Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mazauna Gaɓar Yamma na murnar amincewa da ƙasar Falasɗinu a yayin da Isra'ila ke kutsawa
- Marubuci, Lucy Williamson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Middle East correspondent in Jenin
- Lokacin karatu: Minti 5
BBC ta tsinci Abdel Aziz Majarmeh tsaye kan gawar ɗansa mai shekara 13 mai suna Islam da sojojin Isra'ila suke harbe a gab da sansanin ƴan gudun hijira na Jenin da ke gaɓar yamma da Kogin Jordan.
"Ina ganin ɗana ya faɗi a ƙasa bayan na ji ƙarar harbin bindiga," in ji shi. "Sai motar sojoji ta ƙaraso wajen, inda sojoji kusan biyar ko shida suka fito suka nuna ni da bindigoginsu suna cewa in tafi. A lokacin ban san ɗana ya yi shahada ba, sai na yi ƙoƙarin ɗaukarsa."
Abdel Aziz ya ce ya je sansanin ne wanda sojojin Isra'ila suka mamaye tun a watan Janairu domin ya kwaso wasu takardun gidansu.
"Babu wanda zan kai wa ƙara, domin komai na ƙarƙashin kulawarsu ne. Ita gwamnatin Falasɗinu ba ta iya yi wa kanta komai."
"A zuciyata sai nake ta mamakin shin me ya sa sojojin suka harbi ɗan ƙaramin yaro mai shekara 13?"
Sojojin Isra'ila sun ce sun yi harbi ne domin tarwatsa wata barazana da suke fuskanta a yankin, amma ta ƙara da cewa rundunar ta fara bincike domin gano abin da ya faru.
Sai dai ba ta yin cikakken bayanin wace irin barazana ɗan ƙaramin yaron yake da ita ba.
Birane kamar Jenin sun kasance ƙarƙashin Falasɗinu ne tun gomman shekaru da suka gabata da aka ƙulla yarjejeniyar Oslo tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.
Amma Isra'ila ta ce ana gudanar da ta'addanci a yankin, wanda a cewarta hakan ya sa a watan Janairu, ta aika da tankokin yaƙi zuwa Jenin da birnin Tulkarem domin abin da ta kira yaƙi da wasu ƙungiyoyin Falasɗinawa, inda ta ce ta ɗauki darasi ne da abin da ya faru a Gaza.
Ƙasar Birtaniya da wasu ƙasashen yamma sun amince da samar da kafa ƙasar Falasɗinu mai ƴanci, wanda ya zo daidai lokacin da Isra'ila ke ƙara ƙaimi wajen mamaye gaɓar yamma da Kogin Jordan.
Magarin Garin Jenin, Mohammed Jarrar ya zagaya da wakilin BBC cikin sansanin gudun hijira, inda ake harbe Islam.
Jarar ya ce kusan kashi 40 na Jenin na ƙarƙashin sojojin Isra'ila ne a yanzu, kuma mutane da dama sun tsere daga gidajensu.
"Tun da farko muka fahimci akwai wata maƙarƙashiya jibge sojoji a yankin, ba wai domin samar da tsaro ba. Burin Isra'ila ƙwace gaɓar yamma da Kogin Jordan."
Haka kuma Isra'ila ta ƙaƙaba takunkumai kan gwamnatin Falasɗinu na tattalin arziki.
Mr Jarrar ya ce yanzu yankin na fama da matsin tattalin arziki, domin rashin kuɗaɗen gudanar da muhimman ayyuka da ƴan yankin ke buƙata.
Shi ya sa ya ce amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu da ƙasashen turai suka yi zai taimaka musu.
"Wannan zai tabbatar da cewa Falasɗinawa na da ƙasarsu, ko da kuwa tana ƙarƙashin mamayar wasu," in ji shi.
"Na san amincewar za ta sa Isra'ila ta ƙara faɗaɗa mamaye Gaɓar Yamma, amma duk da haka amincewar na da muhimmanci."
"Ba za a taɓa samun ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu ba," in ji Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a lokacin da yake ganawa da mazauna gaɓar a makon jiya.
"Yankin nan namu ne, kuma dole mu ƙwace abin da muka gada."
Shugaban Amurka Donald Trump ma ya bayyana rashin amincewarsa da kafa ƙasar Falasɗinu.
Isra'ila ta kutsa gaɓar ne bayan yaƙin Isra'ila da Larabawa a shekarar 1967, kuma tun lokacin ta jibge sojoji a yankin.
Wani mazaunin yankin mai suna Ayman ya ce Isra'ilawa sun kafa garuruwa a yankin, "kusan kullum sai ka ga baƙi sun zo suna cewa mu kwashe kayanmu, mu bar yankin baki ɗaya."
"Suna kwashe mana kaya suna zubarwa. Idan ma ka kai ƙara, za ka sojojin da ƴansanda duk mutanen baƙin ne.
A yarjejeniyar Oslo, an amince Isra'ila ta jigbe sojojinta a wasu ƙauyuka irin wannan.
Amma tun lokacin Isra'ila ta ƙi janyewa, lamarin da ke shan suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam.
Ayman ya ce mahaifinsa ya rasu ne a dalilin ciwon zuciya bayan baƙi sun ƙone musu gida a shekarar 2003, sannan ya ƙara da cewa bayan lokacin ma, an sha sake ƙona musu gida.
"Wane ne ya kamata in kai wa kuka? ƴansandan Falasɗinu? ko a birni sun kasa hana komai ballanta a ƙauye irin wannan. A nan tsarona yana hannun waɗanda suka mamaye mu ne."
"Akwai sauran rina a kaba, amma ba zan taɓa barin gidan nan ba sai dai idan an fitar da gawata. A nan aka haife ni, kuma a nan na girma, ta yaya zan bar gidan da na fi sani?"
A gomman shekarun da aka yi a ƙarƙashin yarjejeniyar Oslo, Isra'ila ƙara ƙaimi take yi, sannan ƙungiyoyi masu ɗauke bindga na Falasɗinu ma ƙara ƙarfi suka yi.
"Falasɗinu ba ta Isra'ilawa ba ce, kuma ba za ta taɓa zama tasu ba," in ji Abdel Aziz Majarmeh wanda yake jimamin rasuwar ɗansa.
"Ko mu jima ko mu daɗe, watarana sai sun bar ƙasar nan, kuma sai Falasɗinu ta samu cikakkiyar ƴanci."
Sai dai bayan amincewa a Falasɗinu da Birtaniya da wasu ƙasashen turai, hankali ya fara komawa kan wace ƙasa ce za ta mulki Gaza.
Wasu Isra'ilawa sun ce Gaɓar Yamma yanki ne da dole a yi amfani da zahirin da yake bayyane wajen mulkinsa, ba wai amfani da dokokin da rubuce ba.
Isra'ila ta daɗe tana cewa ba zai yiwu a samu ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu ba sai da amincerta.
Amma yanzu da Birtaniya da wasu ƙasashen suka amince da ƙasar, alama na nuna cewa Isra'ila ita kaɗai ba za ta iya hanawa ba.