Karyewar farashin kayan abinci da abin da hakan ke nufi ga ƴan Najeriya

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Laraba ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarni ga wani kwamitin gwamnatin tarayya da ya aiwatar da matakan gaggawa domin sake karya farashin kayan abinci a faɗin ƙasar.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubale na tsadar rayuwa, duk da cewa an fara ganin ɗan sauƙi a farashin wasu kayan abinci a kasuwanni daban-daban.

Sai dai tambayar ita ce: Me ya janyo wannan saukar farashi? Menene tasirinsa ga talakawa da kuma manoma? Kuma wane mataki ya kamata gwamnati ta ɗauka domin tabbatar da cewa wannan sauƙin farashin ba zai zama barazana ga noman cikin gida ba?

Me ya janyo karyewar farashin?

Domin samun ƙarin haske a kan wannan lamarin, BBC Hausa ta tuntuɓi Alhaji Lawal Garba Kurfi, masani kan harkar noma kuma shugaban manoman masara na ƙasa a jihar Katsina.

A cikin hirarsa, Kurfi ya bayyana cewa saukar farashin kayan abinci abu ne mai kyau, musamman ga masu ƙaramin ƙarfin tattalin arziki.

"Abin jin daɗi ne idan aka kalla ta fannin talakawa, domin yanzu da kuɗinka kaɗan za ka iya siyan kayan abinci da za ka iya ciyar da iyalanka. Wannan sauƙi yana bai wa mutane damar samun isasshen abinci, rage radadin tsadar rayuwa, sannan ya sa rayuwar yau da kullum ta zamad da ɗan sauƙi ga kowa da kowa," in ji shi.

Kurfi ya kara da cewa wannan karya farashi yana da matuƙar amfani musamman ga iyalai masu ƙaramin kuɗi, domin zai basu damar samun kayan abinci cikin sauƙi ba tare da sun shiga cikin matsanancin talauci ba.

Alhaji Kurfi ya yi nuni da abubuwa da dama da suka taimaka wajen karya farashin kayan abinci. Ya ce dama idan ba a manta ba, farashin kayan abinci a shekarar da ta gabata tabbas ya karye sakamakon;

  • Shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje:

A shekarar da ta gabata, farashin kayan abinci ya karye ne sakamakon shigo da kayan abinci daga waje. Wannan ya rage cunkoso a kasuwanni, kuma ya ba talakawa damar samun kayan abinci cikin sauƙi.

  • Yawan amfanin gona na damina:

Lokacin damina yana kawo yawan hatsi da kayan gona kamar masara da wake, wanda hakan ke sa farashin ya ragu saboda ƙarin kayan abinci a kasuwa.

  • Tsarin sufuri da jigilar kaya:

Kurfi ya bayyana cewa matakan gwamnati wajen tabbatar da sufurin amfanin gona cikin aminci ga motoci masu ɗaukar kayan gona daga ƙauyuka zuwa kasuwanni ya rage kuɗin sufuri, kuma wannan ya taimaka wajen saukar farashin.

Tasirin karyewar farashin

Masanin ya bayyana abin da wannan mataki na sake karya farashin kayan abinci ke nufi ga ƴan Najeriya.

  • Ga talakawa: Karyewar farashin abinci zai kawo haske ga iyalai da dama, zai saka jama'a suna iya siyan abinci cikin sauƙi. "Yanzu da ƴan kuɗinka kaɗan za ka iya siyan kayan abinci da za ka ciyar da iyalanka, wannan abu ne mai daɗi musamman ga talakawa."
  • Ƙalubale ga manoma: Duk da cewa talakawa za su yi farin ciki da wannan mataki, manoma na ci gaba fuskantar matsala. "A bana gaskiya manoma sun sha wahala wajen sayen taki da maganin ƙwari saboda tsadar su. Idan farashin kayan abinci ya karye, amma kayan aikin noma ba su karye ba, to manomi zai yi asara."
  • Ya ce manomi yana noma ne saboda dalilai biyu: don ciyar da iyali da kuma don samun riba ta kasuwanci. Idan ya kashe kuɗi masu yawa amma ya sayar da amfanin gona a farashi mai sauƙi, ba zai iya samun riba ba. Wannan na iya jawo wa manoma gajiya da rage noma, wasu ma su barshi gaba ɗaya. Ga manoma, Kurfi ya ce barazana ce idan gwamnati ba ta dauki matakan tallafawa manoma ba.
  • Ga tattalin arzikin ƙasa: Raguwar farashin kayan abinci na iya rage hauhawar farashin kayayyaki wanda zai taimaka wajen daidaita kasuwar ƙasa. Amma masana sun yi gargadin cewa idan ba a tallafa wa manoma ba, wannan ragin farashi zai iya zama kalubale a dogon lokaci.

