Kalli yadda aka janye katafaren gidan cin abinci da ke kan teku
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An janye wani katafaren gidan cin abinci da ke yawo a saman ruwa a Hong Kong.
Gidan cin abincin da gininsa ke kama da irin fada da ake gani a China, an rufe shi ne tun bayan barkewar annobar korona.
Masu wajen sun ce aba su da kudin ci gaba da kula da shi.








