Hanyoyi biyar na inganta aikin ɗansanda a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin ne wasu tsoffin ƴansandan Najeriya suka yi zanga-zangar lumana a Abuja babban birnin Najeriya kan yadda suka ce ana ba su abin da bai taka kara ya karya ba a matsayin fansho da kuma giratuti.
Tsoffin ƴansandan daga sassa daban-daban na Najeriya na gudanar da zanga-zangar ne a Abuja, buƙatarsu ita ce a tsame su daga tsarin fansho na 'karo-karo."
"Na yi ritaya bayan kwashe shekara 35 yana bauta wa ƙasa amma a ƙarshe naira miliyan 2.5 kacal aka biya shi a matsayin giratuti, sannan ake ba shi naira 40,000 duk wata a matsayin fansho. Me wannan kuɗin zai yi min? In ji wani tsohon ɗansanda da ya yi zanga-zangar ta ranar Litinin.
BBC ta tuntuɓi Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin samar da bayanai kan tsaro Beacon and Security Intelligence kan hanyoyin inganta aikin ɗansanda inda ya bayar da hanyoyi biyar na walwala.
"Ba bu abu mafi muhimmanci ga aikin ɗan sanda kamar walwala. Kuma walwala na nufin abubuwa masu yawa kamar haka" In ji Malam Kabiru Adamu.

Asalin hoton, FCT Police command
1) Albashi da Fansho mai tsoka
Babban abin da ya fi ci wa ƴansandan Najeriya tuwo a ƙwarya shi ne albashi da fansho.
Ko da zanga-zangar da suka yi a ranar Litinin na da alaƙa da batun albashin da neman a cire su daga tsaron fansho na karo-karo.
Malam Kabiru ya ce Batun albashi da alawus-alawus na ƴan sanda na cikin muhimman abubuwan da ake buƙata domin inganta rayuwarsu.
"Albashi na gaba-gaba wajen bai wa duk wani ma'aikaci walwalar da ta kamata ya samu ya gudanar da ayyukansa. Ya kamata idan ana son inganta aikin ɗan sanda a Najeriya to a ba su albashi daidai gwargwadon buƙatunsu na yau da kullum domin guje wa matsalar rashawa da cin hanci. Kuma wannan na nufin a ƙarshen aikinsu za su samu fansho da giratuti mai kauri." In ji Malam Kabiru.
2) Kayan aiki
Masanin harkar tsaron na Najeriya ya ce dole ne a samar wa ƴansanda kayan aiki kuma na zamani.
"Idan dai har ana son inganta aikin ɗan sanda to dole ne a sama sa kayan aiki na zamani waɗanda doka ta tanada. Wannan ya haɗa da makamai da ababan hawa kamar motoci da babura da ma man da za a yi amfani da shi a ababan."
Ƴansandan Najeriya na kokawa dangane da rashin kayan aiki da suka jiɓancin duk wani da zai sawwaƙe musu gudanar da ayyukan nasu.
3) Sutura
A lokuta da dama akan ga ƴansanda cikin kayan sarki marasa tsafta ko kuma waɗanda suka koɗe da ma tsufa tare da ƙoƙaƙƙen takalmi.
Wasu ƴansanda sun shaida wa BBC cewa suna amfani da kuɗaɗensu ne domin sayan kayan.
"Mafi yawan lokuta da kuɗinmu muke sayan uniform. Kuma ga shi albashin bai taka kara ya karya ba. To da me za mu sayi uniform ɗin? In ji wani ɗansanda.
Malam Kabiru Adamu ya ce dole ne a sama wa ɗansanda tufafi mai kyau domin jin daɗin aikinsa.
"Yanayin suturar da jami'an tsaro ke sakawa na taka muhimmiyar rawa wajen sanya musu ƙaimin sha'awar yin aiki sannan kuma ta ƙara musu ƙima a idanun ƴan ƙasa." In ji masanin tsaron.
4) Kula da Lafiya
"Ya kamata duk wani ɗansanda da shi da iyalinsa ace suna da damar zuwa asibiti a duba lafiyarsu kodai kyauta ko kuma ta tsarin insorar lafiya kamar yadda al'amarin yake a wasu ƙasashe. Hakan ne zai ba su ƙarfin gwiwar tsayawa su yi aiki kan jiki kan ƙarfi." In ji Malam Kabiru.
Masanin ya ci gaba da cewa "bai kamata a ce ɗan sanda ba shi da lafiya amma ya rasa inda zai je ya samu kulawa ta musamman walau yana cikin aikinsa ko kuma ya bar aiki."
5) Muhalli
Duk da cewa gwamnati na ƙoƙarin sama wa ƴansanda bariki a lokacin da suke aiki, ya kamata tsarin ya kai har lokacin da za su ajiye aiki.
Malam Kabiru ya ce "ya kamata a saka ƴansanda a cikin tsarin samar da gidaje ga ƴan ƙasa ta yadda za a riƙa cire wani abu daga albashinsu. Kenan bayan kammala aikinsu za su zama suna da mahalli."
Ya ƙara da cewa duk lokacin da aka ce ɗansanda ba shi muhalli mai kyau sannan wadatacce da zai zauna da iyalansa to zuciyarsa ba za ta daidaita a kan aikinsa ba.
"Kuma wannan ya kamata ya zama lokacin aikinsu da ma bayan aikin nasu," in ji masanin.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴansanda nawa ne za su wadaci Najeriya?
Malam Kabiru Adamu ya ce babu gaskiyar cewa Majalsiar Ɗinkin Duniya ba ta ƙayyade cewa a samar da ɗan sanda guda ɗaya ga farar hula 450.
Ya ƙara da cewa akwai abubuwan da ake dubawa kafin a ƙayyade yawan ƴan sandan da ya kamata a samar a ƙasa.
"Idan ka duba a Najeriya, akwai hukumomin da ya kamata a ce suna ƙarƙashin ƴan sanda ne misali kamar EFCC da ICPC masu yaƙi da rashawa da cin hanci da hukumar kiyaye haɗurra. Amma ban sani ba ko siyasa ce ko mene ne ya sa aka raba su.
Saboda gane haƙiƙanin yawan ƴan sandan da Najeriya ke buƙata ya dogara ne ga tantance irin ayyukan da ya kamata su yi. Amma dai zancen gaskiya Najeriya na buƙatar ƙarin ƴan sanda." In ji Kabiru Adamu.
A 2024, shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin ganin ya inganta aikin ƴan sanda ta hanyar ƙara yawansu da samar musu makamai na zamani domin tafiyar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.










