Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƴan Afghanistan ke tsere wa Taliban
- Marubuci, By Regan Morris & Leire Ventas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Tijuana
Birnin Tijuana da ke kan iyakar Mexico ya dade yana fuskantar matsalar jin kai, yayin da bakin haure ke kwararowar suna taruwa a yankin, da fatan tsallakawa zuwa Amurka.
A tarihi, galibin bakin hauren sun fito ne daga yankin ƙasashen kudancin nahiyar Amurka, amma a yau ana samun ƙarin bakin haure daga wasu ƙasashe, ciki har da ƙasashen Afirka da Asiya da dama.
Wani jifa da aka yi daga kan iyakar Amurka da kuma kusa da gundumar Tijuana, iyalan Afghanistan sun ce suna cikin ƙoshin lafiya a cikin wani tsari na farko na musulmi kawai.
Amma suna tsoron yin yawo a waje mai nisa saboda da firgicin da suka samu a tafiyar da suka yi a cikin ƙasashe 11 don isa nan.
A ƙoƙarinsu na kai wa Amurka bayan da Taliban ta ƙwace mulkin ƙasar fiye da shekaru biyu da suka gabata, sun ce ba su da makoma a Afghanistan - aikin da suke yi tare da kawayen Amurka ya sanya su cikin waɗanda ake hara.
Don haka suka gudu, suna zaman jira na watanni a Iran da Pakistan.
Sun tashi zuwa Brazil sannan suka tsallaka zuwa Darién Gap na Panama da ƙafa, inda aka yi musu fashi da kuma cin zarafi.
An tilasta wa wasu gungun 'yan Afganistan yin tsirara - maza da mata tare - yayin da wasu 'yan bindiga da suka rufe fuska suke neman wasu kuɗaɗe na ɓoye, in ji Shukriah cikin hawaye.
Tsohuwar 'yar jarida, ta nuna hotuna a wayarta na 'yarta mai shekara tara da rauni a idonta.
Ta ce mutanen sun yi wa ‘ya’yanta naushi, har sai da suka samu karin kudi daga kungiyar.
"Yin magana kan lamarin na da matuƙar wahala" in ji ta, yayin da 'ya'yanta ke wasa a kusa.
Gidan Albergue Assabil/Mesquita Taybah ya kasance wuri mai hayaniya kuma cike da rayuwa - tare da yara ƙanana da yawa suna wasa, akwai kuma ɗakin dafa abinci cike da maza suna dafa shinkafa da nama da wake dai dai sauransu.
Yaran suna da ƙwallon ƙafa amma ba su da sarari wajen bugawa, haka suke buga ƙwallon a cikin ƙaramin tsakar gidan.
Ba su zuwa makaranta tun lokacin da Amurka ta bar Afganistan da Taliban suka ƙwace mulki.
Suna da burin sake fara rayuwarsu a Amurka - idan za su iya gano yadda za su nemi mafaka. Wasu sun shafe fiye da watanni biyu suna jiran ganawa da hukumomin Amurka.
Suna tunanin ko su wuce ba bisa ka'ida ba. Sun ji wasu sun tsallaka ta wasu ramuka a bangon iyakar. Amma su suna son yin abin da ya dace, cikin tsari.
"An bar mu a baya," in ji Sofia, wacce daliba ce a Jami'ar Amurka da ke Kabul, wadda Amurka ke daukar nauyinta.
Sofia - kamar sauran mutanen da ke cikin matsuguni - ba ta son a yi amfani da sunanta na ainihi don tsoron kada a cutar da damarta ta shiga Amurka ko kuma ya haifar da illa ga danginta da aka bari a Afghanistan.
Lokacin da Afganistan ta faɗa hannun 'yan Taliban a shekarar 2021, dubban 'yan ƙasar sun mamaye filin jirgin saman Kabul, inda suka mika jarirai zuwa gaban layin tare da daga takarda don tabbatar da aikinsu tare da gwamnatin Amurka.
Sun kasance suna matsananciyar kama jirgin Amurka da ke kwashe mutane.
Sofia ta ce ofishin jakadancin Amurka ya yi mata tayin tashi. Amma a cikin hargitsin da ya barke, ta kasa shiga cikin jama’a har ta isa filin jirgin.
A maimakon haka, ta je Iran sannan Pakistan, inda ta ce jami’an Amurka sun ce ta rubuta takarda don yin hijira.
Bayan watanni takwas, har yanzu ba ta ji komai ba, don haka tare da gungun 'yan uwa da abokan arziki ta tashi zuwa Brazil daga nan kuma ta fara tafiya zuwa Amurka - ta ƙafa da bas jirgin ruwa da kuma taksi.
