Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyi biyar da Elon Musk ya sauya ta ga masu amfani da ita
Wata uku ke nan da Elon Musk ya mazaya zuwa shalkwatar Twitter da take San Francisco – kamfanin ya kuma kasance kusan kan gaba a kullum a da kafofin yada labaru suke badawa.
Mun yi tattaunawa mai tsawon gaske a kan ra`ayoyinsa a game da soshiyal midiya, da kuma karin wasu matakai da yake dauka da suke jawo ka-ce-na-ce da, kamar su rage kashi 50 cikin 100 na yawan ma`aikatan kamfanin, amma ba sosai a game da yadda amfani da dandalin yau-da-gobe ya sauya ga mutum miliyan 237 da yake amfani da dandalin a duk wata ba.
1. Toshe zabin wasu hanyoyin da ake da su na duba Twitter
Sauyi na baya-bayan nan shi ne yadda Twitter ya dakatar da iya kaiwa ga API dinta, wanda ta shi ne sauran dandali suke iya bi domin sadarwa da ita. Saboda haka idan kana amfani da abin da ake kira manaja da ke gudanar da soshiyal midiya ne, domin leka naka shafin da ake kira account, maimakon manhajar app ko dandalin intanet duka na Twitter, kana iya tarar da Twitter ba ta aiki da su a yanzu haka.
Sai dai har yanzun ba a iya fayyace ko da sani aka yi hakan, kodayake kwararru da dama sun yi imanin hakan ne.
“Tunanina shi ne an yi hakan ne saboda manhajoji wadanda su ne na uku wajen taimaka wa sadarwar, ba sa nuna manhajar ads, suna kyale wanda ya shiga, ya yi amfani da manhajarsu da yake gani kamar yadda za su iya, wanda ya zame wa Musk wani iri, a shirinsa na kara yawan ads ga wanda ya shiga zai iya ganin me ke gabansa baro-baro da kuma ba da fifiko ga sakwannin da mutanen da suka biya Twitter Blue suke sakawa,” in ji mai sharhi a kan lamuran fasaha Kate Bevan.
Twitter ba ta yi wata sanarwa a hukumance a kan, manhajojinta na app da suka yi suna wadanda da alamu suke kokarin tsira, da suka hada da tweetbot, da Fenix da Twitterifik.
2. Warkarwa
Watakila sauyin da ya fi bayyana a fili shi ne a tsarin da mutane suke kallon sakwannina Twitter da suke bayyana a gabansu.
Wata sabuwar jagora (new tab) tana gayyatarka ka zabi tsakanin sabbin sakwanni daga mutanen da kake bibiyarsu, da kuma sakwannin da Twita take jan hankalinka zuwa gare su.
Idan kana shiga Twitter ta IPhone ne, za ka ga fili ko sashi guda biyu a sama, “for you/naka” da “following/bibiya” in kuwa kana amfani da Android ne, sai ka danna wani hoto na tauraruwa da yake saman hannun dama da ke kan sikirin na wayar.
Batun da ke nan shi ne yawancin masu hawa Twitter ba su lura da wannan ba, ko ba su kai ga sanin cewa da alamu an sauya manhajar ta app ta komawa “for you/naka” daga lokaci zuwa lokaci ba. Akwai korafe-korafen cewa wannan bangare yana cike da tayi da kuma tattaunawa a tsakanin mutanen da kake bibiya da wadanda ba ka san su ba, maimakon abubuwan da kai ka zabe su tun ma da farko.
Sai dai wasu wannan bai dame su ba: “A wasu ranakun ina so in je gidan abinci da abokina kawai, wasu ranakun kuma zan leka gidan sharholiya domin ganin wane ne ke ciki. Abu ne na nishadi.
3. Mayar da tsofaffin shafukan Twitter da suka yamutsa hazo
Mista Musk ya soma da wasu manyan shafuka da aka haramta su a lokacin gwamnatin da ta gabata saboda saba wa dokokin Twitter.
Sun hada da Ye (mawaki Kanye West) wanda aka haramta shafinsa saboda yada abubuwa da suke sukar Larabawa da Yahudawa, da Andrew Tate (da a yanzun haka yake tsare a Romaniya saboda laifin safarar mutane) da kuma tsohon shugaban Amurka Donald Trump da abubuwan da yake sakawa a shafin nasa na Twitter, ake zargin suna hura wutar boren Capitol Hill wato Majalisar Tarayyar Amurka na watan Janairun shekarar 2021.
