Iyalan da suka kwashe fiye da shekara 50 suna haƙa kabari a Najeriya

Magaji Abdullahi (tsakiyar ) tseye riƙe da shebur tare da 'yan'uwansa Aliyu (hagu) da Abdullahi (dama) a maƙabartar Tudun Wada a jihar Kaduna

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC

    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kaduna
  • Lokacin karatu: Minti 5

Sama da shekara 50, wasu iyalai suka sadaukar da rayuwarsu wajen kula da wata babbar maƙabarta a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Sun kwashe waɗannan shekaru suna yin wannan aiki na haƙa kabari da wankan gawa, ba tare da ana biyansu ba, sai dai tallafin da ba za a rasa ba daga ƴan'uwan mamatan.

Hukumomi sun ware wa musulman garin Kaduna babbar maƙabartar sama da shekara 100 da ta gabata.

A 1970 ne Ibrahim da Adamu iyalan gidan Abdullahi suka soma aikin na kula da maƙabarta.

Waɗannan ƴan'uwan juna, yanzu haka suna kwance cikin kabari a wannan maƙaɓarta ta Tudun Wada, yayin da yanzu haka 'ya'yansu biyu ke kula da wannan aiki.

"Sun koyar da mu cewa, Allah yana son wannan aikin da muke kuma shi ne zai biya mu koda ba mu samu komai na duniya ba," Cewar Ibrahim, babban ɗan Abdullahi, Magaji ya shaida wa BBC hakan ne yayin da aka tambaye shi me ya sa suka zaɓi ci gaba da wannan aiki duk da ba a biyansu.

Mutumin mai shekara 58 shi ne shugaban masu kula da maƙabartar, inda yake da ma'aikata 18 a ƙarƙashinsa.

Shi da 'yan'uwansa, Abdullahi mai shekara 50 da kuma Aliyu mai shekara 40, (Ƴaƴan Adamu Abdullahi), waɗanda su ne masu kula a kodayaushe da maƙaɓartar, na tsawon sa'o'i 12 kullum.

Akwai buƙatar su kasance kodayaushe a wajen aikin saboda musulmau ba sa jinkirta rufe mamaci.

Masu tona kabari a maƙabaratar Tudun wada Kaduna.

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC

Bayanan hoto, Yana ɗaukar aƙalla sa'a guda kafin a haƙa kabari, kuma suna amfani da awon da waɗanda suka shirya gawar suka aike musu.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana kiran wayar Magaji a kowane lokaci, kodai kai-tsaye ƴan'uwansa ko kuma limamai, dukkan malaman addini na birnin suna da lambarsa.

"Mutane da dama na da lambar wayarmu, saboda haka da zarar wani ya rasu ana kiranmu domin mu yi aikinmu."

Ɗaya daga cikin 'yan ukun yakan je ya ga gawar, a wanke da shi a kuma naɗe ta da likkafani.

Zai auna jikin mamaci domin tura bayanai ga sauran, domin gina masa kabari.

Ana ɗaukar kusan sa'a guda kafin a gina kabari mai tsawon kafa shida, amman wani lokaci ya danganta da laushin wurin da za a gina kabarin, ana samun sauƙi idan wurin babu duwatsu.

Mutanen kan haƙa kabari 12 a rana, duk tsananin zafi da ake yi a Kaduna.

"A yau mun haƙa kabari takwas, gashi ko ƙarfe 12 na rana bai yi ba," cewar Abdullahi wanda ya soma aiki a maƙabarta yana shekara 20.

'Yan'uwan junan na shan wahala musamman lokacin da aka samu rikicin addini tsakanin musulmi da kirista a Kaduna.

Al'ummomin guda biyu na rayuwa ne a kusa da kogin kaduna.

Mutane na addu'o'i a kan wani kabari bayan binne gawa a maƙabartar.

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC

Bayanan hoto, Ana rufe mamaci a ranar da ya rasu, kuma ana rufe gomman gawarwaki duk rana a maƙabartar Tudun Wada.

"An fuskanci rikice-rikicen addini a Kaduna, amman wanda ya fi tsaya min a rai shi ne wanda aka yi a 1990, saboda an kashe mutane da dama," a cewar Magaji.

"Mun riƙa yawo muna kwashe gawarwaki daga kan tituna domin yi masu sutura."

An riƙa rufe muslimai a Tudun Wada, yayin da aka riƙa rufe kiristoci a kudanci.

"Na fuskanci ƙalubale saboda ban jima da fara aikin ba, amma kuma hakan ya ƙarfafa mini gwiwa wajen jajircewa akan aikin."

Yawanci, idan yan uwan junan suka gama haƙa kabari, a lokacin salloli biyar na farillah, limamin masallacin da ke unguwar da aka yi rasuwar na ba da sanarwar cewa akwai jana'iza.

Mutane na zuwa inda gawar take domin yi mata sallah, inda daga nan ake ɗaukarta domin kai ta maƙabarta a binne ta.

Idan aka isa ana saka gawar cikin kabarin sai a sanya itatuwa da fasassun tukwane, inda daga bisani ake bi da ƙasa a rufe ya yi ɗan tudu daga sama.

Bayan kammala rufe mamacin, kafin waɗanda suka kawo gawar su tafi, masu kula da maƙabarta na neman tallafi wajensu.

hoton

Inuwa Mohammed dattijo mai shekara 72, wanda ya fi dukkan masu aikin shekaru, ne ke tattara sadakar, wanda kuma shi ne ya yi bayani kan mahimmacin aikin da iyalan Abdullahi ke yi.

Dattijon ya yi aiki ne tare da mahaifan ƴan'uwan junan masu kula da maƙabarta " Mutane ne masu mutunci waɗanda suke son aikin da suke yi, suka kuma ɗora yaransu bisa wannan ɗabi'a."

Ƴan kuɗin da ake ansa da su ake sayen abincin rana ga ma'aikatan, sai dai ba su isa, saboda haka iyalan suna da wata ƙaramar gona da suke noma abinci.

Ana sake gina kabari kan wani bayan shekara 40, saboda haka filin da za a rufe mutane ba matsala ba ne, illa kawai abinda ke da wahala shi ne kula da wajen.

"Yanzu haka muna da matsala ta rashin isassun kayan aiki, da rashin tsaro, " Cewar Aliyu wanda shi ne ƙarami gaba ɗaya cikin waɗanda ke aikin na kula da maƙabartar Tudun Wada, wanda kuma ya kashe shekara 10 yana aikin.

Ya yi bayanin yadda wani ɓangare na bangon maƙabartar ya zube, lamarin da ya sa ake shiga ana sace ƙarafan da aka yi alamar ƙabarurruka a wajen.

Yawancin kabarurrukan anyi amfani da ƙarafa wajen yi masu shaida, ind ake saka suna da ranar haihuwa da ta mutuwa, kodayake da yawan malaman musulunci ba su goyon bayan hakan. Abin da ya sa wasu ke amfani da duwatsu wajen yin shaida ko icce ko bulo.

Ƴan'uwan junan ba sa mantawa da inda aka rufe kowane mutum, suna ƙoƙarin nunawa wadanda suka kasa gane inda aka rufe ƴan uwansu.

wani kabari da aka sanya wa alama da bayanan wanda ke cikinsa

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC

Bayanan hoto, Wani lokaci ana yi wa kabari shaida yana kuma daukar shekara 40 kafin a sake gina wani bisa shi.

Bayan ziyarar da BBC ta kai a maƙabartar, mutanen sun samu sauyi mai ban mamaki.

Inda sabon shugaban ƙaramar hukumar da ke kula da yankin ya yanka masu albashi.

Shugaban karamar hukumar, Rayyan Hussain ya shaida wa BBC cewa, "Sun cancanci hakan, idan aka yi la'akari da hidimta wa al'umma da suke yi kullum."

"Kabari shi ne gida na ƙarshe ga dukkanninmu, kuma mutanen da ke wannan aikin sun cancanci a biya su, ofishina zai ci gaba da biyansu har zuwa stawon lokacin da zani sauka."

Magaji ya tabbatar wa BBC cewa ma'aikatan sun fara samun albashi a karon farko.

Mutum biyar mafiya daɗewa a kan aikin sun samu naira dubu 43,000, yayin da sauran suka samu naira dubu 20,000.

Ma'aikatan haƙar kabari

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC

Bayanan hoto, Albashin da aka fara biyan ma'aikatan na Tudun Wada bai kai adadin mafi ƙanƙanatar albashi na Najeriya ba.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce yana fatan nan gaba zai ƙara wa ma'aikatan albashi, yayin da ya nuna kuma takaicinsa na banzatar da maƙabartar da tsohon shugaban ƙaramar hukumar ya yi.

Ya kuma yi alƙawarin sake gina katangar da kuma samar da wuta mai aiki da hasken rana da kuma samar da tsaro.

"Zani kuma a gina ɗaki da za a riƙa wankan gawa domin rufewa, abin da yawanci ake yi a gida."

Iyalan gidan Abdullahi sun yi maraba da matakan, inda Magaji ya ce yana fatan ɗaya daga cikin yaranshi 23 za su gaji shugabancin kula da maƙabartar.