Larabawa na ganin dimokuradiyya na karya musu tattalin arziki

Laraba sun fara damowa daga rakiyar mulkin dumukuradiyya, wajen bunkasa tattalin arziki a fadin yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Arewa, kamar yadda wani bincike ya nuna.

Kusan mutum dubu 23, kungiyar nan ta kwararru da ke nazarin ci-gaba a kasashen Larabawa wato Arab Brometer ta yi wa tambayoyi a kasashe tara har da yankunan Falasdinawa, a madadin sashen Larabci na BBC.

Yawancin mutanen da aka tattauna da su, sun yi amanna cewa tattalin arziki yana da rauni a karkashin mulkin dumukuradiyya.

An samu wannan sakamako ne kusan sama da shekara goma bayan juyin-juya-hali na kasashen Larabawa, da aka yi domin samar da tsarin dumukuradiyya a kasashen.

Kasa da shekara biyu da yin wannan zanga-zanga, daya kawai daga cikin kasashen da aka yi – Tunisia – ta zama da mulkin dumukuradiyya.

To amma idan har aka amince da daftrain tsarin mulkin da aka wallafa a makon da ya gabata to kasar za ta sake komawa kan salon mulkin karfa-karfa

Darektan kungiyar kwararrun da ke gudanar da bincike, a kan kasashen Larabawa wadda ke Jami’ar Princeton, a New Jersey da ke Amurka, Arab Barometer, wato Michael Robbins,

Wadda za ta gudanar da binciken a tsakanin karshe-karshen shekarar 2021 da bayan lokacin huturu na 2022, ta ce an samu sauyin ra’ayi a kan dumukuradiyya tun bayan da aka yi nazari na karshe a shekarun 2018/19 a kasashen.

Ya ce : "Ana ta kara fahimtar cewa mulkin dumukuradiyya ba ingantaccen tsarin gwamnati ba ne, kuma ba zai iya gyara komai da komai ba.’’

"Abin da muke gani a fadin yankin shi ne, mutane na fadawa cikin fatara da talauci, suna bukatar abinci, mutane suna bakin ciki da damuwa kan tsarin da suke da shi,’’ in ji shi. 

A fadin kasashen da aka gudanar da binciken sama da rabin yawan mutanen da aka yi wa tambaya sun yarda cewa, tattalin arziki yana da rauni a karkashin mulkin dumukuradiyya.

A dukkanin kasashen da aka yi nazarin, sama da rabin mutanen sun ce sun yarda ko kuma ma sun yarda sosai cewa sun fi damuwa da ingancin manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsu, fiye da irin tsarin gwamnatin da ake da a kasar.

Alkaluman rahoton sashen bincike na Jaridar nan ta The Economist, wadda ke Birtaniya, wato EIU, kan mulkin dumukuradiyya, ya nuna cewa kasashen Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Arewa su ne a baya a dukkanin kasashen da aka yi binciken.

Isra’ila kuwa an ayyana ta a matsayin wadda dumukuradiyyarta ke da matsala, yayin da aka bayyana gwamnatocin Tunisia da Moroko a matsayin hadakar wake da shinkafa.

Su kuwa sauran kasashen yankin an sanya su a rukunin masu gwamnatocin karfa-karfa ko kama-karya.

A kasashe bakwai da kuma yankunan Falasdinawa, sama da rabin wadanda aka tambaya a binciken sun yarda da cewa, kasarsu na bukatar shugaban da zai karya doka domin ya gyara al’amura.

A Moroko ne kawai aka samu wadanda suka zarta rabi da kadan suka amince da wannan magana.

Amma kuma akwai wasu masu dan yawa da bas u yarda da kalamin ba a yankunan Falasdinu da Jordan da Sudan.

A Tunisia takwas daga cikin mutum goma da aka tambaya sun yarda da maganar, inda tara daga cikin 10 ke cewa sun goyi bayan matakin Shugaba Saied na rushe gwamnatin kasar tare da dakatar da majalisar dokoki a watan Yuli na 2021.

Abin da ‘yan hamayyarsa suka bayyana da juyin-mulki, wanda shi kuma ya ce abu ne da ya zama dole domin yin garambawul a tsarin siyasar da ya gurbata gaba daya.

Tunisia ta kasance kasa daya tilo da da ta yi kokarin wanzar da gwamnatin dumukuradiyya bayan juyin-juya-hali na kasashen Larabawa na 2011.

Sai dai kuma kasar sannu a hankali tana kara komawa kan mulkin kama-karya karkashin Shugaban Saeid.

