Kun san mutanen da ke amfani da AI don yin magana da 'ubangiji'?

Asalin hoton, Prashanti Aswan
A Indiya da wasu sassan duniya mutane sun koma amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira da aka yi wa tsari na musamman domin tafiyar da harkokin addinin su.
Me zai faru idan irin wannan hanya ta zamo mana madogara kan harkokin addini?
Vijay Meel, wani ɗalibi mai shekara 25 da ke zaune a Rajasthan na ƙasar Indiya, ya saba komawa ga Allah a duk lokacin da ya fuskanci ƙalubalen zamani a rayuwarsa.
Yana tuntuɓar malaman addini kan duk wani abu da ya shige masa duhu. Amma a baya-bayan nan ya koma tuntuɓar manhajar GitaGPT.
GitaGPT wata manhaja ce ta ƙirƙirarariyar basira da aka horas da ita kan fahimta da karantu littafin bauta na jama'ar Hindu, Bhagavad Gita.
GitaGPT ya yi kama da littafin da aka saba da shi, amma shi yana iƙirarin cewa da Allah ake magana, idan ana tattaunawa da shi.
"Lokacin da na faɗi jarabawa ta a banki, na shiga matsanancin halin damuwa," in ji Meel.
Amma bayan gano GitaGPT, ya rubuta bayanin manyan abubuwan da ke damun sa, sannan ya buƙaci AI ya ba shi shawara.
"Ka mayar da hankali kan matakin da ka ɗauka kawai, ka daina damuwa da abin da za su janyo,'' in ji GitaGPT.
Irin wannan shawara da Meel ya samu sun ƙarfafa masa gwiwa, kuma sun sa ya ƙara hazaƙa.
Meel ya ce "Ba su ce mini ban sani ba, kuma a wannan lokacin ina buƙatar wanda zai zai ƙarfafa mani gwiwa,''
"Saƙon nan ya taimaka mani wajen yin nazari kan abubuwan da nake tunani da kuma fara shirya masu sosai.''
Daga nan sai GitaGPT ya zame mashi kamar wani aboki, wanda ya ke tattaunawa da shi sau ɗaya ko sau biyu a kowanne mako.
Yadda AI ta shiga harkokinmu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
AI na taka muhimmiyar rawa a rayuwarmu, ya shiga harkokin da suka shafi aikinmu da soyayyarmu da yadda muke alaƙa da juna.
Yanzu kuma masu bauta a sassan duniya na gwada yadda fasahar za ta taimake su.
Amma addinin Hindu wanda ya yi suna wajen girmama abubuwan bautar mabiya, yana ƙara amincewa da shigar da fasahar zamani a harkokin addini.
Yayin da AI ke ƙara taka rawa a harkokin rayuwarmu, Indiya na iya zama madubi kan dogaro da amfani da fasaha wajen warware al'amurran addini.
"Mutane na jin cewa an ware su daga harkokin jama'a, dattijai da wuraren bauta sun nisanta kansu da mutane. A misali, mutane da dama na ganin cewa magana da AI yana bayar da wata dama ta jin cewa kamar kana da laƙar ƙut da ƙut da Allah.'' in ji Holly Walters, wani farfesan addini a kwalejin Wellesley da ke Amurka, wanda ya yi nazari kan harkokin addini a kudancin Asiya.
Walters ya ce amfani da AI a harkokin addini ya zama wajibi kuma an riga an zo gaɓar da dole ne kawai.
"AI ya zama ubangiji kenan?
A cikin shekarun da suka gabata an samu gwaje-gwaje da aka yi da dama a kan gudanar da harkokin addini ta fasahar AI.
A 2023, wata manhajar AI da ake kira 'Text With Jesus' ta janyo cece-kuce saboda an ba ta damar tattauna harkokin addini da AI.
A shekarar ne kuma aka samar da manhajar QuranGPT wadda aka tsara domin amsa tambayoyi da yin bayani kan Al-ƙura'ni, duk da girman ta, rahotanni sun ce ta rushe a cikin kwana ɗaya kacal da ƙaddamar da ita saboda yawan mutanen da ke shiga da neman bayanai.
Ana amfani da fasahar AI a dukkan addinai.
An samu wasu ƙungiyoyi irin su 'The Future Church' wadda tsohon injiniya a kamfanin Google, Anthony Levandowski, ya kafa domin ƙarfafa ɗabi'ar amfani da fasahar AI wajen yaɗa ilimin sanin Allah.
Yanzu haka akwai ƙwararru da dama a fannin fasahar ƙere-ƙere da ke aiki tuƙuru domin samar da manhajojin fasahar AI da za su riƙa bai wa mutane bayanan da suke buƙatar sani a kan addinan su daban-daban.
Vikas Sahu, wani ɗalibi daga Rajasthan, a Indiya, ya ƙirƙiro GitaGPT a matsayin aikin da ya yi cikin sharaɗin kammala karatunsa.
Ana sa ran ya fara aiki ba da jimawa ba, kuma Sahu ya ce kawo yanzu manhajar ta samu mutane dubu ɗari da ke bibiyar sa.
Manhajar ta zamo chatbot da ya mayar da hankali kan littafan addinan Hindu kala daban-daban, inda ake yaɗa manufar addinan kai tsaye.

Asalin hoton, Google
Mafi yawan ƙungiyoyin addini suna maraba da wannan nasara.
A farkon 2025, Sadhguru, wani fitaccen malamin addini a Indiya wanda ya kafa gidauniyar Isha ya ƙaddamar da manhajar AI domin wa'azi da fadakarwa ga mabiya.
An tsara manjahar ne don yaɗa bushara daga rubuce-rubucen da Sadhguru ya rubuta a cikin shekara 35, kuma a cikin sa'oi 15 kacal da ƙadaddamar da manhajar, fiye da mutane miliyan ɗaya suka sauke ta domin amfaninsu.
Ana kuma amfani da AI wajen gudanar da bincike kan fasaha da addinai. A 2022 wani bincike ya yi amfani da AI wajen auna tasirin littafan addinin Hindu.
Ƙwararru sun ce ana iya amfani da AI wajen gano saƙonnin da aka ɓoye a cikin litattafai, waɗanda ba lallai a iya gano su ta hanyar karanta litattafan kawai ba.
Sai dai Holly Walters ya ce akwai fargabar cewa idan aka fara yi masu kallon wasu abubuwan da ke ɗauke da saƙonnin addini, to za a iya bayar da kafar da wasu za su riƙa bai wa irin waɗannan manhaja darajar da ta zarce tasu ta ainuhi.











