BBC ta gano kurakuran rundunar sojin Isra'ila

    • Marubuci, Stephanie Hegarty & Ahmed Nour
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Gargadin kwashe mutanen da Isra'ila ta yi wa mutanen Gaza gabanin kai hare-hare na kunshe da kurakurai da dama, kamar yadda wani bincike na BBC ya nuna.

Gargadin ya ƙunshi bayanai masu cin karo da juna, suna da ruɗani kuma wasu lokuta ma an bai wa gundumomi sunayen da ba nasu ba.

Masana sun ce irin wannan kurakurai na iya saɓa wa wajibcin da Isra'ila ta rataya a wuyan ƙasashen duniya.

Dakarun tsaron Isra'ila (IDF) sun yi watsi da duk wani iƙirari da ke cewa gargaɗin na da ruɗani ko cin karo da juna.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce gargadin da BBC ta yi nazari a kai, wani ɓangare ne kawai na "kokarin da take yi na karfafa kwashe fararen hula ba tare da wata matsala ba".

Dokar jin ƙai ta ƙasashen duniya ta buƙaci dakarun da ke kai hare-hare su ba da gargadin kafin su kai hare-haren da ka iya shafar fararen hula, sai dai kuma idan an samu cikas sakamakon yanayi.

Isra'ila ta ce tsarin gargadin nata an yi shi ne domin taimaka wa fararen hula su gujewa wani hadari da zai kai ga mutawa ko samun rauni yayin da take ci gaba da yaƙin da take yi da Hamas.

Tsarin ya karkasa taswirar birnin Gaza zuwa gida-gida da suka yi wa lamba, tsari ne da mutanen Gaza ba su taɓa amfani da shi a baya ba.

Isra'ila ta samar da taswirar gidajen ta intanet da zai bai wa ƴan Gazar damar gano gidajensu inda ya kamata su fice da kuma lokacin da aka bayar da gargadin ficewa.

Ga wani sakon IDF da ta wallafa a ƙarshen Janairu a shafin sada zumunta na X tare da wani madubin adireshi domin fahimtar taswirar birnin Gaza da aka karkasa zuwa gida-gida da suka yi wa lamba

BBC ta zanta da shaidu

Amma mutanen da muka zanta da su sun bayyana irin ƙalubalen da suke fuskanta wajen samun taswirar da suka saka a shafin intanet, da wahalar fahimtar taswirar da kuma gano kurakurai.

BBC ta yi nazari kan kafofi na sada zumunta na IDF na harshen Larabci a Facebook da X da Telegram, inda muka samu daruruwan sakonni dauke da gargadi.

An yi ta buga wannan gargaɗin akai-akai inda wani lokaci tare da ƴan sauye-sauye a cikin kwanaki a jere ko kuma a ranaku daban-daban akan shafuka daban-daban.

Mun kuma nemo bayanan gargadin da aka dauka kuma aka wallafa su ta intanet.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta rabar da irin wadannan takardu na gargaɗi har miliyan 16 a Gaza.

Mun fi mayar da hankalinmu wajen bincikenmu kan gargaɗin da aka bayar tun daga ranar 1 ga Disamba, wanda shi ne lokacin da IDF ta ƙaddamar da tsarin da ya karkasa taswirar birnin Gaza zuwa gida-gida da suka yi wa lambama a matsayin hanyar samar da cikakken umarni fiye da baya, bayan fuskantar matsin lamba na kasashen duniya.

Mun samu sakonnin gargadin IDF da takardun gargadin guda 26 amma mafi rinjaye sun yi nuni ga tsarin da ya karkasa taswirar birnin Gaza zuwa gida-gida da aka yi wa lamba

A takardun gargaɗi da ke kan intanet, IDF ta shaida wa BBC cewa ta yi gargaɗin kai hare-hare ta hanyar tura sakwannin ta wayar hannu.

Da yake da wahala a iya samun cikakkun rahotanni a Gaza tare kuma da lalacewar hanyar sadarwar wayar, BBC ta kasa tattara shaidu kan saƙonnin gargadin da aka tura ta sakon wayar hannu da kuma kiraye-kirayen waya.

Gargaɗi daban-daban guda 26 da muka samu sun ƙunshi takamaiman bayanai daga IDF waɗanda mutane za su iya amfani da su don tserewa daga wuraren hatsari.

