Barca ta fara La Liga da nasara karkashin sabon koci Flick

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona karkashin sabon koci, Hansi Flick ta fara La Liga ta bana da nasara, bayan da ta je ta ci Valencia 2-1 ranar Asabar.
Flick tsohon kociyan tawagar Jamus da Bayern Munich ya koma Barcelona ne, bayan da ta sallami Xavi.
Valencia ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Hugu Duro, bayan tamaula da ya samu ta wajen Diego Lopez ya buga ta wuce Marc-Andre ter Stegen.
Daga baya ne aka yi bani-in -baka tsakanin Robert Lewandowski da Lamine Yamal da ta kai Lewandowski ya farke ƙwallon.
Valencia ta sa kaimi da yawa, amma Barcelona ta nuna cewar da gaske take a bana, inda ta yi ta sa ƙwazo a karawar.
Daga baya ne Lewandowski ya kara na biyu a bugun fenariti, bayan da aka yi wa Raphinha ƙeta.
Yamal ya gagari Valencia, inda mai shekara 17 ya dunga warwasa tamaula son ransa da ya dunga zama baraza na ga masu masauƙin baki.
Haka dai Barcelona ta ci gaba da wasan har zuwa karshensa, inda ta tsira da maki uku da ƙwallo biyu a raga aka zura mata ɗaya a wasan farko a La Liga ta 2024/25.
Barcelona, wadda ta yi ta biyu da tazarar maki 10 tsakaninta da Real Madrid, wadda ta lashe kofn bara za ta fuskanci Athletic Bilbao a wasan mako na biyu ranar Asabar 24 ga watan Agusta.











