Tsaikon sake zaben fid da gwani ya sa shakku ga ‘yan takara a Najeriya

Jam'iyyun siyasa a Najeriya

Asalin hoton, OTHER

Wasu magoya bayan jam`iyyun siyasa daban-daban a Najeriya na fargabar cewa watakila gwanayensu ba za samu damar tsayawa takarar gwamna ba a zaben 2023. 

Sun nuna wannan fargabar ne sakamakon hukuncin da wasu kotuna suka yanke na soke zaben fitar da gwani da jam`iyyun suka yi, tare da ba da umarnin a sake gudanarwa, amma kuma har yanzu shiru kake ji, ga kuma lokaci na kurewa.

A yanzu haka dai wasu ‘yan takarar da magoya bayansu sun zama ‘yan kallo kasancewar ba su san makomarsu ba.

Jam`iyyar PDP a jihar Zamfara da jam`iyyar APC a jihar Taraba duk a arewacin Najeriya, na cikin irin wannan yanayin na rashin tabbas.

Jam’iyyun sun ce babban abin da ke tayar musu da hankali shi ne rashin sake zaben fid da gwani duk da karatowar lokacin babban zabe.

Ambassada Hassan Ardo Jika, jigo ne a jam`iyyar APC a jihar Taraba, ya shaida wa BBC cewa, duk wani dan jam’iyyarsu ta APC a jihar Taraba na cikin fargaba.

Ya ce “ A halin da ake ciki yanzu ba su san me zai faru da jam’iyyarsu a zaben 2023 ba, dalili kuwa shi ne babu dan takara a yanzu a jam’iyyar a jihar, saboda wanda aka ayyana shi ne dan takarar kotu ta soke, ga shi har yanzu babu wani zabe da aka yi don tsayar da dan takara.”

Sai dai hukumar zaben Najeriya ta shaida wa BBC cewa ya kamata `yan siyasa su kwantar da hankalinsu.

Hajiya Zainab Aminu, jami’a ce a hukumar, kuma ta ce hukumar na duba hanyoyin warware duk wata sarkakiyar da ta shafi shari`a kafin a kai ga zaben.

Ta ce suna sa ran kafin lokacin zabe za a yanke hukunci na dukkan kararrakin da ke gaban kotu, sannan wadanda aka ba su damar sake gudanar da zabukan cikin gida za su sake zaben kafin lokacin babban zaben sannan su aike da sunayen wadanda suka samu nasara.

A watan Farairun 2023 ne za fara zaben shugaban kasa da na `yan majalisa, daga nan sai a yi na gwamna da `yan majalisun dokoki na jiha bayan mako biyu.

`Yan siyasa dai sun zuba ido su ga yadda za a warware wannan sarkakiya, saboda wasu na ganin cewa ba lallai ba ne wasu `yan takarar su hakura da shigar da wata sabuwar karar, idan suka ji ba su gamsu da yadda zaben fid da gwanin ya gudana ba.