Rodri, Vinicius, Yamal da Messi na cikin masu neman gwarzon ɗan wasan Fifa

A
Lokacin karatu: Minti 2

Yan wasan da dama ne sunayensu suka shiga jerin waɗanda za su fafata wajen lashe kyautar 'yan wasan Fifa na 2024.

Jr Vinicius da yan wasan Manchester City Haalanda da Rodri da ya lashe Ballon dOr suna cikin jerin sunayen.

'Yan wasan City biyun sun shiga cikin jerin ne saboda nasarar da ƙungiyarsu ta samu na lashe Premier a bana sau hudu a jere.

Dan wasan Real Madrid da Ingila Jude Bellingham na daga cikin 'yan wasa 11 d za su iya cin kyautar, waɗanda ke taka leda a Spain.

Lionel Messi, wanda ya lashe kyautar a 2023, shi ɗaya ne ɗan wasan da ke cikin jerin sunayen waɗanda ke taka leda a wajen Turai.

Rodri da ya lashe Ballon d'Or shi ke kan gaba a neman lashe kyautar amma yana fuskantar gogayya daga ɗan wasan Real Madrid Vinicius Jr, wanda ya yi na biyu a zaɓen da aka yi a Oktoba.

Bellongham mai shekara 21, wanda ya zo na uku a gasar Ballon d'Or, na fatanm zama ɗan wasa namiji na farko da zai lashe kyautar Fifa cikin 'yan wasan Ingila.

A bangaren masu horaswa akwai kocin Manchester City Pep Guardiola da na Real Madrid Carlo Ancelloti da na Bayer Leverkusen Xabi Alonso da na Argentina Lionel Scaloni sai kuma na Spain Luis la Fuenta.

A masu tsaron raga akwai na Arsnela David Raya da na Manchester City Ederson da na Aston Villa Emiliano Martinez.

Andriy Lunin na Real Madrid da Gianluigi Donnarumma na PSG da Mike Maignan na AC Milan da kuma Unai Simon na Athlrtic Bilbao sune sauran masu tsaron ragar.

'Yan takarar gwarazan Fifa

Dani Carvajal (Spain/Real Madrid)

Erling Haaland (Norway/Manchester City)

Federico Valverde (Uruguay/Real Madrid)

Florian Wirtz (Germany/Bayer Leverkusen)

Jude Bellingham (England/Real Madrid)

Kylian Mbappe (France/Paris St-Germain/Real Madrid)

Lamine Yamal (Spain/Barcelona)

Lionel Messi (Argentina/Inter Miami)

Rodri (Spain/Manchester City)

Toni Kroos (Germany/Real Madrid)

Vinicius Jr (Brazil/Real Madrid)

Masu horaswa

Carlo Ancelotti (Real Madrid)

Lionel Scaloni (Argentina)

Luis de la Fuente (Spain)

Pep Guardiola (Manchester City)

Xabi Alonso (Bayer Leverkusen)

Masu tsaron raga

Andriy Lunin (Ukraine/Real Madrid)

David Raya (Spain/Arsenal)

Ederson (Brazil/Manchester City)

Emiliano Martinez (Argentina/Aston Villa)

Gianluigi Donnarumma (Italy/Paris St-Germain)

Mike Maignan (France/AC Milan)

Unai Simon (Spain/Athletic Bilbao