Mutum biyu sun mutu a hadarin jirgin ruwan Mexico a Amurka

b
Lokacin karatu: Minti 1

Akalla mutum biyu sun mutu wasu 19 sun jikkata lokacin da wani jirgin sojin ruwan Mexico ya daki gadar Brooklyn da ke birnin New York na Amurka.

Magajin Birnin Eric Adams ya ce jirgin mai suna Cuauhtémoc ya fuskanci tangarda gab da yin tsarin a yammacin jiya Asabar.

Kuma hukumomi sun ce mutane 277 ne a cikin jirgin da ke wata ziyara kasar.

Hotunan da aka yada a shafukan intanet sun nuna yadda turakan da ke dauke da lemar da ke kada jirgin Cuauhtémoc ya daki gadar lokacin da ya zo wucewa a jiya Asabar.

Ma'aikatan jirgin na tsaye a jikin turakan a lokacin, inda turakan suka fada cikin jirgin ruwan.

Babban jami'i na musamman na 'yan sandan New York, Wilson Aramboles ya ce ya yi amanna tangardar na'ura da daukewar wutar jirgin ne suka haddasa hatsarin

Ya ce "ina ganin tangarda aka samu da jirgin ya kubucewa matukinsa, hakan ya sa turakan jirgin suka daki gadar".

Biyu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin na halin rai kwakwai-mutu-kwakwai.

Magajin birnin Erit Adams ya ce babu abin da ya shafi gadar ta Brooklyn, sannan babu wanda ya fada cikin ruwa.

Tun da fari, sojin ruwan Mexico sun ce mutane 22 ne suka jikkata a hadarin amma ana gudanar da bincike.