Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Burkina Faso: Ina alƙawuran da Kyaftin Ibrahim Traoré ya yi?
Shekara uku kenan tun bayan da Kyaftin Ibrahim Traoré ya hau mulkin Burkina Faso, bayan da ya hambarar da wani sojan Laftana Kanar Paul Henri, wanda shi ya fara ture gwamnatin tsohon shugaban kasar Roch Marc Christian Kaboré.
A lokacin da ya hau mulkin, Ibrahim Traoré ya ce wanda ya gada bai cika alkawarin da ya yi wa al'ummar kasar ba, musamman ma a fannin tsaro. Haka kuma ya zarge shi da rashin iya mulki.
A lokacin da ya karbe mulki kungiyoyin 'yanbindiga na rike da akalla kashi 40 cikin dari na yankunan kasar, kamar yadda wani rahoto na Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaro (ISS) ya nuna.
A kan hakan Ibrahim Traoré ya nuna kudurinsa na yakar kungiyoyin domin kwato wadannan yankuna.
To amma zuwa yau kamar yadda wani rahoto na Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da aka wallafa ranar 19 ga watan Maris na 2025, gwamnatinsa ta tabbatar da cewa tana da iko da kashi 69 cikin dari ne na kasar a yanzu.
A lokacin da shugaban ya kama mulki a watan Satumba na 2022 ya yi alkawarin cewa, zai murkushe 'yanbindigar a cikin wata shida, sannan ya shirya zabe a cikin wata goma sha biyu ya mika mulki ga farar hula.
To sai dai a lokacin wani taro a Ouagadougou, cikin watan Yuli na 2024, shekara biyu bayan juyin mulkin, Ibrahim Traoré, ya sauya shawara, inda ya gabatar da shirinsa na raya kasar na tsawon shekara biyar.
Wato kenan zai tsawaita mulkinsa da shekara biyar.
Bayan kudurinsa na kwato sassan kasar da ke hannun 'yan tawaye, shugaban ya bayyana irin tanade-tanaden da ya ce ya yi wa al'ummar kasar na bunkasa rayuwarsu da kuma karbe izinin hakar ma'adanai daga hannun 'yan kasashen waje.
To zuwa wannan lokacin - shekara uku bayan ya kwace mulki, me za mu iya tunawa daga alkawuran da shugaban mulkin sojin ya yi?
Bangaren tsaro
Kungiyar IS da Al-Qaeda suna ta kai munanan hare-hare a Burkina Faso tun 2015.
Wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba sun ce wadannan hare-hare sun yi sanadin mutuwar dubbai - wadanda suka hada da fararen hula da sojoji, sannan sama da mutum miliyan biyu sun tsere daga muhallinsu.
A lokacin da ya hau mulki Ibrahim Traoré ya yi alkawarin kawo karshen wadannan hare-hare, tare da korar mayakan kungiyoyin ya kwato yankunan da suka mamaye.
A matakin farko sabon shugaban na Burkina Faso ya fitar da kasarsa daga kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, kafin su kirkiri kungiyar hadaka ta kasashen yankin Sahel (AES) tare da Mali da Nijar.
Haka kuma ya janye kasarsa daga alaka da kasashen da suka saba mu'amulla tun asali - kamar Faransa, inda ya kulla kawance da Rasha, domin ta taimaka masa yakar kungiyoyin 'yan bindigar.
Gwamnatin sojin ta dauki 'yan-sakai 9,000 domin karfafa rundunar sojin kasar, baya ga wasu matakai da ya dauka na yakar kungiyoyin 'yan bindigan da inganta tsaron kasar.
Zuwa watan Agusta na wannan shekarar ta 2025 gwamnatin ta ce ta yi nasarar kwato kashi 69 cikin dari na kasar.
Shugaban, wanda ya samar da sababbin kayan aiki ga rundunar sojin kasar, ya yi kira ga sojojin da su zage damtse su kara kwazo wajen ceto kasar.
Ya ce ta hakan ne kadai kasar za ta tabbata mai 'yancin kanta.
Da sauran tafiya a tsaron kasar
Jawabai da matakan da gwamnatin sojin ke dauka ba su hana 'yan bindigan kai hare-haren ba a kasar ta Burkina Faso.
A zahiri dai shugaban yana kokarin cika alkawarin da ya yi na kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi kasar.
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kungiyoyin 'yan bindiga sun tsananta munanan hare-hare a kan sojoji da farar hula, tare da kame wasu sassan kasar.
Daya daga cikin hare-hare mafiya muni da aka kai kasar shi ne na Barsalogho, a arewa maso tsakiyar kasar a watan Agusta na wannan shekara ta 2025.
Kungiyar GSIM, mai alaka da Al-Qaeda, wadda ta kai harin kamar yadda wasu bayanai suka nuna ta hallaka sama da mutum 400, to amma gwamnati ba ta fitar da nata alkaluman ba.
Bayan wannan harin akwai wasu da 'yan bindigan suka kai a wasu sassan kasar, kamar garin Kounla, inda suka kai kan tawagar soji, suka kashe wasu tare da raunata wasu.
