Kungiyoyin Saudiyya na zawarcin Salah, Arsenal za ta dauke Sesko

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta dauke dan wasan gaban Ingila mai shekara 28, Ollie Watkins daga Aston Villa (Talksport)
Arsenal na tunanin sayen dan wasan gaban RB Leipzeig mai shekara 20, Benjamin Sesko, a kan kudi £60m (Telegraph - subscription required)
Dan wasan Masar da Liverpool mai shekara 31, Mohamed Salah Mai tsaron ragar Brazil dan shekara 31 suna cikin manyan yan wasan da kungiyoyin gasar Saudiyya ke zawarci (Guardian)
Kila Erik ten Hag ya ci gaba da horas da Manchester, inda dan kasar Holland din mai shekara 54 zai yanke hukunci kan makomarsa, bayan kammala wasan karshe na gasar FA ta bana, a ranar 25 ga watan Mayu. (Guardian)
Thomas Tuchel, wanda Manchester United ke fatan zai maye gurbin Ten Hang, ya fara tattaunawa da Bayern Munich game a kan batun sake kulla wata kwangilar da su.(Times - subscription required)
Chelsea ta gabatar da sabon tayi a kan dan wasan tsakiyar Palmeeira, Willian Estevao kuma ta cimma yarjejeniya da dan wasan Brazil din.(Sun)
Kungiyoyin Saudiyya na zawarcin tsohon dan wasan Chelsea da Manchester United da kuma Tottenham, boss Jose Mourinho. Al-Qadsiah. (Mail)
Manchester United na shirin dauke dan wasan bayan Ingila mai shekara 21, Jarrad Branthwaite da kuma dan wasan kasar Belgium. (Manchester Evening News)
AC Milan da Sevilla fafutukar daukar dan wasan gaban Portugal mai shekara 21, dake taka leda a Wolve,Fabio Silva. (Caught Offside)
Borussia Dortmund na zawarcin dan wasan Ingila mai taka leda a Sunderland, Jobe Bellingham.(Football Insider)














