Me ya sa sauya sunan jami'a ke tayar da ƙura a Najeriya?

Asalin hoton, @Bayo Onanuga/X
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
- Lokacin karatu: Minti 4
A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauya sunan jami'ar Maiduguri zuwa Jami'ar Muhammad Buhari, wani abun da ya janyo mahawara a tsakanin ƴan jihar.
A wani taron majalisar ministocin ƙasar tare da iyalin marigayin ne gwamnatin tarayya ta sanar da amincewa da sauya sunan daɗaɗɗiyar jami'ar, wadda ke gab da cika shekara 50 da kafuwa zuwa Jami'ar Muhammadu Buhari.
Lamarin ya haifar da zazzafar muhawara, musamman a kafofin sada zumunta, inda wasu ƴan ƙasar suke cewa sauya sunan jami'ar, tamkar sauya tarihinta ne da kuma jefa malamanta cikin ruɗani.
To sai dai ma'aikatar ilimin Najeriya ta ce shugaban ƙasar ya sauya sunan jami'ar ne saboda jajircewa da ƙoƙarin da marigayin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi a ɓangaren ilimin ƙasar.
Ba wannan ba ne karon farko da ake rikita-rikita bayan sauya sunan jami'a a ƙasar, domin a baya an sha samun inda ake gudanar da zanga-zanga domin sauya sunan makaranta - kamar a Legas da Abuja.
Shin me ya sa sauya suna—wanda a wasu ƙasashe ke faruwa ba tare da wata hayaniya ba—ke jawo tirka-tirka a Najeriya? me hakan ke nufi? Wane irin tasirin hakan ke da shi ga tsarin ilimi?
Me sauya sunan ke nufi?
A game da mayar da Jami'ar Maiduguri zuwa Jami'ar Muhammadu Buhari, BBC ta tuntuɓi Dokta Aliyu Tilde, wanda tsohon malamin jami'a ne, kuma tsohon kwashinan ilimi a jihar Bauchi, ya ce mahaifiyar Buhari Babarbariya ce, sannan "ya yi gwamnan arewa maso gabas, sannan ya yi shugaban ƙasa. Ni ina ga ko da a Legas ne aka sa sunansa bai kamata a ce ba a so ba. Sai dai ka san shi ɗan'adam yana tafiya ne da ɗabi'a, bai cika son canji ba."
A game da yadda lamarin kan kawo sauye-sauye a jami'o'in, Tilde ya ce dama duk sabon abu yana zuwa da wani lamarin.
"A hankali za a saba. Ko ni ina kwamishina mun canja sunan Jami'ar Jihar Bauchi zuwa Sa'adu Zungur saboda mun ga irn gudunmuwar da ya bayar, sai muke ganin ya kamata a girmama shi kamar yadda aka girma sauran na baya."
Dr Kabiru Danladi Lawanti, malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya ce matakin "zai goge tarihin jami'ar a kundin tattara bayanai na jami'o'in duniya wato global database. Ka ga duk takardun da aka rubuta da bincike da aka saka a cibiyoyin bincike na duniya idan ka canja sunan jami'ar, baki ɗaya ka rusa wannan abu."
Karrama shugabannin baya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A game da dalilin da ya sa ake canja sunan da sunan shugabanni, Tilde ya ce akwai abubuwa da ake yi saboda "tarihi da martaba mutane da tabbatar da gudunmuwar da suka bayar wajen gina ƙasa. Wannan ya sa ake sanya sunayen waɗanda suka yi shugabanci a wurare irin su filin jirgi da asibitoci da makarantu."
Amma a nasa ɓangaren, Lawanti ya ce dama da sabuwar jami'a aka buɗe ne, aka sa sunan ɗansiyasa, "to babu wanda zai yi magana. Amma jami'a ta yi shekara 50 zuwa 100 ko sama da haka, ka zo ka sa mata sunan ɗansiyasa, gaskiya ba a yi wa wannan jami'ar adalci ba."
A game batun karrama tsofaffin shugabanni, malamin jami'ar ya ce kamata ya yi a riƙa karrama shugabannin a fannonin ci gaba da suka fi bayar da gudunmuwa.
