An yanke wa matar shugaban ƙungiyar IS hukuncin kisa

- Marubuci, David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Hukumar kula da harkokin shari'a a Iraqi ta bayyana cewa an yanke wa uwargidar tsohon shugaban IS, marigayi Abu Bakr al-Baghdadi hukuncin kisa.
Kotun da ke zama a birnin Karkh ta samu matar da laifin "yin aiki tare da ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi wajen tsare mata masu bin addinin Yazidi", kamar yadda majalisar ƙoli ta shari'a ta ƙasar ta sanar.
Wani jami'in ma'aikatar cikin gida na ƙasar ya bayyana sunan matar da Asma Mohammed, wadda ake kira Umm Hudaifa.
Lauyoyinta ba su ce komai ba game da batun, amma a wata tattaunawa da BBC, matar ta musanta hannu a cikin ayyukan assha da ake zargin ta da aikatawa, kamar garkuwa da kuma bautar da mata mabiya addinin Yazidi.
Baghdadi ya aure ta ne a lokacin da yake jagorancin ƙungiyar IS wadda ta riƙa tafka ayyukan assha a yankunan Iraqi da Syria, inda ya ƙunshi mutum kimanin miliyan takwas.
A shekarar 2019, watanni kaɗan bayan sojoji sun yi galaba kan ƙungiyar a yankin, sojojin Amurka sun kai samame a wurin da Baghdadi da wasu iyalansa ke ɓuya a arewa maso yammacin Syria.
Baghdadi ya tarwatsa rigar bama-baman da ke jikinsa a lokacin da aka rutsa shi a wani rami, abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa da kuma biyu daga cikin ƴaƴansa, yayin da aka kashe biyu daga cikin matansa huɗu a lokacin musayar wuta.
Umm Hudaifa ba ta wurin a lokacin, kasancewar ta koma tana rayuwa a kudancin Turkiyya a 2018, inda ta riƙa amfani da wani suna na daban.
A cikin watan Fabarairun wannan shekara ne aka mayar da ita Iraqi inda hukumomi suka tsare ta, kuma aka ci gaba da bincike kan alaƙar ta da ayyukan ta'addanci da na laifukan yaƙi.
Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce suna da ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa ƙungiyar IS ta tafka kisan kiyashi da manyan laifuka a kan matan addinin Yazidi, waɗanda ƙungiyar ta ba su wa'adin su sauya addinin ko a kashe su.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dubban mabiya addinin Yazidi ne aka kashe sannan aka bautar da wasu dubbai, inda aka riƙa ƙwace yara da mata daga hannun iyalansu tare da azabtar da su, lamarin da ya haɗa da fyaɗe da cin zarafin lalata.
Haka nan masu binciken na Majalisar Dinkin Duniya sun ce IS ta tafka laifukan yaƙi, ciki har da kisa da azbtarwa a lokacin da ta yi wa fafaren hula kimanin 1,700 kisan kiyashi, waɗanda akasarinsu Musulmai ne ƴan shi'a a shekarar 2014.
Lokacin da BBC ta tambayi Umm Hudaifa game da waɗannan laifuka, ta ce ta ƙalubalanci mijin nata game da "jinanen al'umma" da ke a hannunsa.
Ta kuma ce "tana jin takaici" kuma tana "nadamar" abubuwan da suka faru ga mata da yara mabiya Yazidi, musamman wadanda aka kai su gidanta a matsayin bayi.
Wasu mabiya addinin Yazidi wadanda mayaƙan IS suka yi garkuwa da kuma yi masu fyaɗe sun shigar da ƙara a wata kotu da ke Iraqi, suna zargin Umm Hudaifa da haɗa baki wajen garkuwa da su da cin zarafin mata yara da manya. Ta musanta zargin.
A cikin shekarun nan kotunan Iraqi sun yanke hukunce-hukuncen kisa da ɗaurin rai da rai ga maza da mata waɗanda aka kama da laifin "kasancewa ƴan ƙunyoyin ta'addanci".











