Yadda matan da ba su son haihuwa ke ƙara yawa a Kenya

Hoton Nelly Naisula Sironka tana murmushi sanye da dankunne

Asalin hoton, Nelly Naisula Sironka

Bayanan hoto, Nelly Naisula Sironka ta ce ba ta da damuwa kan matakin da ta ɗauka na mara wa al'adarsu baya
    • Marubuci, Danai Nesta Kupemba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Iyakar abin da Nelly Naisulka ta sani shi ne ba ta taɓa sha'awar samun ƴaƴa ba a rayuwarta, kuma matar, mai shekara 28 da haihuwa ta ɗauki wani mataki guda ɗaya wanda ba zai taɓa canzuwa ba, wanda zai sanya ba za ta taɓa ɗaukar ciki ba.

A watan Oktoban, ta ɗauki wani tsattsauran mataki na juyar da mahaifa, wanda ake kira 'tuba ligation' a turance, wato rufe mahaifa na har abada.

"Sai na ji tamkar an ƴanta ni ne" kamar yadda ta shaida wa BBC, tana mai cewa a yanzu makomarta na hannunta.

Tiyatar na hana ɗaukar ciki, ta hanyar rufe bututun magudanar ƙwayayen haihuwa, na mace.

A tsakanin 2020 da 2023, ƙiyasi ya nuna cewa an samu kimanin mata dubu 16 a ƙasashen da ke yankin gabashin Afirka, na zuwa a yi musu irin wannan tiyata, a cewar ma'aikatar Lafiya a Kenya.

Sai dai wani abu da har yanzu ba a iya tantancewa ba shi ne, ko nawa ne adadin matan da ba su taba haihuwa ba a cikin waɗanda aka yi wa tiyatar?

Sai dai Dakta Nelly Bosire ya ce irin waɗannan mata na kawo kansu don a rufe musu mahaifa domin su daina haihuwa, na sauyawa a Kenya.

"A al'adance, mafi akasarin wadanda ke zuwa don a rufe musu tmahaifar, su ne wadanda suka haifi yara fiye da ɗaya," kamar yadda ƙwararren likitan mata, ya shaida wa BBC.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Amma yanzu muna ganin ƙaruwar mata da ba su da yara na kawo kansu don a yi musu tiyatar"

An dai yi wa mata wannan aiki ne, ga matan da suke yaƙinin cewar ba sa son samun yara a gaba, domin sauya aikin na da matuƙar wahala.

"Likitoci ba su fiya bayar da shawarar a yi aikin rufe bututun magudanar ƙwayayen haihuwar ba", a cewar Dr Bosire

Duk da cewar ta futo daga babban gida, Ms Sironka ta ce ba ta taba kulawa da irin matsin lambar da ta fuskanta ba, na ganin ta fara haihuwa ba, kamar yadda yake a al'adar Kenya, inda ake da buri wajen ganin mace ta haihu ita ma ta sami 'ya'yanta.

Ta jinjina wa mahaifinta, kan yadda ya yi tsayuwar daka, wajen ganin ta mayar da hankalinta, kan ilimi, wanda hakan ya sa ta sanya soyayyar karatu a ranta.

Littattafai da masu rajin kare hakkin mata na Amurka, irinsu Toni Morrison, Angela Davis, da Bells Hooks, suka rubuta na daga cikin abubuwan da suka bude wa mata idanu.

"Ms Sironka wadda ita ce shugabar kungiyar masu tsattsauran ra'ayi kan 'yancin mata a Kenya ta ce "ta tattauna kan rayuwar mata da ba su taba haihuwa ba ko kadan" .

Kungiyar tana aiki ne don ganin ta kawo karshen cin zarafin mata.

"A nan ne na fuskanci cewar wannan wani abu ne da za a iya cimma".

Ta yi wasiwasin toshe bututun magudunar kwan haihuwa tsawon shekaru, amma ta yanke daukar mataki yin sa bayan da ta tara kudin da za a yi mata aikin, da samarwa kanta aiki mai albashi mai tsoka, da zai bata damar daukar hutu bayan an yi aiki.

Ta kashe shillin din kenya 30, 000 (£190; $230) a wani asibitin kudi.

Ms Sironka na tunanin cewar ana take hakkin mata a duniya baki daya, mussamman ganin yadda mata suka yi rashin nasara wajen ganin an sanya damar zubar da ciki a cikin kundin tsarin mulkin Amurka a 2022, hakan na daga cikin abubuwa da suka karfafa mata gwiwar daukar wannan mataki nata.

Hakan ya sa mata fargabar cewar yancin mace na hakkin kula da jikinta da kanta, ka iya fuskantar turnaki, a wasu wuraren, don hakan ta yanke a yi mata tiyatar rufe bututun magudanar kwan haihuwar.

"A Afirka da kasashe irinsu Amurka, an sami karuwa tsattsauran ra'ayi da mulkin yan kama karya, wani misali mai kyau da ke futowa da irin mulkin da ake fuskanta a Kenya", tana mai muhawara.