Hare-haren sun taba hatta tsakiyar babban birnin kasar, Ouagadougou, lamarin da ya kai ga tarin mutane kaura domin samun mafaka a makwaftan kasashe, irin su Mali da arewacin Togo.
Har yanzu yanayin tsaro a kasar ta Burkina Faso abu ne mai tayar da hankali.
Saboda haka kungiyoyi da dama da ke lura da abin da ke faruwa na cewa, akwai sauran aiki sosai a kan lamarin.
Batun zamantakewa da tattalin arziki
A lokacin da ya kwace mulki Kyaftin Traoré ya sha alwashin sake gina kasar tare da inganta harkar mulki.
A kan haka ya yi wasu dokoki masu muhimmanci na tabbatar da kishin kasa da yaki da nuna fifiko ko sonkai na siyasa a aikin gwamnati.
Yaki da cin hanci da rashawa ya kai ga kama tsohon ministan sufuri Vincent Dabilgou tare da yanke wa wasu mutane 11 hukunci a kotu kan almubazzaranci da kokarin danne kudin al'umma.
Shugaban ya bullo da wasu manufofi da tsare-tsare da kuma ayyuka na bunkasa tattalin arzikin kasar da samar da sababbin abubuwan jin dadin rayuwa da zuba jari a harkar noma.
Sai dai masana na gargadin cewa: ''Duk da cwa wadannan matakai ne masu kyau da za su bunkasa masana'antu a kasar, to dole ta lura da kyau kada ta kai ga fadawa tarkon, cin hanci da rashawa da almubazzaranci da sauran illoli da aka san kamfanoni da hukumomin gwamnati a kasashen Afirka.''
Alkawuran da ba a cika ba da kuma kalubale
Kan batun mulkin siyasa, shugaban juyin mulkin na watan Satumba na 2022 a Burkina Faso, ya tabbatar wa da kungiyar ECOWAS cewa zai mayar da mulki ga farar hula zuwa shekara ta 2024, kamar yadda suka cimma yarjejeniya.
To amma maimakon ya mutunta wannan yarjejeniya, sai ya fice da kasarsa daga kungiyar ta yammacin Afirka, inda ya shiga hadakar sabuwar kungiyar yankin Sahel ta kasarsa da Mali da kuma Nijar.
A wani jawabi da ya gabatar a talabijin na kasar, shugaban ya ce muhimmin abin da ke gabansa shi ne yaki da rashin tsaro da kare kasar amma ba shirya zabe ba.
Wannan ne ya sa Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaro ta Afirka, ISS, ta ce jawabin nasa ya nuna ba zai cika alkawarin da ya yi na mayar da mulki ga farar hula ba.
Baya ga haka, ya fake da yaki da kungiyoyin 'yan bindiga da ke yi masa barazana, ya tsawaita mulkinsa da shekara biyar.
Bayan matsalar tsaro da ke ci gaba da ta'azzara, wadda kuma ya yi alkawarin shawokanta a cikin wata shida, akwai kuma matsalar 'yan gudun hijira, wadda ita ma yake fama a kanta.
Cibiyar ISS, ta ce akwai kusan mutum miliyan biyu da hare-hare suka raba da muhallinsu a cikin kasar, da kuma wasu sama da 36,000 da ke bukatarkusan dala miliyan 877 domin taimaka musu da muhalli da kula da lafiya, amma kuma kasar ba ta da wannan kudin.
Matsalar tsaron na ci gaba da tilasta wa tarin mutane kaura, lamarin da ke kara ta'azzara matsalar a kasar har ma zuwa makwabtanta.
Bayan matsalar tsaron, fatara da talaucin daman sun addabi al al'ummar kasar.
ISS na ganin tafiyar da ake yi wajen aiwatar da sauye-sauye da kuma yaki da rashawa, na haifar da cikas tare da sanya kokwanto a kan kudurin gwamnatin.
An dakatar da 'yanci
Duk da wadannan matsaloli na gazawa, da rashin cika alkawarun da ta yi, gwamnatin ta Burkina na dogaro da akidarta ta yaki da kuma daina mu'amulla da kasashen mulkin-mallaka, kamar Faransa, domin ta samu goyon bayan al'umma.
To amma ta hakan kuma gwamnatin na kawar da kai daga 'yancin al'umma da daidaikun mutane.
Kungiyoyin kare hakkin dan'Adam da dama na zargin shugaban mulkin sojin na Burkina Faso da rufe bakin masu suka tare da kirkirar yanayi na fargaba da tsoro.
Gwamnati na tilasta wa 'yan farar hula da 'yan jarida zuwa fagen daga wajen yaki da kungiyoyin ta'addanci.
Rahoton kungiyar Amnesty International ya nuna cewa ana kama mutanen da gwamnati ke zargi da zagon-kasa ko hada baki a yake ta, ba tare da bin ka'ida ba.
Masu fafutuka da 'yan jarida da alkalai na bacewa a rasa inda suke.
A jawabin da ya yi ranar 1 ga watan Afirilu Kyaftin Ibrahim Traoré ya ce Burkina Faso ba ta cikin dumukuradiyya tana bin gwadabe ne na juyin-juya-hali na ra'ayin kawo-sauyi.