Ku San Malamanku tare da Alƙali Abubakar Salihu Zaria

An haifi Alƙali Abubakar Salihu Zariya ranar 1 ga watan Janairun 1980 a unguwar Tudun Wada cikin birnin Zariya a jihar Kaduna.

Ya fara karatu a makarantar Isah Abdulkarim Nursery and Primary School, kafin ya samu shaidar digirinsa ta farko a Jami'ar Ahmadu Bello inda ya karanta fannin Addinin Musulunci.

Cikin malaman da ya yi karatu a hannunsu, akwai mahaifinsa da Mallam Umar a Tudun Wadan Zariya da Mallam Aminu Adam Nepu, masanin fiƙhu da nahawu, akwai Mallam Mai Bala'i Gyallesu da Mallam Shu'aibu Salihu Zariya.