Hotuna: Manyan mutanen da suka jefa ƙuri'a a zaben Najeriya na 2023

Yayin da aka kammala kaɗa ƙuri'a a sassan Najeriya domin zaɓar sabon shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki, ga wasu hotunan fitattun mutane da suka kaɗa ƙuria'rsu a zaben.

Shugaba Buhari
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari tare da mai ɗakinsa a mazabarsa da ke Katsina inda ya jefa ƙuri'arsa
.

Asalin hoton, @ProfOsinbajo

Bayanan hoto, Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo yayin da yake jefa ƙuri'arsa a Ikenne da ke jihar Ogun.
.
Bayanan hoto, Tsohon Shugaban ƙasa Abdulsalam Abubakar yayin da ake tantance shi domin kada kuri'arsa a Minna da ke jihar Neja
.
Bayanan hoto, Nyesom Wike, Gwamnan jihar Rivers a yayin da ya isa mazaɓarsa domin jefa ƙuri'a
.
Bayanan hoto, Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi zaɓe a mazaɓarsa dake jihar Ogun
.
Bayanan hoto, Gwamnan Kaduna, Nasir ElRufai yayin da yake kan layi gabanin jefa ƙuri'arsa a jihar
.

Asalin hoton, @GEJonathan

Bayanan hoto, Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan yana jefa ƙuri'arsa
.
Bayanan hoto, Ɗan takarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu tare da mai ɗakinsa a lokacin da suka isa rumfar zabe domin a tantance su.
.

Asalin hoton, @PeterObi

Bayanan hoto, Ɗan takarar Shugaban ƙsa a inuwar Jam'iyyar Labour, Peter Obi dai-dai lokacin da yake kaɗa ƙuria a mazaɓarsa da ke jihar Anambra
.

Asalin hoton, @PeterObi

Bayanan hoto, Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar Labour, Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed yayin da ya isa mazabarsa a jihar Kaduna domin jefa ƙuri'a
.
Bayanan hoto, Dai-dai lokacin da ake tantance ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar hamayya ta PDP kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar gabanin ya jefa ƙuri'a a jihar Adamawa
.
Bayanan hoto, Shi ma ɗan takarar shugaban Najeriya a ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a yayin da yake kaɗa ƙuri'arsa a garin Madobi a jihar Kano.
.

Asalin hoton, Leadership.ng

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje lokacin da yake bin layi domin kaɗa ƙuri'a a mazaɓarsa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa