Teloli na son mayar da Nairobi wani sabon birni na zamani ta fuskar tufafi

Asalin hoton, JOSEPH BARAZA
A jerin wasikun da muka samu daga 'yan jaridun Afirka, Ismail Einashe ya ziyarci wasu shaguna biyu da ake amfani da matattun tsummokara domin dinka wasu sabbin nau'ukan kayan amfanin yau da kullum da kuma sabbin nau'ukan sutura.
A yayin da gari ya yi lumshi a Nairobi babban birnin kasar Kenya, na ga wasu teloli guda biyu na amfani da keken dinki wajen harhada nau'ukan kayayyakin amfani kamar jakar daukar kaya, a jikin bangon shagunan kuma ana iya ganin wasu jakunkuna da aka jera wadanda aka dinka daga tsofaffin sutura.
Wannan aikin da telolin ke gudanarwa a wani shago da ke unguwar Suave, wanda ke hawa na biyu na ginin Charming wanda aka yi wa fenti da launin fari da shudi, da Mohamed Awale, ya gina a shekarar 2013. Wannan shago na daya daga cikin manyan shagunan dinka kayan jakunkuna.
Suna amfani da matattaun kayayyaki wajen mayar da su kayayyakin amfani kamar jakunkunan adana kaya, da jakar daukar kaya, da kananan abubuwa kamar su karamar jakar sa kudi, da karamar jakar adana hotuna.
Haka kuma wannan shago ya zama wani wajen sarin kaya ga 'yan kasuwar Gikomba, daya daga cikin manyan kasuwannin kayan gwanjo a yankin gabashin Afirka, ya ce ya fara wannan sana'a ne domin rage matattun tufafi a kasar.
Telolin suna mayar da kayan gwanjo kamar su wandunan jeans da kananan riguna, da rigunan kwat wadanda aka shigar kasar daga Amurka ko Turai zuwa wasu abubuwa masu masu matukar amfani ga dalibai da matasan kasar.

Asalin hoton, PETER NJOROGE/BBC
Telan ya ce ya fara sana'arsa ne a wani dan karamin daki da ke harabar babban shagon nasa, kuma daga wannan lokacin ne kasuwancin nasa ya ci gaba da habaka.
Sana'ar Awale ta ja hankalin manyan kamfanonin tallata kayayyaki ta intanet kamar su Google ya kuma rika sayar da kayayyakinsa zuwa kasashen waje.
Kuma a farkon wannan shekarar ya samu tallafin karo karatu daga wata gidauniya mai suna Ethical Fashion Initiative, inda ya je ya yi wani kwas na wata biyu a birnin Florence na kasar Italiya, inda ya samu horo a fannin dinka jakunkuna da dangoginsu, tare da kuma samun horo kan yadda zai habaka sana'arsa.
A daya gefen kuma wani katafaren shagon sayar da dinkakkun tufafi ne a wani babban mai dinka tufafi mai suna Kepha Maina.
Ya kafa shagon nasa ne a shekarar 2013, wanda kuma yake gudanarwa daga zauren gidansa da ke tsakiyar birnin Nairobi.

Asalin hoton, FLUX COLLECTION @KEPHAMAINA
Maina ya samu kwarin gwiwar wannan sana'a tasa ne daga kayayyakin da manyan masu sana'ar hannu na yankin gabashin Afirka kamar su Ibrahim el-Salahi, wani fitaccen mai sana'ar fenti na kasar Sudan.
Sabanin masu irin wannnan sana'a a biranen Paris da Milan, a Nairobi ba a gudanar da bikin baje-kolin irin wadannan kayayyaki saboda karancinsu a a kasar.
A yanzu dai Maina ya fitar da sabbin kayan ya yi guda hudu, kuma cikin watan Satumba zai kaddamar da wani sabon nau'in ya yi na zamani, inda ya ce zai samar da sabbin nau'ikan tufafi na zamani da za su dace da al'umar kasar.

Asalin hoton, FLUX COLLECTION @KEPHAMAINA
Sai dai matsalar da masu sana'a irin wannan ke fuskanta a Kenya ita ce mafiya yawan al'umar kasar ba sa sayen sababbin nau'ikan tufafi na zamani wadanda 'yan Kenya suka dinka, a maimakon haka sun fi mayar da hankali kan nau'ikan da aka shigo da su daga kasashen ketare.
Duk da wannan kalubale da masu irin wannan sana'a irin su Maina ke fuskanta, a cikin 'yan shekarun nan an fahimci cewa ana samun yawaitar masu irin wannan sana'a a birnin Nairobi abin da ke alamta cewa al'umar kasar suna fara karbar hajojin nasu.