Farashin kayan abinci

BBC ta kuma tuntuɓi wasu ƴan kasuwa kan batun farashin kayan abinci a da da yanzu inda wan ɗan kasuwa a Kubwa da ke Abuja, Musa Kabiru ya ce

"A da buhun shinkafa muna sayar da shi ₦85,000 amma yanzu ya dawo ₦60,000. Masara ma daga ₦55,000 ta koma ₦43,000, wake kuma a da kan farashin naira 85,000 yanzu ya koma naira 65,000, kwandan tumatir ya sauka daga ₦22,000 zuwa ₦13,000. Wannan ya kawo ɗan sauƙi ga jama'a,"

Sai dai kuma ya shaida cewa duk da batun karya farashin yana da amfani akwai kuma nasa rashin amfanin.

"Matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na rage farashin kayan abinci abu ne mai kyau. Amma abin da muke fata shi ne kada a bar wannan saukar farashi ya ɗan dade. Gwamnati ta tabbatar an ɗauki matakan da za su sa ya ɗore."

Wata ƴar kasuwar ita ma ta ce "mutane sun fara yin dariya a kasuwa saboda kayan sun ɗan sauka. Amma mu 'yan kasuwa mun san ba kowa yake murna ba, musamman manoma da suka kashe kudi wajen shuka."

Mece ce mafita?

Alhaji Kurfi ya lissafo abubuwan da gwamnati da manoma da masu saye da sayarwa ya kamata su yi domin tabbatar da cewa saukar farashin kayan abinci ya zama mai amfani ga kowa ba tare da cutar da tsarin noma ba:

1. Abin da gwamnati ya kamata ta yi:

  • Tallafa wa kayan aikin noma: Gwamnati ta saukaka farashin taki, maganin ƙwari, da sauran kayan aikin noma domin manoma su iya noma cikin riba.
  • Ƙirƙirar hukuma ta siyan kayan gona: Wacce za ta siya daga manoma a lokacin girbi, ta adana a rumbunan gwamnati, sannan ta fito da su idan farashin kayan abinci ya yi barazanar hauhawa.
  • Inganta sufuri da hanyoyin kasuwanci: Samar da hanyoyi masu kyau da sauƙaƙe jigilar kayan gona domin rage kuɗin sufuri.
  • Tsarin tallafi na dogon lokaci: Kafa tsarin da zai tabbatar da cewa farashin kayan abinci ba zai yi tsanani ga talakawa, amma manoma su ci riba.

2. Abin da manoma ya kamata su yi:

  • Yin noman da ya dace da kasuwa: Sanin buƙatun kasuwa domin kada su noma kayan da ba za su iya sayarwa a riba ba.
  • Kula da kayan aikin noma: Amfani da kayan aikin noma yadda ya kamata domin rage asara.
  • Hada kai da hukuma: Amfani da tsarin siyan kayan gona na gwamnati domin samun tsaro da riba mai kyau.

3. Abin da masu saye da sayarwa ya kamata su yi:

  • Daidaita farashin kaya: Kada su yi ƙoƙari su tursasa farashin kayan abinci ko su yi zamba a kasuwa.
  • Bayar da kayan abinci a kasuwa cikin gaskiya: Tabbatar da cewa abincin da suke sayarwa ya isa ga talakawa a farashi mai sauƙi.
  • Hada kai da gwamnati da manoma: Tallafawa tsarin gwamnati na adana kayan gona da gudanar da kasuwa cikin tsari mai kyau.