Matashin da ya ɗauki hankalin duniya da karatun ƙur'ani a bikin fara gasar cin kofin duniya

Asalin hoton, Ghanima Al Muftah
Tun bayan da aka yi bikin buɗe gasar cin kofin duniya ta bana a Qatar, hankulan mutane da dama suka raja’a kan matashin Balaraben ƙasar da ya mamaye kanun labarai.
Sunan Ghanim Al-Muftah ya karaɗe illahirin kanun labarai da shafukan sada zumunta a fadin duniya saboda irin rawar d aya taka a yayin buɗe gasar ta Qatar 2022.
Ghanim – wanda ya kasance mai lalurar nakasa -fitaccen mai amfani da shafukan intanet ne da ya kasance jakadan hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa a gasar bana.
A wajen bikin buɗe gasar Ghanim Al-Muftah tare da fitaccen ɗan fim na Amurka Morgan Freeman sun yi jawabai masu ratsa zuciya da suka jan hankulan ƴan kallo a filin wasa na Al-Bayt inda bayan kammalawarsu ne aka take wasa tsakanin mai masauƙin baƙi Qatar da kuma Ecuador.
A cikin jawabinsa, Freeman ya yi magana a kan yadda za a yi amfani da wasan ƙwallo wajen haɗa kan al’ummar duniya.

Asalin hoton, Getty Images
An ruɗe da sowa da tafi a lokacin da Freeman da Al-Muftah, wanda yake da lalurar rashin girma, suka bayyana a dandamalin.
Al Muftah ya ɗauki hankali duniya ne da karanto wasu ayoyin Al-ƙur’ani da ya yi a lokacin da suke yi wa baƙi maraba shi da ɗan fim Freeman.
Al Muftah wanda yake da rabin jiki ya ce “Muna bayyana kiranmu, saboda yi wa kowa maraba. Wannan gayyata ce ga ɗaukacin duniya.”
Daga nan matashin wanda ya sanya farar jallabiya da makawuya da baƙin kwarkwar yana tafiya a kan hannayensa ya fara karanto ayoyin Ƙur’ani a cikin Suratu Hujurat aya ta 13.
Ya ambato ayar mai cewa: “Ya ku mutane! Lalle ne Mu, Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da ƙabilu, domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (shi ne) wanda yake mafificinku a takawa. Lalle ne Allah Masani ne, Mai kididdigewa.
Sai Freeman ya cafe da cewa “Na fahimci hakan. Abin da ya haɗa mu a nan ya fi bambancinmu yawa. Ta yaya za mu sa wannan abu ya ci gaba da wanzuwa har gaba da yau?
Al-Muftah ya amshe da cewa “Ta hanyar haƙuri da girmama juna, za mu iya zama ƙarƙashin inuwa ɗaya.”
Wane ne Ghanim Al Muftah?

Asalin hoton, Ghanim Al Muftah website
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifi Ghanim Al Muftah ranar 5 ga watan Mayun 2002, da wata lalura ta halittar rabin jiki, inda ba shi da cinyoyi da ƙafafu.
Ana kiran cutar da ake haife shi da ita wacce ba a faye samun irinta ba, Caudal Regression Syndrome (CDS) a Turance.
Sai dai Ghanim bai bar wannan cuta ba ta nakasa zuciyarsa ba, inda ya yi ta karatunsa har matakin da yake yanzu na neman digiri yana karantar kimiyyar siyas da burin son zama jami’in diflomasiyya.
Ghanim matashi ne mai son abubuwan da suka shafi wasanni kamar hawan dutse da wasan zamiya da sauran su.
A wani bayani da aka wallafa a shafinsa na intanet, an ce an yi ta zuga iyayen Ghanim su zubar da cikinsa tun lokacin da hoton ciki ya gano irin yaron da za a haifa – don kaucewa wahalhalu.
Amma iyayen nasa sun yi biris da zantukan inda suka sha alwashin zame masa ƙafafu da hannaye.
A lokaci da yake ƙarami Ghanim ya sha wahala sosai ta tsangwama da wariya daga wajen yara a makaranta, lamarin da ya hana shi mayar da hankali kan karatu.
Mahaifiyarsa tana yawan ƙarfafa masa gwiwa da cewa ya yi wa abokansa bayani a kan ciwonsa da faɗakar da mutane baki ɗaya.
Daga baya dai Ghanim ya ƙarafafa wa kansa gwiwa ta hanyar zama jarumi da ƙirƙirar abubuwa har ma ya zama fitacce a intanet.
Yana da miliyoyin mabiya a shafukan Instagram da Tuwita da Facebook da Youtube.
Tun bayan wannan bayyana da ya yi a bikin bude gasar, ake ganin farin jinin Ghanim ya ƙaru sosai a faɗin duniya.











