Pochettino ya sha kashi a hannun Mexico a wasa na biyu a matsayin kocin Amurka

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Mauricio Pochettino ya yi rashin nasara a wasa na biyu a matsayin kocin Amurka a hannun Mexico da ci biyu babu ko ɗaya.

Tsohon kocin Chelsea Pochettino mai shekara 52, ya fara da nasara a kan Panama 2-0 a wasansa na farko a ranar Lahadi, yanzu kuma ya sha kashi a wasan sada zumunta.

"Ba wani ƙoƙari muka yi ba, amma irin wannan wasan wata dama ce a garemu mu gyara ɓarakarmu," in ji Pochettino.

"Duka dai Mexico sun fi mu ƙoƙari kuma sun cancanci samun nasara a wasan, amma a wurinmu wani mataki ne na koyo."

Dan wasan gaban Raul Jimenez ne ya fara da cin kwallo, abin da ya bai wa Mexico damar shiga gaba kenan a wasan da aka yi a Estadio Akron kusa da Guadalajara.

Sannan Cesar Huerta ya jefa kwallo ta biyu, hakan ya sa Mexico ta tabbatar da nasararta, ko da yake magoya bayansu sun ta yi musu ihu sakamakon canjaras da suka yi a makon jiya da ƙungiyar Valencia ta Spain.

Christian Pulisic, Ricardo Pepi da kuma Weston McKennie na daga cikin waɗanda ba su buga wa Amurka ba, wadda ta hari ɗaya tal a wasan.

Mexico ta kawo ƙarshen wasanni bakwai da Amurka ta yi a jere ba ta yi rashin nasara ba.

Mexico ta yi ban kwana da ɗan wasan da ya fi buga mata wasanni a tarihi Andres Guardado da wasa 182 - kuma an masa tafin girmamawa lokacin da aka sauya shi a wasan.