''Wajibi ne sai Jamus ta ci Faransa da Japan mu dawo da martabarmu''

Ya zama wajibi Jamus ta doke Faransa da Japan a wasan sada zumunta, domin dawo da martabarmu, in ji Kai Havertz.

Wasa ɗaya tawagar Jamus ta yi nasara a karawa biyar da ta yi, tun bayan fitar da ƙasar a wasannin rukuni na Gasar cin Kofin Duniya a Qatar cikin 2022.

Hakan ta sa ana ta caccakar koci, Hansi Flick kafin wasan sada zumuntansu na ranar Asabar da Japan, da kuma wanda za ta yi da Faransa a ranar Talata.

Idan Jamus ta gamu da cikas a wasa biyun da za ta yi, wataƙila a kori Flick, bayan shekara biyu yana aiki.

Wasa biyu kacal Jamus ta yi nasara a cikin manyan fafatawa 11 da ta yi a kusa-kusan nan.

''Shekara mai zuwa za mu karɓi bakuncin Gasar cin Kofin Turai, saboda haka ya kamata mu ƙarfafa gwiwar 'yan ƙasarmu da faranta musu rai.'' in ji Havertz.

"Ba ma kallon wasannin a matakin sada zumunta. Mun ɗauki wasanninmu da Japan da kuma Faransa matuƙar muhimmaci. Za mu yi duk abin da ya dace don faranta ran 'yan ƙasarmu.''

Jamus za ta buga wasannin biyu ne, ba tare da Jamal Musiala ba, wanda a ranar Alhamis aka ce zai yi jinya, don haka ba zai buga karawar Bundesliga guda biyu ba.

Tuni Flick ya gayyaci Thomas Mueller, wanda ya maye gurbin Niclas Fuellkrug, wanda ya ji rauni.

Saura wata tara a fara gasar cin kofin nahiyar Turai a Jamus, yayin da 'yan ƙasar ke takaici a kan rashin taka rawar gani, ciki har da fitar da su da aka yi a manyan gasa uku har da European Championship a 2021 zagayen ƙasa 16.

Magoya baya sun yi wa Flick da 'yan wasan Jamus ihu, bayan rashin nasarar da ƙasar suka yi a hannun Colombia da Poland, sai kuma canjaras da Ukraine.

Jamus ta samu gurbin buga gasar cin kofin Turai, saboda ita ce za ta karɓi baƙuncin wasannin a 2024.