Lokacin da ta sanar da danginta, abin bai zo musu da mamaki ba, domin yadda ta yi fice wajen bayyana aniyarta na zama ba tare da haihuwa a rayuwa ba.

Yaya batun Soyayya?

"Ina nan ina ta tunani akai," ta fada tana mai daga kafadu.

Ba wai iya Ms Sironka ce kadai ba ce ta zabi irin wannan salon rayuwa ba, inda take kalubalantar yadda rayuwar mata kamar yadda al'ada ta tsarawa matan take tafiya.

Hoton yar YouTuber Muthoni Gitau da adon kwaron malam buda mana littafi da ta yi adon gashin ta.

Asalin hoton, Muthoni Gitau

Bayanan hoto, Muthoni Gitau 'Yar Youtube a Kenya, ta sanar da dubban mabiyanta cewar ta yanke shawarar a daure mata bututun

A kafafen sada zumunta akwai wadanda ke futowa fili suna bayyana ra'ayinsu kan juyar da mahaifa, saboda ba sa son haihuwa.

A cikinsu akwai Muthoni Gitau, wata mai aikin kawata wuri, kuma mai shirin podcast.

Ta ce ta bayar da labarin juya mahaifarta, tsawon minti 30, a shafin sada zumunta na You Tube a watan Maris din bara, tana mai yin bayani kan matakan da aka bi wajen yin aikin.

" Lokaci na farko da na ji a raina cewar ba na son haihuwa, shi ne ban fi shekara 10 ba," tana mai shaida wa BBC.

Mahaifiyarta na ɗauke da juna biyu a lokacin, ana kuma ta yi mata tambayoyi kan yadda gobenta za ta kasance.

"Na ga wadanda za su iya zama abokan rayuwata. Kawai dai ni ban ga yiwuwar zan taba haihuwa ba har na sami 'ya'ya ba, a cewarta.

Kamar dai Ms Sironka, matsayar Ms Gitau ta yi tsayin daka kan matsayar tata ne, saboda matsayar da ta daukarwa kanta, da ya tafi daidai da ra'ayinta.

Bayan siyen maganin hana daukar ciki, wanda ta ce yana sa ta cikin mawuyacin hali, daga nan ta yanke matakin daukar matakin na dundundun.

A lokacin farko da ta tunkari likita, kan batun juya mahaifar, tana da shekaru 23, amma ta ce ta fuskanci turjiya.

An yi ta fada mata maganganu tamkar wadda ake yi wa huduba, kan yadda yara suka kasance albarka ne daga wajen ubangiji. Ya tambaye ni, 'Idan kuma na hadu da wanda shi ba ya son yara fa?'" ta tambaya.

Likitan na da bayanai daban-daban ga dukkan wanda ya hadu da shi, da ke da irin wannan tunani, maimakon ainihin mara lafiyar da ke zaune a gabansa, a cewar ta.

Ms Gitau ta ce korar hakan tamkar wani mataki ne, na "karya zuciya". Wasu karin gwammon shekaru ne kafin daga bisani fatan ta ya cika.

Dr Bosire, ta nanta irin babban kalubalen da ake fuskanta a Kenya, na fuskantar sauyi a bangaren lafiya, da ke sauya musu tunani, tare da girmama ra'ayin mara lafiya, wajen daukar mataki kan lafiyarsa.

"Wannan alaka chakuda ta da al'adarmu, inda mutane ke da yakinin cewar ba dai-dai ba ne mace ta je a juya mata mahaifa, a cewarta.

Wani likitan mata a Kenya, Dr Kireki Omanwa, ya amince cewar, lamarin na da alaka da mahawarar da ake ta yi a tsakanin likitoci.

"Har yanzu ba a iya kammala mahawarar ba", yana mai shaida wa BBC.

Amma Ms Gitau ba ta karaya ba duk da cewar a shekarar da ta gabata, a lokacin da ta je ganin wani likita, a karon farko a ofishin wata kungiya mai zaman kanta, wadda ke koyar da ƙayyade iyali.

Ta ƙudurce wasu bayanai da ta rike a matsayin hujojin da za su tallafa wa matsayar tata, da ya sa take jin ba gudu ba ja da baya: "likitan na da kirki."

Har yanzu ba ta yi aure ba, tana zaune cikin farin ciki, da wannan matsayar tata, wanda take jin cewar zai bata damar tafi da rayuwarta yadda ta so.

Yar shekara 34 na kuma farin ciki da irin martanin da bidiyon da ta yi ya samu, kuma yana nuni da cewar babu masu sukar ra'ayinta.

Ta ce mutane masu yawa da ke kafafen sada zumunta, sun yi ta yaba mata, kuma suna yi mata kallo a matsayin wadda ke kara samun kwarin gwiwa.

"Mata za su iya bayar da tasu gudunmawar, a duniya ta hanyoyi masu yawa," a cewarta.

"Ba wai sai an bi hanyoyin da ake bi ba wajen, rainon dan'adam. Ina farin cikin kasancewa a cikin ƙarnin da ake mutunta ra'ayin mutane."