An sa zare tsakanin Dan Aliyu da Rabe a damben Marabar N'Yanya

Damben gargajiya

An dambata tsakanin Dan Aliyu da Rabe Shagon Ebola a wasan safiyar Lahadi a Marabar N'yanya jihar Nasarawan Najeriya.

An tsara wasannin a gidan damben Bambarewa sarkin yaƙin masu gidajen dambe a ƙasar.

An kuma yi wasannin ne da aka yi wa 'yan damben Arewa biyo ajo, wato Sha'aike da Shamsu Dogon Autan dan Bunza.

Dan Aliyu daga Arewa da Rabe daga Kudu sun sha kida daga makadin 'yan dambe Labaran dan Gwamba, wanda ya yi musu kurarin da ya ba su karfin shiga fili.

Turmin farko ba wanda ya kai duka haka ma a turmi na biyu, daga baya ne suka sa kuzari a turmi na uku, amma ba kisa aka raba su.

Sauran wasannin da aka buga a ranar ta Lahadi Boloko da Shagon Lawwalin Gusau, turmi biyu suka yi ba kisa.

Shi kuwa Shagon Na Aisha nasara ya yi a kan Shagon Na Jafaru Kura a turmin farko.

An kuma yi canjaras tsakanin Autan Na Aisha da Garkuwan Dunan Ba-ta-Jemu ba, amma 'yan damben sun samu kudi sosai daga 'yan kallo,domin sun yi wasa mai kyau.

Shi ma wasan Garkuwan Kurma da Shagon Bokan Sama'ila ya ƙayatar, sannan aka kammala da wasa tsakanin Shagon Basiru da Dogon Inda.

An kuma sa kudi a wasa tsakanin Rabe da Autan Na Aisha, amma wani dan kallo ya hana damben cewar Autan Na Aisha kada ya yi wasan.

An buƙaci ya bayar da kudi fiye da wanda aka sa, shi kuwa bai yi hakan ba, inda 'yan kallo wadanda suka bukaci yin dambe suka kara kudi.

Daga ƙarshe dai ba yi damben da kowa ya so ya kashe ƙwarƙwatar ido ba.