Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin an fara samun nasarar kakkaɓe ƴan bindiga a Najeriya?
A Najeriya, rahotanni sun ce an fara kakkabe wasu daga cikin gaggan 'yan bindiga a wuraren da suke yawan kai hare-hare a jihohin Zamfara da Katsina da Sakkwato da kuma Neja.
Wani dan jarida mai binciken kwakwaf kan harkokin tsaro, Mannir Sani Fura-Girke, ya ce akwai kwararan alamu da ke nuna ana samun nasara a yakin da ake yi da 'yan bindigan.
"Gaskiya halin da ake ciki musamman kwana17 da suka wuce , tun da aka fara matsalar rashin tsaro ba a taɓa samun irin wannan nasarar ba, saboda yadda ake fatattakar ɓarayin dajin, ba a jira sai sun kawo hari, binsu ake har dabobin su ana yaƙarsu," a cewarsa.
Malam Mannir ya shaida wa BBC cewa an samu nasarar rage ƙarfin shugabannin ƴan bindigar :
"Shugaban wadannan ƴan bindiga, Kachalla Ali wanda kusan babu kamarsa a wajen satar mutane da garkuwa da su ko kuma satar dabbobi, saboda yana da yara sama da 2,700, kuma shi ne yake iko da jihohin Zamfara da Kaduna da Neja da Kebbi da wani yanki na Nasarawa, kuma ya yi ƙarfin da yake da alaƙa da ƴan Boko Haram, amman sai ga shi an gama da shi da tawagarsa."
"Sannan an gama da wasu Kachallolin, irin su Kachalla Jafaru, wanda dabarsa ke nan kusa da dajin Mun-haye a Karamar hukumar Tsafe, sai kuma Begu wanda shi ma ya addabi yankin Karamar Hukumar Dan-musa da ke jihar Katsina da wani yanki na Kankara da ma wani yanki na jihar Zamfara da sauran Kachalloli da dama waɗanda duk an halakasu," in ji Mannir Fura-Girke.
Munnir Sani Fura-Girke ya ce akwai hanyoyin da ake gano cewa an hallaka waɗannan ƴan bindiga;
"kusan duk inda suke kusa da ƙauyuka ne kuma suna mu'amala da mutane saboda haka duk wanda aka kashe su da kansu suke faɗi, kuma waɗanda aka yi garkuwa da su idan sun dawo suna bada labari, sannan jami'an tsaro suna ɗaukar hotuna daga nan ake gane waɗanda aka kashe."
Mallam Munnir ya ce ƴan bindigar na tserewa daga dabobinsu musamman saboda yadda mutanen wasu jihohin suka ɗauki matakin kare kansu da kuma yadda jami'an tsaro ke ɓarin wuta kan ƴan bindigar, "saboda haka suna komawa jihohin Taraba da Adamawa saboda abin ya yi masu tsauri da yawa, kusan babu inda za su fita da mashin goma ba a kai masu hari ba, shi ya sa ba su sanya fitilar mashinansu domin tsoron kada a kawo masu hari."
Ɗan jaridar ya bada shawarar cewa ya kamata sauran jihohin da ƴan bindigar ke tserewa su ɗauki matakin kare kansu.