Kamar yadda nazarin kwararru na EIU na mujallar The Economist ya nuna a kan mulkin dumukuradiyya a tsakanin kasashe a 2021, kasar ta yi kasa zuwa mataki 21 a jerin.

Kuma an bayyana ta a matsayin gwamnatin hadaka ta wake da shinkafa, amma ba wadda dumukuradiyyarta ta daburce ba.

An gudanar da binciken ne a Tunisia a tsakanin watan Oktoba da Nuwamba na 2021.

Tun daga wannan lokacin an ata zanga-zanga a kann kin jinin shugaban kasar, yayin da yake kara rike iko, ta hanyar rushe majalisar dokoki, da kankane iko da hukumar zabe.

Sannan kuma ya ci gaba da kokarin gudanar da zaben raba-gardama a kan daftarin sabon tsarin mulki, wanda da dama al’ummar kasar ke ganin cewa zai kara bas hi karfin iko.

A yanzu dai tattalin arzikin kasar ya kara tsunduma cikin matsala.

"Yanzu, abin takaici, Tunisia na komawa baya ga mulkin kama-karya, ko abin da muke kira koma-bayan dumukuradiyya,

Wanda shi ne abin da ake gani a fadin duniya yanzu,’’ in ji Amaney Jamal, daya daga cikin wadanda suka samar da cibiyar binciken kan kasashen Larabawa ( Arab Barometer) kuma malami a Jami’ar Princeton.

"Ina ganin daya daga cikin abubuwan da ke haddasa hakan, ba wai kuduri ne na yin kama-karya ba, ko kuma tsarin siyasa na kama-karya ba.

"Kawai abu ne da mutane ke ganin cewa mulkin dumukuradiyya ya gaza a fannin tattalin arziki a Tunisia,’’ in ji masanin.

Ana kallon matsalar tattalin arzikin a kasashe 7 da yankunan Falasdinawa a matsayin babban kalubalen da ya ma fi na rashawa da rashin zaman lafiya da kuma yaduwar annobar korona.

A kasashe biyu ne kawai ba a daukar matsalar tattalin arzikin cewa ita ce mafi muhimmanci.

A Iraqi inda aka fi kallon matsalar cin hanci da rashawa, da kuma Libya da yaki ya daidaita, inda a can kuma rashin zaman lafiya ne aka fi gani shi ne mafi muni. 

Akalla mutum daya daga cikin uku a dukkanin kasashen da aka gudanar da nazarin ya yarda da bayanin cewa, a shekara daya da ta gabata, abincinsu ya ƙare, kafin su sami isasshen kudin da za su sayi wani.

Fafutukar samun abin da za a ci ta fi tsanani a Masar da Mauritania, inda kusan mutum biyu a cikin uku ke cewa hakan na faruwa garesu a wani lokaci ko ma a kai-a kai

An gudanar da yawancin binciken tun kafin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairu.

Yakin da ya kara ta’azzara matsalar karancin abinci a fadin yankin, musamman ma ga Masar da Libya da Tunisia, wadanda sun dogara sosai ga Rasha da Ukraine wajen sayen alkama.

Wadanda aka yi wa tambaya a nazarin, da suka ce suna fama da matsalar samun kudin sayen abinci, idan abincin ya kare musu, ba sa goyon bayan mulkin dumukuradiyya sosai a yawancin kasashen da aka yi binciken musamman a Sudan da Mauritania da Morocco.

Tawagar kwararru masu bincike kan kasashen Larabawa (Arab Barometer), ta Jami’ar Princeton ta Amurka, ita ce ta yi nazarin.

An tambayi mutum 22,765 gaba da gaba a kasashe tara da kuma yankunan Falasdinawa.

Tun 2006 suke gudanar da bincike. Nazarin ya shafi kasashen Larabawa ne, saboda haka bai danganci Isra’ila ko Turkiyya ko Iran ba. Kodayake ya kunshin yankunan Falasdinawa.

An hada da yawancin kasashen yankin, amma da yawa daga cikin gwamnatocin kasashen yankin tekun Fasha, sun ki yarda su bayar da hadin kai ga binciken.

Sakamakon Kuwait da Algeria bai shigo da wuri ba, ta yadda za a iya sanya shi a rahoton na sashen Larabci na BBC.

Ba a iya hadawa da Syria ba saboda wahalar samun shiga kasar.

Bisa dalilai na shari’a da al’ada na bukaci wasu kasashen su bar wasu tambayoyin.

An yi la’akari da wannan mataki a wajen fitar da sakamakon binciken.

Ana iya samun cikakken bayani a kan nazarin a shafin Arab Barometer website.