4. Twitter Blue/launin ruwan bula na Twitter
Bayan`yar somawar da aka yi da kafar hagu, a karshen watan Nuwamba, sai ga tsarin Twitter Blue ana shiga. Kudi $8/$11 (£6.50/£9) da ake biya a duk wata, akwai alkawuran samun garabasa da ta hada da wajen tace abin da ake so, da bunkasa ganin bayanai tangaran, da wasu daidaikun manhajar ads. Idan aka yi batun labaru masu ban sha`awa na wasu kuwa, kamar ya ja hankalin mutane masu yawan gaske amma ba lodi ba- sai dai ba a taba samun labaru a hukumance da aka fitar a game da nasararsa zuwa yanzun ba.
5. Alamomi na Azurfa da zinari
“Blue tick”, wanda a yanzun ita ce alama ta wanda yake mu`amala da Twitter, ita ce kuma alamar da aka saba gani, ta an tantance shafi. Twitter ita ce da kanta ta samar da shafuka na wasu tsirarun da aka zabo da suka yi suna, da `yan jarida da ire-irensu domin nuna cewa ba na bogi ba ne.
Wadanda suka sayi blue tick a karkashin tsohon tsarin har yanzun suna tare da shi, tare da wani sako da ke bayanin cewa “Legacy” ne da “may or may not be notable” wato batun abu na gado ko da aka bar wa `yan baya, da abu da ake iya lura da shi ko akasin hakan. Saboda haka ganin alamar a ruwan bula wato blue tick a gaban shafi ba tana nufin bai wa shafin wani tambari na iko ba ne.
An maye gurbinsa da wata alamar ta zinari ko azurfa domin wasu nau`ukan kaya da kusoshi na gwamnati – saboda haka Coca-Cola a yanzun alamar zinare aka sa mata, da bayani da ke nuna cewa “kasuwanci ne a hukumance”, sannan shafin Rishi Sunak, firaministan Ingila yana da baje na azurfa.
"Gwanin murza zare"
Gaskiyar ita ce ko da Mista Musk ko babu shi, dole Twitter ta sauya salo.
Yawan masu mu`amala da ita da kudaden shiga da take samu daga manhajojinta na ads sun dade da raguwa, inda soshiyal midiya da suke hamayya da ita suka yunkuro da karfinsu suna ci gaba gadan-gadan babu kama hannun yaro.
An san Twitter a matsayin `yar karamar aba, sai dai ta yi tasiri- sai dai tasirin bai kasance ya rikida zuwa riba ba.
Mr Musk “gwani ne na da ya iya hulda da jama`a, da iya murza zarensa, da kirkira da kago abubuwa”, in ji kwararre bangaren soshiyal midiya Matt Navarra.
Ba ya tsoron abin da zai haifar da jayayya ko yin abubuwan da suka saba wa dokokin da ke cikin littafi.
Sai dai, shin wannan dabaru nasa na kawo sauyi za su farfado da wannan kamfani da yake kan durkushewa, da ya ce yana asarar $4m a kowacce rana a lokacin da ya sayi kamfanin?
Abu ne mai wuyar gaske a iya cewa ga amsar, saboda kamfanin Twita ba ya son bayyana adadinsa. A yanzun kamfani ne mallakar wani, kuma ya cancanci ya zama hakan.
Sai dai ba a ga sabbin masu tallace-tallace suna tururuwa zuwa dandalin ba, masu mu`amala da shi suna korafi a game da sauye-sauyen, da yadda ake nuna musu shafin nasu da kuma canjin da aka yi wa API kwanan nan, da ya bata ran masu bunkasa irin wadannan kamfanoni, da Twita yake bukata daga waje, domin taimaka masa bunkasa.
“Da alama yanayi ya sauya, sauyawar da ta sha bamban da can baya,” in ji Mista Navarra a game da kwarewarsa a huldar, ta mai masu bibiyarsa su dubu da dari da hamsin (150,000).
“Ban ga wata alama ta ci gaba ba, a sabuwar Twitar”