Me ya sa ƙungiyar Kano Pillars ta kasa kataɓus a kakar bana?

Asalin hoton, Kano Pillars FC/Facebook
A ranar Laraba 3 ga watan Disamba ne ƙungiyar Rivers United ta jihar Rivers ta doke Kano Pillars da ci ɗaya mai ban haushi, lamarin da ya ƙara fama ciwon da ke damun magoya bayan ƙungiyar ta Kano.
A wasan na mako na 15 a wasannin gasar cin kofin Firimiyar Najeriya, Rivers United ta zura ƙwallo a ragar Pillar ne a minti 88 a fara wasan, bayan magoya bayan ƙungiyar ta Masu Gida sun fara tunanin komawa da maki ɗaya, sakamakon da ya sa ƙungiyar ta ƙara zama daram a ƙarshen teburi.
Zuwa yanzu ƙwallo bakwai suka zura tun daga fara gasar ta bana, amma an zura mata ƙwallo guda 17 a ragarta. Ke nan ƙwallo 10 ne ya raba tsakanin waɗanda ta jefa, da waɗanda aka jefa mata.
A cikin wasa takwas na ƙarshe da ta buga, nasara ɗaya kawai ta samu, inda ƙungiyar ta doke ƙungiyar Ikorodu City da ci biyu da ɗaya a ranar 24 ga watan Nuwamban bana a filin wasa na Muhammad Dikko.
A ranar Lahadi kuma za ta karɓi baƙucin Kun Khalifat a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, kuma ko ta yi nasara za ta ci gaba da zama ta ƙarshen teburi.
Wasannin Pillars takwas na ƙarshe
Rivers United 1–0 Kano Pillars
A ranar Laraba 3 ga watan Disamba ne Rivers ta yi wa Pillars ci ɗaya mai ban haushi a jihar Rivers.
Kano Pillars 2-1 Ikorodu City
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar 24 ga watan Nuwamban bana ne Pillar ta doke Ikorodu City a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina.
Remo Stars 1-0 Kano Pillars
A ranar 19 ga watan Nuwamba ne Remo ta doke Pillars da ci ɗaya mai ban haushi a filin wasan MKO Abiola da ke birnin Abeokuta a jiyar Ogun.
Bendel Insurance 3-2 Kano Pillars
A ranar 15 ga watan Nuwamba ne Insurance ta doke Pillars da ci uku da biyu a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin na jihar Edo.
Kano Pillars 0-0 Bayelsa United
A ranar 9 ga watan Nuwamba, an tashi canjaras a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina, inda Pillars ke buga wasanninta na gida.
Enyimba 2-0 Kano Pillars
A ranar 2 ga watan Nuwamba ne ƙungiyar Enyimba ta doke Kano Pillars da ci biyu da nema a filin wasa na Enyimba da ke birnin Aba a jihar Abia.
Kano Pillars 0-2 Niger Tornadoes
A ranar 25 ga watan Oktoba Niger Tornadoes ta bi Pillars har gida a jihar Katsina ta doke ta da ci biyu da nema.
Barau FC 2-1 Kano Pillars
A wasan hamayya da aka buga a ranar 19 ga watan Oktoba a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, ƙungiyar Barau FC ce ta samu nasarar doke Pillars da ci biyu da ɗaya, amma Barau ce a gida kasancewar a lokacin an mayar da Pillars da buga wasanninta a Katsina.

Asalin hoton, Kano Pillars FC/Facebook
Matsaloli
Ƙungiyar Kano Pillars ta sha fama da matsaloli a kakar ta bana, inda bayan wasanta da ƙungiyar Shoting Stars rigima ta ɓarka, har aka cire mata maki uku daga ƴan maki kaɗan da ta tara, sannan aka ci ta tarar naira miliyan 9 tare da mayar da ita wasanni a filin wasa na Muhammad Dikko da ke jihar Katsina.
Haka kuma ƙungiyar ta yi canjin mai horaswa, ina bayan wasanta da ƙungiyar Barau a Kano ta dakatar da Ogenyi Evans, sanna a ranar 21 ga watan Oktoba aka sanar da naɗa fitaccen mai horar da ƴan wasa Muhammad Babaganaru a matsayin sabon kocin ƙungiyar.
Naɗa shi ke da wuya magoya baya suka fara murna da tunanin za ta koma ganiyarta, amma har yanzu da za a iya cewa jiya-i-yau.
Domin jin me ya sa ake samun kwan-gaba-kwan-baya a ƙungiyar, BBC ta zanta da mai sharhin wasanni, Salisu Musa Jegus, wanda ya ce akwai matsaloli jigbe a ƙungiyar.
"A wasan ƙwallon ƙafa abubuwa da yawa ne suka kawo nasara, duk da cewa nasarar zuwa take, amma ana kalon wasu matakai irin su yadda aka shirya ƙungiyar da tunanin ƴan ƙungiyar da ma irin tunanin masu jagorantarta da yadda aka ɗora ta. Idan ya ya zama ana kan daidai to za a samu nasara, amma idan ya zama akwai tasgaro to lallai dole za a samu rashin nasara," in ji shi.
'Yadda za a gyara'
A game da yadda za a iya magance matsalolin da ƙungiyar ke fuskantar, Salisu Jegus ya ce akwai wasu abubuwa da yake tunanin suna buƙatar garambawul domin ƙungiyar ta koma kan ganiya.
Ya ce akwai ɓangaren ɗaukar nauyi wanda gwamnati ce take ɗaukar nauyin Kano Pillars, "sai kuma akwai ƴan wasa da masu horaswa da shugabanni sai masu goyon baya."
- Gudanarwa: Ya ce a ɓangaren shugabanci dole a ƙara ƙaimi, domin a cewarsa, ba maganar gyara fili ba ne kawai ko kayan sakawa, "dole a ba waɗanda suka san harkar dama su jagoranci ƙungiyar kafin a riƙa samun nasarar da ake buƙata. Akwai matsala a ɓangaren gudanarwa."
- Ya ce akwai ɓangarorin shugabanci guda uku, "akwai kwamishinan wasanni, akwai Janar-Manaja sannan akwai shugaban hukumar gudanarwa. Don yadda waɗannan shugabannin uku za su aiki tare abu ne mai muhimmanci. Ko kuma idan zai yiwu a bar ɗaya kawai ya jagoranci ƙungiyar."
- Masu horaswa: Masanin ya ce akwai buƙatar ƙungiyar ta samu masu horasa da suke da ƙwarewa ta zamani kuma suke tafiya da zamani.
- Magoya baya: A ɓangaren magoya baya, waɗanda ake tunanin ƙungiyar tana cikin ƙungiyoyin da suke da ɗimbin magoya baya a ƙasar, Jegus ya ce suna buƙatar fahimtar hanyoyin da za su riƙa zaburar da ƙungiyar. "Su dai suna ƙaunar ƙungiyar ne, amma akwai buƙatar su san hanyoyin da za su riƙa zaburar da ita ba su riƙa jawo mata matsala ba."
- Ƴan wasa: A ɓangaren ƴan wasa, Jegus ya ce ana buƙatar waɗanda suke da ƙwarewa da gogewa a kan gasar Firimiyar Najeriya. Sannan ya ce akwai buƙatar su riƙa zuwa ne a adana su kwana biyu kafin wasa.











