Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane laifi Sheikh Hasina ta aikata har aka yanke mata hukuncin kisa?
- Marubuci, Anbarasan Ethirajan and Tessa Wong
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Wata kotu a ƙasar Bangladesh ta yanke wa tsohuwar Firaiministar ƙasar Sheikh Hasina hukuncin kisa sanadiyyar murƙushe zanga-zangar adawa da gwamnatinta a shekarar da ta gabata.
Hasina, wadda aka same ta da laifi a tuhume-tuhumen take hakkin bil'adama, an yi mata shari'a ne yayin da take ci gaba da gudun hijira a Indiya, inda ta tsere tun bayan tuntsurar da gwamnatinta.
Wata kotu ta musamman da aka kafa ta gano cewa Hasina ce ta umarci a murƙushe masu zanga-zangar - wadda ɗalibai suka jagoranta - inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa an kashe kimanin mutum 1,400 a lokacin, kuma harsasan jami'an tsaro ne suka kashe akasarinsu.
Hasina ta musanta duk zarge-zargen da aka yi mata.
"Kotun je-ka na yi-ka ce wadda abokan hamayyar siyasata ke jagora, kuma suka yanke hukuncin da suka tsara...domin kawar da hankalin duniya daga ruɗani da rashin ƙwarewar (sabuwar) gwamnati," kamar yadda ta shaida wa BBC a ranar Juma'a 14 ga watan Nuwamban 2025.
Wannan hukunci da kotun ta yanke wani babban ƙalubale ne ga hulɗar diflomasiyyar Indiya da Bangladesh.
Bangaladesh ta buƙaci a miƙa mata toshuwar Firaiministar, sai dai Indiya ba ta nuna wata aniyar yin hakan ba.
An ƙara matakan tsaro a fadin ƙasar Bangladesh kan fargabar tashin hankali, inda aka samu ɓallewar zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar.
Mai rajin kare dimokuraɗiyya
Sheikh Hasina ita ce Firaiminsta mafi daɗewa a tarihin Bangladesh, inda ta yi mulki tsawon shekara 20.
Hasina, wadda ake yaba mata a matsayin wadda ta bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar, ta shiga siyasa ne a matsayin ƴar rajin kare dimokuradiyya.
Sai dai a shekarun baya-bayan nan an zarge ta da zama ƴar kama-karya, inda take gallaza wa abokan hamayyarta.
Umarnin yin 'amfani da muggan makamai'
A watan Janairun 2024, Hasina ta samu gagarumar rinjaye domin ci gaba da wa'adin mulki na huɗu a matsayin Firaiminista, inda mutane da dama suka soki zaɓen tare da bayyana shi a matsayin dodo-rido, sannan ƴan hamayya da dama suka ƙaurace.
Daga baya a shekarar sai zanga-zanga ta ɓarke, inda al'umma suka buƙaci a yi watsi da tsarin kasafta muƙamai da ayyukan gwamnati.
Daga baya zanga-zangar ta rikiɗe zuwa ta adawa da manufofin gwamnati bayan da gwamnatin ta riƙa amfani da sojoji wajen murƙushe zanga-zangar, ƙarfi da yaji.
Yayin da aka ci gaba da kiraye-kirayen saukar ta daga mulki, Hasina ta yi kunnen-uwar-shegu, tare da bayyana masu kiraye-kirayen a matsayin "ƴan ta'adda". Haka nan ta sanya an jefa mutane da dama a gidan yari, sannan aka gurfanar da ɗaruruwansu a gaban kotu.
Wani sauti da aka naɗa ya nuna cewa ita ce ta umarci jami'an tsaro su yi "amfani da miyagun makamai" a kan masu zanga-zanga. Sai dai ta musanta bayar da umarnin a yi amfani da bindiga kan fararen hula masu zanga-zanga.
Wasu daga cikin lokuta da abubuwa suka ƙazance sun haɗa da abin da ya faru ranar 5 ga watan Agusta, ranar da Hasina ta fice daga ƙasar a cikin jirgin helikwafta jim kaɗan kafin dandazon mutane su dirar wa gidanta a birnin Dhaka.
Ƴansanda sun kashe aƙalla mutum 52 a ranar, a wata unguwa mai yawan al'umma, hakan shiga tarihi a matsayin mafi muni cikin lokutan da ƴansanda suka fi nuna karfi kan fararen hula a ƙasar.
Haka nan an tuhumi Hasina da laifukan take hakkin bil'adama wanda ya shafi ɓatar da mutane a birnin Dhaka.
Bugu da ƙari Hasina da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatinta na fuskantar shari'a kan zarge-zargen rashawa a wata kotu ta daban, sai dai sun musanta.
Laifukan da ake zargin Hasina da tafkawa
An daɗe ana zargin cewa Hasina na amfani da ƙarfi wajen murƙushe abokan hamayyarta da ma kafafen yaɗa labarai, wani abu da ake wa Kallon abin mamaki ganin yadda ta faro a matsayin ƴar rajin kare dimokuraɗiyya.
Ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi ƙiyasin cewa an ɓatar da mutane aƙalla 700, wasu ɗaruruwa kuma aka yi musu kisan gilla, tun bayan fara mulkinta a shekarar 2009. Hasina ta musanta cewa akwai hannunta a ciki.
Haka nan an zargi dakarun sojin Bangladesh da munanan take hakkin bila'adama. A shekarar 2021, Amurka ta ƙaƙaba takunkumi kan rundunar ƴansanda ta Rapid Action Battalion – wani ɓangare na rundunar ƴansandan ƙasar da ya yi ƙaurin suna wajen kashe-kashen gilla.
Masu rajin kare hakkin bil'adama da ƴan jarida sun riƙa fuskantar tsangawa da kame da bibya da kuma cin zarfai.
Bugu da ƙari an zargi gwamnatin Hasina da ''tsangwamar ta hanyar shari'a'' inda ake gurfanar da mutane a gaban kotu, ciki har da mutumin da ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, Muhammad Yunus – wanda ya shugabanci ƙasar bayan tuntsurar da Hasina.
An taɓa ɗaure shi a shekarar 2024 inda aka tuhume shi da laifuka sama da 100, a wata shari'a da magoya bayansa suka ce bi ta da ƙullin siyasa ne.
Gwamnatin Hasina ta musanta zarge-zargen.