Ana gagarumin gangamin adawa da yaƙin Gaza a shafukan intanet

Wani hoto da ƙirƙirarriyar basira (AI) ta ƙirƙira - da ke nuna wasu ɗaruruwan tantuna a sansanin ƴan gudun hijirar Falasɗinawa tare da wani rubutu da ke cewa "All Eyes on Rafah" (Ido na kan Rafah) - na ta karakaina a shafukan sada zumunta.

Sashen Larabci na BBC ya bi diddigin hoton da aka ƙirƙirara a Malaysia, wanda kuma masu amfani da shafin Instagram fiye da miliyan 44 suka wallafa, ciki har da fitattun mutune a Indiya da Pakistan da kuma Puerto Rico.

Hoton tare da kuma taken sun yaɗu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta, bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da wani hari da ya yi sanadiyyar ƙona wani sansanin ƴan gudun hijirar Falasɗinawa a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce aƙalla mutum 45 ne suka mutu a lamarin, yayin da ake yi wa ɗaruruwa magani sakamakon raunukan ƙuna da na karaya da suka samu.

Shugabannin ƙasashe, da gwamnatoci da ƙungiyoyin duniya sun yi Allah wadai tare da nuna damuwarsu kan lamarin.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana lamarin da ''babban kukure'', yana mai tabbatar da cewa an ƙaddamar da bincike kan batun.

Mai magana da yawun majalisar tsaron Amurka, John Kirby ya bayyana lamarin da ''mai tayar da hankali''. Amma ya bayyana cewa ''babu wani sauyi da hakan zai kawo''.

Bayan harin ya faɗa kan tantuna a Rafah, sai hoton ya bazu a shafukan sada zumunta, bayan da wani matashi ya wallafa shi a shafinsa na sada zumunta, kamar yadda sashen Larabci na BBC ya gano.

Ta ya aka ƙirkiri hoton?

Daga ina taken 'ido na kan Rafah' ya soma?

A lokacin da Isra'ila ta kai hari kan wani tanki a kusa da Rafah ne, Richard Pepperkorn, wani wakilin Ƙungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) a yankunan Falasɗinawa da aka mamaye, ya wallafa saƙo ɗauke da rubutun a shafinsa.

A watan Fabrairu ya shaida wa manema labaraia cewa ''Ido na kan Rafah''. A lokacin yana gargaɗi kan sojojin Isra'ila na kai hari birnin.

Pepperkorn na magana ne da manema labarai ta intanet a shalkwatar MDD da ke birnin Geneva.

Ya ce yana fargabar afkuwar "mummunan bala'i" idan sojojin Isra'ila suka ƙaddamar da mummunan hari zuwa birnin.

Daga lokacin ne kuma jami'ai da ƴan gwagwarmaya suka yi ta maimaita kalmomin Pepperkorn, domin nuna damuwarsu da adawa da hare-haren Isra'ila a Rafah.

Bayan ƴan watanni, taken ''Ido na kan Rafah” ya ci gaba da bayyana a lokutan zanga-zanga a faɗin duniya da kuma a shafukan sada zumunta.

Clare Sands, wani fitaccen mawaƙi a ƙasar Ireland ya yi amfani da taken a lokacin wallafa wata waƙarsa a shafin sada zumunta, yana mai kira ga ƴan siyasa su taimaka a dakatar da hare-hare a birnin.

Ta ya hoton ya yaɗu a shafukan sada zumunta cikin kwana biyu da suka gabata?

Masu zanga-zanga a birane da dama sun yi gangami domin nuna goyon baya, inda suka riƙa amfani da kalmomin tare da riƙe kwalaye masu ɗauke da rubutun.

An yi amfani da kalmomin da suka yi fice a watan Fabrairu a lokacin wallafa hoton asalin a Malaysia.

Su ma fitattun mutanen da suka wallafa hoton sun yi amfani da taken, ciki har da mawaƙin Pop, Ricky Martin, da tauraruwar fina-finan Turkiyya, Tuba Buyukustun, da ta fina-finan Indiya Priyanka Chopra, da kuma Kinda Alloush ta fina-finan Syria.

Maher Nammari, wani masanin hanyoyin samun kuɗi a intanet, kuma mashawarci kan ƙirƙirarriyar basira, ya faɗa wa BBC cewa abin da ya sa ya yarda AI ne ya ƙiƙiri hoton, shi ne babu alamomin da ke nuna cewa ɗaukar hoton aka yi.

Hoton bai nuna asalin wuri ko birnin da aka ɗauke shi a Rafah ba.

Ya nuna wani daji a sahara, tare da tantuna, sai kuma rubutun ''Ido na kan Rafah'' a kan hoton.

A lokacin da Nammari zai wallafa hoton a shafin Instagram ya rubuta "Ƙara naka" domin hoton ya samu yaɗuwa.

Yana buƙatar latsawa biyu ga masu amfani da shafin, lamarin da ya sa miliyoyin mutane suka samu damar amfani da shafin.

Amma Nammari yanayin yadda abin ya faru da kuma yadda ya samu karɓuwa a shafukan sada zumunta ya taimaka wajen yaɗa hoton.

Ya kwatanta shi da wasu gangami da a ka taba yi a baya kan wasu abubuwa wanda bai samu yaɗuwa ba kamar wannan.

Namara ya ce wani ƙarin dalilin da ya sa hoton ya samu yaɗuwa shi ne ba ya ɗauke da wani abin tayar da hankali kamar jini ko harbin bindiga ko nuna mutane ko suna ko wurin da aka kai wa hari, wanda dokokin Instagram za su iya hana yaɗa shi.

Gangamin da suka gabata?

Wannan gangamin shi ne irinsa na farko da ke yaɗa saƙon goyon baya da ya samu karɓuwa a shafukan sada zumunta.

A baya an samu gangami, mai ɗauke da taken "Rayukan Baƙaƙen Fata na da Muhimmanci," an yi amfani da wannan domin yaƙi da wariyar launin fata, da wariya da rashin daidaito da aka nuna wa baƙaƙen fata a shekarun 2020 da 2021.

Gangamin ya samu karɓuwa a Amurka bayan 'yan sanda sun kashe wasu manyan mutane, an kuma yi amfani da kalaman a Birtaniya da wasu wuraren.

A ƙasar Sudan ma, masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi gangami bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF, lamarin da ya yi sanadin kisan ɗaruruwan mutane tare da raba dubbai da muhallansu.

Ɗaya daga cikin fitatun gangamin da ka a yi a shafukan sada zumunta a ƙasar shi ne wanda aka yi amfani da “Blue for Sudan”.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta sauya hotunansu da ke shafukansu zuwa launin shuɗi domin nuna goyon bayansu ga masu zanga-zanga a birnin Khartoum.

Daga baya aka riƙa amfani da taken wajen gangamin siyasa da na tattalin arziki.

A shekarar 2023, fitattun mutane a faɗin duniya suka riƙa wallafa saƙonnin nuna goyon baya ga mutanen da girgizar ƙasa ta shafa a birnin Marrakesh na ƙasar Moroco da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Sun yi ta wallafa hotuna a shafin Instagram domin nuna jaje, da karɓar tallafi tare da nuna goyon baya da iyalan mutanen da lamarin ya rutsa da su.