Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ziyarar Shugaban Faransa zuwa Morocco ke nufi ga Algeria?
- Marubuci, BBC Arabic Service
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
A wannan makon ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ya je Moroko, bisa gayyatar Sarki Mohammed VI, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Ziyarar ta biyo bayan amincewar da Faransa ta yi shirin 'yancin cin gashin kai na ynkin Yammacin Sahara, amincewar da ta yi ta kasancewar yankin a matsayin wani muhimmin ɓangare na ƙasar Moroko.
Ta bai wa yankin 'yancin cin gashin kai inda al'ummar yankin za su kasance ƙarƙashin gwamnati ta kansu wadda kuma za ta kasance ƙarƙashin Moroko.
Ziyarar ta kasance ta farko ta Macron tun 2018. Kuma ta biyo bayan kusan shekara uku ta zaman tankiya da sasanto na hulɗar diflomasiyya tsakanin Faransa da Morokon.
Tsamin dangantaka
An riƙa samun tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu a shekarun nan.
Musamman kan zargin da ya biyo bayan wani rahoton 'yan jarida da ya zargi Moroko da amfani da na'urar leken asiri da satar bayanai a kan jami'an Faransa, ciki har da Shugaba Macron, a 2021zargin da Moroko ta musanta.
Sannan a Satumban 2021, Faransa ta tsaurara matana bayar da biza a kan 'yan Moroko, inda a watan Janairu na 2022 tsohuwar ministar waje ta Faransar, Catherine Colonna, ta je Moroko domin sasanta lamarin.
Sai dai kuma a bara saɓanin ya sake tasowa lokacin da Moroko ta zargi Faransa da hannu a rahotan Tarayyar Turai da ke zargin Moroko da takura wa 'yan jarida a Moroko.
Bugu da ƙari gwamnatin Moroko ta nuna ɓacin ranta a kan alaƙar Faransar da Algeria, inda ta buƙaci Paris ta fito fili ta nuna matsayinta kan maganar Yammacin Sahara.
Shi dai wannan yanki ne da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana a matsayin wanda ba shi da gwamnatin kansa, wanda kuma Moroko ke iƙirarin yankinta ne, tare da shirin ba shi ƙwarya-ƙwaryan 'yancin-kai.
Ita kuwa ƙungiyar Polisario wadda Algeria ke mara wa baya na son a yi ƙuria'r raba-garma ne domin yanke hukunci a kan yadda yankin zai kasance - ƙarƙashin Moroko ko kuma mai cikakken mulkin kai.
Yadda batun Sahara ya sauya al'amura
Gwamnatin Moroko na amfani da batun Sahara a matsayin wanda take tantance ƙawayenta da kuma abokan gabarta a manufofinta na waje.
Gwamnatin tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ta amince da matsayar gwamnatin Moroko a kan yankin Sahara a ƙarshen 2020, a matsayin wani sharaɗi na gwamnatin Morokon don amincewa da buƙatar Amurka ta mayar da dangantaka da Isra'ila.
Tsawon shekaru Faransa ta yi ƙoƙarin kasancewa 'yar ba-ruwanmu a rikicin Morokon kan yankin Yammacin Sahara - saboda matsayin Algeria na mai goyon bayan ƙungiyar fafutukar 'yancin kan yankin.
A ranar 30 ga watan Yuli, Shugaba Macron ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga matsayin Moroko a kan yankin - abin da a ƙarshe ya kai ga shirya ziyarar shugaban a Moroko.
Abin da bai bayyana ba shi ne yadda wannan alaƙa za ta shafi matsayin alaƙar Faransa da Algeria.
Ko wannan ya sauya ƙarfin Algeria a yankin?
Dangantakar Algeria da Faransa ta inganta tsakanin 2010 da 2020. To amma nan da nan alaƙar ta yi tsami a ƙarshen watan Yuli bayan da Macron ya sanar da goyon bayansa ga shirin bayar da ƙwarya-waryan cin gashin kai ga yankin Sahara.
Farfesa Hasni Abidi, ɗan Algeria - masani kan hulɗar ƙasashen duniya a Jami'ar Geneva ya ce tun ma kafin ziyarar Macron akwai alamar tsamin dangantaka tsakanin Faransa da Algeria.
To amma duk da abubuwan da suka faru na tsamin dangantaka, ƙasashen biyu sun ci gaba da alaka in ji masanin.
Wane amfani ko illa sasantawar ke da shi?
Ziyarar Macron a Moroko ta wuce ƙoƙarin farfaɗo da dantaka tsakanin ƙasashen biyu - ziyara ce da ke da manufa babba ta duniya idan aka yi la'akari da matsalolin siyasa da tsaro a Gabas ta Tsakiya da yankin Sahel na Afirka.
Wannan ya ƙara nuna cewa Faransa na son ta yi amfani da alaƙarta ta Moroko ta ƙara tasirinta a Afirka - ganin yadda tasirin ke zagwanyewa a shekarun nan, inda ƙasashe irin su Mali suke karkata ga Rasha.
Masani Hasni Abidi ya ce Faransa ta dogara ne a kan Moroko a kan abubuwa da dama, saɓanin Algeria, wanna shi ya sa ta karkata wajenta.
Wannan ya haɗa da ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci da zuba jari da Faransar ke yi a Moroko
Tururuwar baƙin haure zuwa Turai
Batun ƙaurar jama'a zuwa Turai abu ne da yake da muhimmanci a alaƙar Moroko da Faransa, inda ake kallon gwamnatin Moroko a matsayin mai muhimmanci a ƙoƙarin da Turai ke yi na hana tururuwar baƙin haure zuwa nahiyar, saboda kusancin Morokon da Turai, inda ta nan yawanci mutane ke bi.
Wannan ya sa Turai ke ganin Moroko za ta iya taka rawa mai muhimmanci sosai wajen rage yawan baƙin haure zuwa Turai.
Duk da yadda ake hawa sama da fado a hulɗa tsakanin Faransa da Moroko, dangatakar tarihi da al'ada tsakaninsu ta ci gaba da wanzuwa da kyau.
Faransanshi shi ne harshe na farko wanda ba na hukuma ba a Moroko, sannan kuma manufofin Faransa a kan Moroko na ci gaba da wanzuwa a fannoni daban-daban, abin da ke nuna aƙalla alaƙa na wanzuwa lami lafiya a tsakaninsu duk da saɓanin da kan bijiro lokaci zuwa lokaci.