Ballon d'Or 2022/23: Messi da Haaland na cikin 'yan takara 30

Mujallar Faransa ta fitar da sunan 'yan wasa 30 da ke takarar gwarzon dan kwallon kafa, wato Ballon d'Or na duniya na 2022/23.

Cikin 'yan wasan har da Lionel Messi da Erling Haaland, waɗanda ake hasashen wani daga ciki ka iya lashe kyautar.

Wasu 'yan wasan da suka taka rawar gani da ake ganin za su iya lashe kyautar sun hada da Vinicius da Rodri ko kuma Kevin de Bruyne.

Tsohon dan wasan Real Madrid, wanda ya koma taka leda a babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia, Karim Benzema, shi ne gwarzon Ballon d'Or na bara.

Wannan karon za a auna ƙwazon ɗan wasa a kakar 2022/23, ke nan daga fara kakar a watan Agusta zuwa Yuli da aka kammala.

Saboda haka za a yi la'akari da gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022, wanda hakan zai bai wa Messi damar lashe Ballon d'Or na takwas jimilla ke nan.

Sai dai duk da haka Haaland yana da damar lashe kyautar, bayan kwallayen da ya ci a kakar da ta wuce da daukar Premier League da FA Cup da kuma Champions League.

Messi, kyaftin din Argentina, wanda yanzu ke taka leda a Inter Miami ya ci ƙwallo bakwai da bayar da uku aka zura a raga daga 15 da Argentina ta zura a raga ta lashe kofin duniya a Qatar.

Dama dai shi ne kaɗai kofin da tsohon ɗan wasan na Barcelona da Paris St Germain bai dauka ba a baya, yanzu ya hada dukkan wani babban kofi a fannin tamaula a duniya.

Messi bai yi ƙwazo ba sosai a PSG, amma ya taka rawar gani a 2021, wanda bai dauki Champions League ba, amma ya lashe Ligue 1 a kungiyar.

Shi kuwa Haaland, wanda ya fara kakar farko a bara a Premier League tare da Pep Guardiola ya ci kwallaye da yawa da lashe Premier da FA Cup da kuma Champions League.

Haaland ya zama kan gaba a cin kwallaye da yawa a Premier League da lashe takalmin zinare da zama fitatcen dan kwallo a Turai a bara.

A kakar da ta wuce Haaland ya zura kwallo 52 a raga a karawa 53 a dukkan fafatawa, wanda yanzu ya ci kwallo shida a wasa hudu a Premier League.

Ƴan wasa 30 da ke takarar Ballon d'Or na 2022/23:

  • Karim Benzema
  • Josko Gvardiol
  • Jamal Musiala
  • Andre Onana
  • Mohamed Salah
  • Bukayo Saka
  • Kevin de Bruyne
  • Jude Bellingham
  • Kolo Muani
  • Bernardo Silva
  • Khvicha Kvaratskhelia
  • Nicolo Barella
  • Emiliano Martinez
  • Ruben Dias
  • Erling Haaland
  • Martin Odegaard
  • Ilkay Gundogan
  • Yassine Bounou
  • Julian Alvarez
  • Vinicius Junior
  • Leo Messi
  • Rodri
  • Lautaro Martínez
  • Antoine Griezmann
  • Robert Lewandowski
  • Kim Min-jae
  • Luka Modric
  • Kylian Mbappe
  • Victor Osimhem
  • Harry Kane