Farashin masara da shinkafa ya fara sauka a kasuwannin arewacin Najeriya

Kayan abinci

Asalin hoton, EPA

Lokacin karatu: Minti 3

An fara samun saukin farashin wasu daga cikin kayan amfanin gona da suka soma shiga kasuwanni a yankin arewacin Najeriya.

Farashin kayan abinci da suka hada da masara da shinkafa 'yar gida ya fara sauka.

Hakan dai na zuwa ne a yayin da ake fama da hauhawar farashin kayan abinci a Najeriyar.

Manoma kamar Alhaji Shu'aibu Sulaiman, da ke garin Dandume na jihar Katsina, ya danganta saukar farashin masara da shinkafar da fara girbinsu da aka soma a wurare da dama a yankin arewacin Najeryar.

Cikin wata hira da BBC, manomin ya ce, a bana Allah ya albarkaci amfani gona tun da ga shi har wasu kayan amfanin gonar kamar masara da shinkafa sun fara isa kasuwanni.

Ya ce, "Yanzu abin da ake jira a girbe a kai kasuwa s une Dawa da Waken Suya."

Alhaji Shu'aibu Sulaiman, ya ce "Yanzu ma somin tabi ne na zuwan masara kasuwa, kuma sakamakon fara kai ta kasuwa ma har farashin ya sauka domin a yanzu ana sayar da buhun sabuwar masara a kan kudi naira dubu 60 ko 58 kai wani lokaci ma har akan samu buhu a kan naira dubu 55, akasin a baya da ake sayar da tsohuwar masara a kan buhu naira dubu 90 zuwa 95."

Manomin ya ce, a kan samu buhun tsohuwar masara a yanzu a naira dubu 80 ko dubu 79.

Shinkafa da Masara
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce, "A bangaren shinkafa 'yar gida kuwa a yanzu ta fi shigowa kasuwa ma sosai hakan ya sa farashinta ya yi kasa, don ana siyan buhun sabuwar shinkafa mai nauyin kilo 100 kuma tsaba a kan naira dubu 135 zuwa dubu 140, tsohuwa kuwa ana sayar da buhunta mai nauyin kilo 100 a kan farashin naira dubu 155 zuwa dubu 160."

Alh. Shu'aibu Sulaiman, ya ce a baya har naira dubu 170 zuwa 180 an sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilo 100.

"A duk shekara idan amfanin gona ya fara shiga kasuwa farashi na sauka, kuma a bana muna ganin alamar kayan zai kara sauka domin a yanzu haka a cikin manoma kashi 100, kashi 30 ne kayansu ya nuna har suka fara kai wa kasuwa, to akwai na kashi 70 da basu ma fara kai wa kasuwa ba, don haka idan nasu ya nuna suka kai kasuwa kayan abincin zai yawaita a kasuwanni kuma dole farashi ya kara sauka."

Saukar farashin kayayyakin abincin na zuwa ne a dai-dai loakcin da hukumar kididdiga ta Najeriya NBC ta fitar da wani rahoton da ke cewa tattalin arzikin kasar ya karu zuwa naira tiriliyan 6.95 a rubu'in wannan shekara ta 2024.

Rahoton ya ce bunkasar tattalin arziki ya karu ne sakamakon kayan da Najeriya ke fitarwa zuwa kasashen ketare, wanda ya zarta shekarar bara na naira tiriliyan 6.52.

Masana tattalin arziki dai na ganin akwai bukatar kasar ta mayar da hankali wajen samarwa naira tagomashi a kan dala, da fito da hanyoyin da za su sassauta matsin rayuwa da ake fuskanta sakamakon karin kudin mai da na makamashin lantarki da sauran su da gwamnatin ta yi.