata yarjejeniyar taƙaita mallakar bindiga ta ƙashin kai da gwamnatin Amurka a 2000.

Glock ya mutu ya bar matarsa da 'ya'ya guda uku mace ɗaya da maza biyu.