Amma 17 daga cikinsu kuma suna ɗauke da kurakurai. Waɗannan kurakuran sun haɗa da:

  • Akwai gargadi 12 inda aka ambaci gidaje ko unguwanni a cikin rubutun da aka wallafa a shafukan sada zumunta amma ba a nuna a taswira ba.
  • Gargadi tara sun ba da haske a kan wurare a taswirar amma ba a ambace su a cikin rubutun da aka wallafa ba.
  • Gargaɗi 10 suna da yankunan da za a yi ƙaura a taswirar waɗanda suka raba zuwa gundumomi, amma taswirar ba ta fayyace iyakar ba.
  • Gargadi bakwai suna da kibau akan taswirar da ake nufi da nuna wuraren da babu hadaari, amma suka nuna wuraren da ake kwashe mutane a maimakon haka.

Bugu da ƙari, wani gargaɗin ya lissafa unguwannin da ke cikin gundumomi da ba daidai ba, wani kuma ya haɗa gidajen da aka wa lambobi na unguwanni biyu kuma na uku ya nuna gidajen da aka lissafo a saƙonni a gefen da bai dace ba na Gaza idan aka kwatanta a taswirar.

Lokacin da aka tambaye rundunar sojin Isra'ila game da waɗannan kurakuran, IDF ba ta magance batutuwan da taswirar ba amma ta nace cewa rubutun da aka wallafa a shafukan sada zumunta kan gargaɗin na da sahihanci kuma ya isa sosai.

Har ila yau, ya ce lokacin da aka yi amfani da kibau don kai mutanen Gaza zuwa ga wuraren da ke da tsaro, "a bayyane yake cewa kibau din sun yi nuni zuwa ga wata hanya ta gaba ɗaya" kuma ta nanata cewa an ba da mahimman bayanai a cikin rubutun da aka wallafa.

Wadannan kurakurai na iya karya wajabcin Isra'ila a karkashin dokokin ƙasashen duniya na samar da "gargadin ci gaba na ficewa mai inganci", in ji Janina Dill, babbar darektar Cibiyar Da'a ta Oxford, Doka da Rikicin Makamai.

Idan akasarin gargadin sun kunshi kurakurai ko kuma fararen hula ba su fahimce su ba a lokacin, to, "wadannan gargadin ba su cika aikin da ya dace ba kamar yadda yake a tanadin dokar jin kai ta kasashen duniya". In ji ta.

Wannan kurakuran sun gurgunta aikinsu, in ji Kubo Macak, farfesa a fannin dokokin kasashen duniya a Jami'ar Exeter, wanda shi ne "bai wa fararen hula damar kare kansu"..

'Taƙaddama'

A watan Disamba, Saleh, wani dan kasuwa daga birnin Gaza, wanda ke neman mafaka tare da 'ya'yansa da surukansa a Nuseirat da ke tsakiyar Gaza ya ce, babu wutar lantarki ko siginar waya da kuma katsewar intanet na tsawon lokaci.

Ya ce ya ga an kashe mutane tare da yadda wasu ke guduwa daga wata makaranta da ke kusa yayin da ake ta harbin bindiga, amma ya ce bai samu wani bayani game da gargadin ficewa daga rundunar tsaron Isra'ila ba.

A ƙarshe, ya sami wani dan katin SIM na waya wanda ya ba shi damar shiga shafukan bayanai a Masar da Isra'ila kuma ya ci karo da gargadin kwashe mutane a shafin Facebook na gwamnatin Isra'ila.

"An ba da umarnin ficewa daga ƙauyuka da yawa - [amma] ba mu san ko wane yanki ne muke zaune ba. Wannan ya haifar da babbar muhawara," in ji Salah.

Salah na iya shiga shafin intanet ne na ɗan karamin lokaci, amma ya aika sako ga matarsa ​​Amani, wadda ke Burtaniya tun kafin yaƙin.

Ta sami damar shiga shafin intanet ɗin da aka saka taswirar gargaɗin inda a nan ne ta gane inda mijinta yake.

Amma daga baya, duba da takamaiman gargadi na ficewa da aka yi a Facebook, ma'auratan sun fahimci lambar gidan da Salah ya yake, inda ya nuna yankin gida biyu - wanda ya kara ruɗa iyalan.

Daga karshe Salah ya yanke shawarar tafiya da yaran. Amma wasu daga cikin danginsa sun tsaya a wurin inda har fada ya kara tsananta.

Lokacin da BBC ta yi nazari kan gargadin ficewa da ke kan Facebook da Salah ya yi ta kokarin ganowa, mun sami karin rudani.

A cikin rubutu, sakon ya bukaci mutane su bar gidaje masu lambar 2220 da 2221 da 2222 da 2223 da 2224 da kuma 2225 - duk gidajen kenan da suka bayyana a cikin babban taswirar da ke kan intanet na IDF.

