An dakatar da eja din Olise na Crystal Palace wata shida

Michael Olise

Asalin hoton, Getty Images

An dakatar da mai kula da wasannin dan kwallon Crystal Palace, Michael Olise wata shida, bayan karya dokar cinikin dan wasan a lokacin da yake Reading a 2019.

An samu Glen Tweneboah da laifin kulla yarjejeniyar da zai samu kaso 10 cikin 100 idan aka sayar da Olise ga wata kungiyar, koda yake bai karbi kason ba.

Olise, wanda ya fara taka leda daga makarantar horar tamaula ta Royal Academy ya saka hannu kan yarjejeniyar kwararren dan wasa a 2019.

Mai shekara 22 ya ci kwallo 10 a Palace a kakar nan, wanda aka yi ta alakanta shi da cewar zai bar Selhurst Park, wanda yake da farashin £60m.

An kuma ci tarar Reading £200,000 kan rawar da ta taka kan batun a lokacin shugaba, Nigel Howe, wanda aka dakatar wata12 aka kuma ci shi tarar £5,000.

Wani kwamiti ne mai zaman kansa ya yi bincike kan lamarin da hukumar kwallon kafar Ingila ta kafa, don fayyace gaskiyar lamarain.

Dakatarwar da aka yi wa Tweneboah za ta fara aiki ranar 4 ga watan Oktoban 2024 - Kuma zai iya tattaunawa da wata kungiyar kan nemarwa Olise kungiya - an kuma ci tarar sa £15,000.

Haka kuma an ja kunnen mai kula da huldar tamaula a Reading, Michael Gilkes da sakatare, Sue Hewett kan hannu da suka tsoma kan lamarin.