Rodrygo na son barin Madrid, Man Utd na harin Baleba

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaba na Brazil Rodrygo, mai shekara 24, na son barin Real Madrid yayin da Arsenal da Manchester City da Liverpool ke son ɗanwasan. (AS - in Spanish)
Manchester United na diba yiyuwar ɗauko ɗanwasan Brighton Carlos Baleba, mai shekara 21, amma ga alama za ta jinkirta kan ɗanwasan na tsakiya na Kamaru har zuwa bazara. (Sky Sports)
West Ham na tattaunawa kan ɗanwasan gaba na Lazio da Argentina Taty Castellanos, mai shekara 27 kan fam miliyan 25. (Mail)
Liverpool da Manchester United da Newcastle na sa ido kan ɗanwasan Watford da Morocco Othmane Maamma, mai shekara 20. (Teamtalk)
Juventus na tuntuɓi West Ham kan ɗanwasan tsakiya ɗan Argentina Guido Rodriguez, mai shekara 31. (La Corriere dello Sport - in Italian)
Crystal Palace da Leeds da Nottingham Forest na ribibin ɗanwasan tsakiya na Newcastle mai shekara 26 Joe Willock na Ingila. (i paper - subscription required)
Newcastle na shirin ɗauko ɗanwasan baya na Dayann Methalie, mai shekara 19, wanda ya fara haskawa a babbar gasa a Toulouse a 2025. (Sun)
Eintracht Frankfurt na da ƙwarin guiwar ɗauko ɗanwasan gaba na Faransa Arnaud Kalimuendo, mai shekara 23, a matsayin aro daga Nottingham Forest. (Athletic - subscription required)
Fulham na fuskantar hamayya kan burinta na ɗauko ɗan ƙasar Amurka Ricardo Pepi, 22 daga PSV. (Teamtalk)
Chelsea na diba yiyuwar ɗauko ɗanwasan tsakiya na Aston Villa da Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, da kuma ɗanwasan gaba na Arsenal da Ingila Ethan Nwaneri. (CaughtOffside)