"Misali a Borno, shi wanda ake magana (Buhari) soja ne da ya kai muƙamin janar. Akwai jami'ar sojoji ta Biu, ba zai zama laifi ba don an saka sunansa a wannan jami'ar saboda ya yi aikin soja, ya yi yaƙin basasa kuma mutum ne da aka yarda yana da gaskiya da amana."
Me ya sa ake samun taƙaddama?
Dokta Aliyu Tilde, ya ce taƙaddamar ba ta rasa nasaba da halayyar ɗan'adam.
Ya ce, "ni ina ganin yana cikin ɗabi'ar ɗan'adam, idan mutum ya saba da abu, har na tsawon shekara 50 kamar na Jami'ar Maiduguri da aka yi a baya-bayan nan, rana ɗaya idan ka zo ka sauya, gaskiya za a ji nauyi sosai."
Tilde ya ce ko a baya an taɓa yin yunƙurin sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa El-Kanemi, "kuma duk da babba ne a jihar, amma ba a amince ba, haka aka haƙura."
Ya ce a lokacin da yake koyarwa a jami'a, inda a cewarsa yana makarantar a 1984 aka mayar da ita Jami'ar Usman Danfodio daga Jami'ar Sokoto, lamarin da ya ce ya zo "banbaraƙwai."
A nasa ɓangare, Dokta Lawanti, ya ce a ra'ayinsa bai dace ba kwatsam a sauya sunan daɗaɗɗiyar jami'a mai tarihi, inda ya ƙara da cewa babu laifi idan sabuwar jami'a ce.
Ya ce muhawarar da ake samu na da alaƙa da siyasa, domin a cewarsa "abubuwan sun kasu kashi biyu.
"Akwai mutane da saboda siyasa idan an sa sunan wanda suke so, ba sa ganin abin a matsayin matsala, wasu kuma saboda ba sa son ɗansiyasar, sai ka ga suna magana."
Lawanti ya ƙara da cewa akwai buƙatar a cire son-rai, a duba abin da ke faruwa a duniya, "za mu ga cewa ba wata jami'a da da ake ƙirƙira ba tare da tarihin da ya sa aka ƙirƙire ta ba. Akwai Jami'ar Oxford da Cambridge. Oxford ta haura shekara 900 - an ƙirƙire ta a 1096- Cambridge kuma tana da kusan shekara 600, amma an bar su da sunayen garuruwansu saboda tarihin da ke da alaƙa na tarihin garin."
Ya ce ko a Najeriya, haka abin ya kamata domin a cewarsa Borno na da tarihi na kusan shekara 2000, "saboda haka sanya wa jami'a sunan garin, yana cikin abubuwan da ke mutunta tarihin al'ummar garin. Don haka ni a nawa ra'ayin, kuskure ne ka ɗauki jami'ar da ta yi kusan shekara 50 da sunan wani ɗansiyasa."
Jami'o'i da aka yi gumurzu bayan sauya musu suna
- Federal University, Oye Ekiti (FUOYE) zuwa Adeyinka Adebayo a Ekiti
- Jami'ar North West ta Kano zuwa Jami'ar Yusuf Maitama Sule
- Jami'ar Lagos (UNILAG) zuwa Jami'ar Moshood Abiola (MAULAG)
- Jami'ar kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya ta Akure (FUTA) zuwa Jami'ar Shehu Shagari.
- Jami'ar Abuja zuwa Jami'ar Yakubu Gowon.
Jami'o'in da aka sauya wa suna ba tare taƙaddama ba
- Jami'ar Ife zuwa Obafemi Awolowo University (OAU)
- Jami'ar gwamnatin tarayya ta koma zuwa Jami'ar noma ta Michael Okpara
- Jami'ar kimiyya da fasaha ta tarayya a Yola zuwa Modibbo Adama University of Technology (MAUTECH)
- Jami'ar gwamnatin tarayya ta Ndufu-Alike zuwa Jami'ar Alex Ekwueme.