Sofia ba ta yi tafiya tare da Shukriah ba, amma kuma an yi mata fashi a Darien tsakanin Panama da Colombia kamar yadda sauran bakin haure da muka zanta da su.
Mutane da yawa suna biyan masu fasa-kwauri don kai su Panama - hakan ya zama kasuwanci mai bunƙasa a can. Amma 'yan Afganistan sun dogara da umarnin kafofin watsa labarun don ketare Darien.
Dubban mutane daga China, Indiya, Pakistan, da Kamaru a yanzu suna keta dajin da a da ake ganin ba za a iya wucewa ba, suna bin taron jama'a ta wannan tudun domin tsira.
"Akwai matuƙar hatsari," in ji Sofia, inda ta ƙara da cewa da ta san da hakan, da bata bi su ba a tafiyar.
Da dare, suna jin kukan namomin daji wanda ke sa musu tsoro. Da rana kuma, suna ganin ruwan sama da ke haddasa ambaliyar ruwa sakamakon haka suke hawa tsauni tare da yaransu da kayayyakinsu.
Ƴan bindiga sun ƙwace musu kuɗi da saraƙunansu. Kullum cikin tsoron kar da macizai su cije su.
Wani mutum da ke tafiya tare da su nanutse cikin rafi a lokacin da yake ƙoƙarin tsallaka rafin, in ji Sofia. Ta ce ta ji labarin matan da aka yi wa fyaɗe.
Sofia ta ce ta ga a ciro hannayan mutum biyu daga rafin da kuma kuma gawwarwakin mutane da dama a hanya.
"Kullum cikin kuk muke," in ji ta. "Me ya faru da waɗannan mutane? Ƙilla sun mutu ne sakamakon ambaliyar ruwa, ko kuma wasu namun daji ne suka kashe su, ko ƙilla ƴan bindiga ne suka harbe su, babu wanda ya sani.
Suna iya hango Amurka idan suka fito daga matsugunansu. Suna iya tafiya 'yan matakai ɗari don taɓa bangon iyakar. Amma duk da abubuwan da suka fuskanta, sun ce jiran da suke yi yana azabtarwa.
Don neman mafakar Amurka, ana sa ran bakin haure su yi amfani da manhajar wayar hannu da ake kira CBP One don samun alƙawari tare da Kwastam da Kariyar Iyakoki na Amurka.
Manhajar na da nufin sauƙaƙe tsarin mafakar, amma hakan bai yiwu ba
'Yan ci-rani da kungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun ce bala'i ne kuma ba ya aiki yadda ya kamata, lamarin da ya bar mutane masu rauni makale na tsawon watanni a Mexico suna kokarin samun ganawa.
Matsugunin Tijuana na cike da mutanen da ke jiran tserewa. Shekaru 10 da suka gabata, da wuya aka iya ganin bakin haure daga Asiya ko kuma Afrika, amma a halin yanzu, mutane da dama daga ƙasashe daban-daban ke zuwa garuruwan da ke kan iyaka da kudancin Amurka.
Dalilin da yasa Gidauniyar Musulman ƙasashen kudancin Amurka suka buɗe wannan matsugunin kenan a shekarar 2022 saboda taimaka wa baƙin haure musulmai ta hanyar ba su matsuguni, da abinci da yake halal, da wurin sallah, da kuma wuraren kwana daban-daban na maza da mata.
'Yan Afganistan da suka yi wa Amurka aiki kai tsaye ko a kaikaice na iya fuskantar kisa ko zuwa kurkuku idan aka tasa keyarsu zuwa Afganistan, amma hatta 'yan Afghanistan da aka kwashe zuwa Amurka suna fuskantar rashin tabbas.
Gwamnatin Biden ta tsawaita musu biza na wucin gadi a farkon wannan shekarar, amma da yawa suna zaune a cikin limbo, ba su da tabbas game da matsayinsu na shige da fice a nan gaba.
Kuma ba da jimawa, za su iya fuskantar wahala wajen neman mafaka ko da a ce bakin hauren sun samu ganawa.
A Washington DC, wasu 'yan Republican a Majalisa ba za su amince da taimako ga Ukraine da Isra'ila ba idan gwamnatin Biden ba ta tsaurara takunkumin kan iyaka ba kuma ta saka neman mafaka a Amurka ya zama da wahala.
Sofia ta kasance tana jira watanni biyu a cikin matsuguni - tana ƙoƙari kowace rana don samun ganawa.
"Ba ni da wani zabi illa in jira," in ji ta, ta kara da cewa babu inda za ta kuma ba za ta iya komawa Afganistan ba saboda 'yan Taliban sun san ita "kawar Amurka ce".