Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ballon d'Or: Lionel Messi ya lashe kyautar karo na bakwai a tarihi
Ranar Litinin aka bayyana Lionel Messi a matakin wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana.
Hakan kenan ya zama kyaftin din Argentina mai taka leda a Paris St Germain ya lashe kyautar karo na bakwai jumulla.
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun lashe kyautar sau 12 tsakaninsu daga cikin 13 da suka fafata, inda Luka Modric ya ratso ya ci kyautar.
Messi ya ƙara tazara a yawan cin Ballon d'Or tsakaninsa da abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo, wanda ya lashe sau biyar.
Messi da Ronaldo sun fara takarar karabar kyautar Ballon d'Or tun daga 2008, bayan da Kaka ya ci kyautar 2007 a lokacin da yake taka leda a Real Madrid.
Daga nan ne Ronaldo ya lashe Ballon d'Or na farko a Manchester United a 2008.
Shi kuwa Messi ya karbi kyautar daga hannun Ronaldo a 2009, wanda ya lashe karo hudu a jere har zuwa 2012.
Daga nan kuma kyautar ta koma wajen Ronaldo da ya lashe biyu a jere a 2013 da kuma 2014, sai Messi ya sake karba a 2015.
Daga nan Ronaldo ya lashe biyu a jere a 2016 da kuma a 2017, sai a karon farko da Luka Modric ya zama gwarzon shekara na 2018, kuma kyautar da aka ci ba tsakanin Messi ko Ronaldo ba.
Kyaftin din Argentina shine ya ci kyautar 2019, sannan ba a gudanar da gasar 2020, saboda gudun yada cutar korona.
A ranar Litinin ne Messi ya kara lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2021 na bakwai jumulla, kuma a karon farko ba a Barcelona ba.
Messi ya koma taka leda a Paris St Germain a bana, bayan da Barcelona ta kasa biyansa albashi, saboda matsin tattalin arziki da ta fada sakamakon bullar cutar korona.
Jerin lashe Ballon d'Or tsakanin Messi da Ronaldo:
2019Lionel MessiArgentinaBarcelona
2018Luka ModricCroatia Real Madrid
2017Cristiano Ronaldo PortugalReal Madrid
2016Cristiano Ronaldo PortugalReal Madrid
2015Lionel MessiArgentinaBarcelona
2014Cristiano Ronaldo PortugalReal Madrid
2013Cristiano Ronaldo PortugalReal Madrid
2012Lionel MessiArgentinaBarcelona
2011Lionel MessiArgentinaBarcelona
2010Lionel MessiArgentinaBarcelona
2009Lionel MessiArgentinaBarcelona
2008Cristiano Ronaldo Portugal Manchester United
2007KakáBrazil Milan
Ƴan wasa 30 ne aka fara zaɓa domin lashe kyautar ta bana, kuma ƴan jarida 180 ne suka zaɓi biyar daga ciki.
A karon farko Messi ya taimaka wa Argentina lashe Copa America na 2021.
Ɗan wasan gaba na Poland, Robert Lewandowski, da ke taka leda a Bayern Munich ne ya lashe takalmin zinari a Turai a kakar 2020-21 a matsayin wanda ya fi cin ƙwallaye a raga, bayan ya zira 41 tare da taimaka wa Bayern Munich lashe Bundesliga.
Mujallar Faransa ce ke bayar da kyautar Ballon d'Or duk shekara.
A 2020 ba a bayar da kyautar ba saboda annobar korona - karon farko tun 1956.
Mene ne Ballon d'Or?
Mujallar Faransa ta fara bayar da kyautar Ballon d'Or tun 1956, inda take karrama gwarzon ɗan wasan duniya, kuma ɗan wasan Ingila Stanley Matthews ne na farko da ya lashe kyautar.
Da farko ƴan wasan Turai ake ba kyautar kafin 1995 da aka faɗaɗa ga dukkanin ƴan wasan da ke taka leda a ƙungiyoyin Turai. Daga 2007 gasar ta koma ta duniya.
Ƴan jaridar mujallar Faransa ne ke zaɓen ƴan wasa 30, inda kuma sauran ƴan jarida a faɗin duniya za su zaɓi wanda zai lashe kyautar. Ko wace ƙasa a duniya tana da wakili ɗaya.
Daga 2010 zuwa 2015 aka haɗe kyautar da ta Fifa, amma daga baya suka rabu, inda Fifa ta ƙaddamar da kyautarta mai suna The Best a 2016.