Amma a cikin taswirar da ke biye, an karkatar da gidajen guda shida masu lamba guda ɗaya, kuma an yi kuskuren ɗaukan su a matsayin gida mai lamba 2220.

Duk da wadannan sabani, a watan Janairu, Isra'ila ta gabatar da tsarin gargadin ficewa a kotun ƙasashen duniya a matsayin wani bangare na kariya daga zargin da Afirka ta Kudu ta yi mata na aikata kisan kiyashi.

Lauyoyin Isra’ila sun yi zargin cewa, tana yin iyakacin kokarinta wajen kare fararen hula, kuma ta samar da cikakken taswira ta yadda za a iya kwashe fararen hula na wani dan lokaci, maimakon kwashe daukacin mutanen yankunan.

Sun gabatar da gargadin ficewa da suka wallafa a kafafen sada zumunta guda daya a gaban kotu a matsayin shaida - amma BBC ta gano kurakurai biyu a ciki.

An jera gidaje masu lamba 55 da 99 a cikin rubutun da aka wallafa daga 13 ga Disamba amma ba a sanya su a cikin taswirar ba.

Abin da muke nufi - IDF

IDF ta shaida wa BBC cewa idan aka ambaci lambar gida a cikin rubutun da aka wallafa, gargadin ya fito fili, ko da a ce ba ya cikin taswirar.

Lauyoyin Isra'ila sun kuma yi ikirarin cewa, IDF ta shafinta na X tana ba da bayanai kan wuraren mafaka da ke kusa da wuraren da aka kwashe mutanen.

Amma a cikin dukkanin rubuce-rubucen gargadin da takardun gargadin da muka yi nazari a kai, ba mu ga wani gargadi da ke ba da suna ko ainihin wuraren mafaka ba.

Binciken BBC ya kuma gano an yi amfani da tsarin karkasa gidajen Gaza da IDF ta yi ba daidai ba. Tara daga cikin gargaɗin 26 sun jera haɗakar lambobin gidaje da sunayen unguwanni.

Wasu tara kuma ba su ambaci lambobin gidaje ba kwata-kwata.

Duk da cewa za a iya shiga zuwa babbar taswirar, amma sai suka lissafa unguwanni kawai.

BBC ta kasa samun hanyar tantance ainihin gidajen waɗannan unguwannin.

Iyalan Abdu, wadanda suka hada da mutane 32, sun kuma tsere daga birnin Gaza zuwa tsakiyar Gaza a farkon yakin. Sannan, a cikin watan Disamba, sun sami takardar gargadi da aka wurga daga jirgin sama.

Saƙonni a dandalin WhatsApp na iyali, waɗanda BBC ta gani, ya nuna ruɗanin da iyalai suka shiga yayin da suke taƙaddamar kwanaki biyu kan abin da takardar gargadin ke nufi.

Ya ƙunshi jerin unguwannin da za a iya yin ƙaura, amma dangin ba su iya gano yawancin wuraren ba.

Gargadin ya bukaci mutane da su fice daga "sansanin Al-Bureij da kuma unguwannin Badr, da gabar tekun Arewa, da al-Nuzha, da al-Zahra, da al-Buraq, da al-Rawda, da al-Safa a yankunan kudancin Wadi Gaza."

Mun gano al-Zahra da Badar na kusa, amma suna arewacin gaɓar kogin Wadi Gaza.

Amma ba mu iya samun unguwannin al-Rawda ko al-Nuzha a cikin "yankunan kudu da Wadi Gaza" ba.

Iyalan Abdu sun sha fama wajen yanke shawarar abin da za su yi. Shin ko su tsaya a cikin mummunan yaƙin da ke faruwa - ko kuma su fice duk da cewa ba su fahimci gargadin ficewar ba?

Wasu sun bi gargadin ficewar zuwa "matsuguni a Deir al-Balah". Amma da suka isa sai suka ji ba lafiya inda suka yanke shawarar komawa. Idan za su mutu toh sai su mutu tare, suka ce mana.

Bayanan tauraron dan adam game da lalacewar da Gaza ta yi sakamakon yaƙin wanda Jami'ar Jihar Oregon da Corey Scher na Jami'ar City New York suka yi nazari - ya nuna cewa yankin Deir al-Balah da iyalan suka koma neman mafaka ya fuskanci mummunan hari a cikin wannan lokaci fiye da yankin da suka bari.

IDF ta ce ta bincika "bayanai game da kasancewar fararen hula da ficewar da suka yi sakamakon wadannan gargadin" kuma ba su kasance masu ruɗani ko saɓani ba.

IDF ta ce gargadin ya ceci rayukan fararen hula marasa adadi a Zirin Gaza.