Jihohin Najeriya bakwai da ke kan gaba a samun kudin shiga

Lokacin karatu: Minti 4

Adadin kuɗin da jihohin Najeriya ke samu daga kason tarayya ya kusan ninkawa idan aka kwatanta da kafin 2023, sakamakon cire tallafin man fetur, a cewar cibiyar budgIT mai nazarin kasafin kuɗi a Najeriya.

Galibin jihohin kan dogara da kuɗaɗen rabon razikin ƙasa da suke samu daga gwamnatin tarayya, wanda ake rabawa a kowane wata, tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin da kuma ƙananan hukumomi.

Da kuɗaɗen ne jihohin ke gudanar da ayyuka da biyan albashi da kuma tafiyar da gwamnati.

Don haka idan babu wannan kuɗi jihohin ƙasar da dama ba za su iya gudanar da kansu ba.

To sai dai akwai jihohin da ke ƙoƙorin samar wa kansu hanyoyin dogaro da kai ta hanyar inganta karɓar haraji da inganta kasuwanci domin dogaro da kansu.

BBC ta yi nazarin alƙaluman da Cibiyar BudgIT ta ƙayyade tare da tantance ƙarfin arzikin da kowace jiha ke da shi da alƙaluman da hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta fitar kan harajin cikin gidan na jihohi.

Sai dai cibiyar ta BudgIT ba ta sanya jihar Rivers - mai ɗimbin arzikin man fetur - cikin lissafin ba, saboda dokar-ta-ɓacin da aka sanya wa jihar a farkon shekarar nan, lamarin da ya sa ta kasa wallafa abin da samu a 2024.

Legas

Jihar Legas ce kan gaba cikin jihohin da suka fi samun kuɗin shiga, kamar yadda shafin BudgIT ya nuna.

Legas ta yi gagarumin yunƙuri wajen haɓa wa kanta kuɗin shiga.

A shekarar 2024 da ta gabata jihar ta samu kuɗin shiga da ya kai naira tiriliyan 1.26, ƙarin kashi 50 cikin 100 na abin da ta samu a shekarar 2023, kamar yadda BudgIT ya nuna.

Kuma bayanai sun ce kashi 73 cikin 100 na wannan kudi jihar - wadda ke kudu maso yammacin ƙasar ta same su ne daga harajin da take karɓa

Jihar Legas na da tarin kamfanoni masu yawa da manya-manyan otel-otel ga kuma tasoshin jiraren ruwa da ake shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, ga kuma yanzu katafariyar matatar mai ta Dangote, mafi girma a Afirka.

Enugu

Jihar Enugu da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya na daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen samun kuɗin shiga, a cewar BudgIT.

Ana ganin jihar za ta iya riƙe kanta da abin da take samu ko da ba ta samun kason tarayya ba.

Jihar ta samu gagarumin ci gaba na kuɗin shigar da take samu a cikin gida.

Arzikin da jihar ta samu a cikin gida a 2024 ya kai naira biliyan 180.50, ciki har da naira biliya 26.68 da ta samu ta hanyar biyan haraji.

Kano

Bisa alƙaluman da hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta fitar sun nuna jihar Kano ta samu kuɗin shiga na cikin gida har naira biliyan 74.77 a shekarar 2024, saɓanin naira biliyan 37.38 a 2023.

Hukumar tattara haraji ta jihar ta Kano, KIRS ta kuma sha alwashin tattara harajin cikin gida da ya kai naira biliyan 180 a 2026.

Kaduna

Jihar Kaduna na biye wa maƙwabciyarta Kano inda jihar ta samar da naira biliyan 71 na harajin cikin gida a shekarar da ta gabata ta 2024, kamar yadda alƙaluman hukumar tattara harajin jihar ta Kaduna wato KADIRS.

Kwara

Jihar Kwara - wadda ke tsakiyar Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ake ganin karansu ya kai tseko ta fuskar tara kuɗin shiga a cikin gida.

Cibiyar BudgIT ta ce jihar ta tara kudin shiga a cikin gida ya kai naira biliyan 65.16 a 2024

Bayan da BudgIT ta fitar sun nuna cewa jihar Kwara ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar tara kuɗin shiga a wannan shekara cikin shekara huɗu da suka gabata.

Anambra

Jihar Anambra na cikin jihohin da suka yi wa sauran takwarorinsu zarra ta fuskar tara kudin shiga a cikin gida.

Jihar - wadda ke yankin kudu maso gabashin ƙasar - ta samu kuɗin shiga a 2024 har naira biliyan 42.97, ƙari a kan naira biliya 36.20 da ta samua a 2023 a cewar BudgIT.

Anambra na da manyan fitattun kasuwanni da ke taimaka mata samun kudin haraji, ciki har da kasuwar onasha, wadda ta yi fice a yankin Afirka ta Yamma.

Abia

Bayanan da ƙungiyar BudgIT ta fitar sun nuna cewa jihar Abia da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya na daga cikin jerin jihohin da ke ƙoƙarin rage dogara da kason gwamnatin tarayya.

BudgIT ta ce kuɗin shigar da jihar ke samu a cikin gida ya ƙaru daga biliyan 17.99 a 2023 zuwa naira biliyan 41 a 2024.

Matsalar rashawa

Masana tattalin arziƙi sun sha faɗin cewa jihohi da dama za su rayu ko da kuwa babu tallafin gwamnatin tarayya, idan har za su cire son zuciya sakamakon rashawa da cin hanci da suka baibaye harkokin gwamnati.

Wasu jihohin da dama na tara yawan kuɗin da ya bi wanda suke bayyanawa sannan wasu kuma kan gaza tara isassun kuɗin ne sakamakon rashin cikakken tsarin karɓar haraji da kuma siyasar da ake sakawa a tsarin karɓar.